Gaskiya nake nema 'Yan uwana Musulmi, Shin Wai Gaskiya ne Abubakar ne Khalifan Annabi (s) ???



 HADISAN WASIYYAR KHALIFANCIN ABUBAKAR DAGA ANNABI (S. A. W. W) CIKIN LITTATTAFAI  !!!


@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


ANNABI (S. A.W.W) BAI HALIFANTAR DA KOWA BA IN JI UMAR BN KHADDAB 


Wato duk wani ma'abocin karatu da neman inda gaskiya take don ya bi ta zai riqa cin karo da maganganu masu cin karo da juna rubuce cikin littafan da aka inganta su, wanda hakan ke sa mutum cikin rudewa ya ma rasa gaskiyar magana cikin addinin gaskiya wanda ya kamata a sami maganar gaskiya cikinsa. 


Wannan kuwa na da alaqa ne da qoqarin da magabata suka riqa yi don boye gaskiya da kuma hassada ga wasu wadanda ba sa sonsu, tare da qoqarin daukaka qasqantattu. 


Maganar gaskiya ita ce Annabi (S. A. W. W) yayi wasiyya kan wanda zai jagoranci al'umarsa ya tafiyar dasu kan haqiqanin abinda ya barsu akai, amma saboda ba wanda mafi yawan mutane suke so bane sai aka qirqiro wasu hadisan qarya masu nuna wasu ne na dabam akayi wasicci dasu. Saboda haka sai suka sami matsala ta rashin sanin yadda za su iya kare wadannan qarerayi nasu.


SHIN WAI GASKIYA NE ABUBAKAR NE KHALIFAN ANNABI ? 


Ga riwayoyi nan masu muni game da haka;


👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇


(10)- وحدثني الحسن بن علي الحلواني حدثنا جعفر بن عون عن أبي عميس ح وحدثنا عبد بن حميد واللفظ له أخبرنا جعفر بن عون أخبرنا أبو عميس عن بن أبي مليكة سمعت عائشة وسئلت من كان رسول الله صلى الله عليه وسلم مستخلفا لو استخلفه قالت أبو بكر فقل لها ثم من بعد أبي بكر قالت عمر ثم قيل لها من بعد عمر قالت أبو عبيدة بن الجراح ثم انتهت إلى هذا 


Kuma Hassan Bn Aliyu Al-Halwaaniy ya bani labari, Ja'afar Bn Auni ya bamu labari daga baban Umais, kuma Abdu Bn Humaid ya bamu labari da lafazinsa, Ja'afar Bn Auni ya bamu labari, baban Umais ya bamu labari daga Ibn Abiy Mulaikata cewa,


 " Na ji an tambayi A'ishatu cewa wanene Manzon Allah (S. A. W. W) ya Halifantar wanda zai gaje shi  ? Tace, " ABUBAKAR. "


Sai aka ce mata, " Wanene kuma a bayan Abubakar  ?" Tace, " UMAR. "


Aka ce mata, " Wanene kuma bayan Umar  ?" Tace,  " ABU UBAIDATA BN JARRAAHA. " Shine yazo zuwa nan. 


(13)- حدثنا عبيد الله بن سعيد حدثنا يزيد بن هارون أخبرنا إبراهيم بن سعد حدثنا صالح بن كيسان عن الزهري عن عروة عن عائشة قالت قال لي رسول الله صلى الله عليه وسلم في مرضه ادعي لي أبا بكر وأخاك حتى اكتب كتابا فإني أخاف أن يتمنى متمن ويقول قائل أنا أولى ويأبى الله والمؤمنون إلا أبا بكر


Ubaidullahi Bn Sa'ad ya bamu labari, Yazeed Bn Haroun ya bamu labari, Ibrahim Ibn Sa'ad ya bamu labari, Salihu Bn Kaisaan ya bamu labari daga Zuhriy, daga Urwata, daga A'ishatu tace; " Manzon Allah (S. A. W. W) ya fada min cikin halin jinyarsa; 


" KI KIRAWO MIN ABUBAKAR DA 'DAN'UWANKI HAR NA RUBUTA WANI RUBUTU (wasiyyah), DOMIN NI INA JIN TSORO KADA WANI MAI BURI YAYI BURIN (wannan matsayi na Halifanci), KUMA MAI MAGANA YAYI MAGANA CEWA NI NAFI CANCANTA (da wannan matsayi). ALLAH DA MUMINAI SUN QI SAI ABUBAKAR. "


(SAHIHUL-MISLIM, KITABUL FADHA'IL) 


Sannan kuma an kawo wani hadisi cikin Tirmidhi cewa; 


4023» حدثنا الحسن بن الصباح البزار حدثنا سفيان بن عيينة عن زائدة عن عبد الملك بن عمير عن ربعي هو ابن حراش عن حذيفة قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: ((اقتدوا باللذين من بعدي أبي بكر وعمر)).


Hassan Bn Sabaahi Al-Bazariy ya bamu labari, Sufyan Bn Uyainata ya bamu labari daga Za'idata daga Abdulmalik Bn Umair, daga Rab'eey, shine Ibn Haraashi, daga Huzaifata yace; Manzon Allah (S. A. W. W) yace; 


" KUYI KOYI DA WADANNAN MUTANE BIYU A BAYANA, ABUBAKAR DA UMAR  ."


(SUNAN TIRMIDHI, KITABUL FADHA'IL, HADISI MAI LAMBA 4025)



A taqaice dai wadannan sune manyan hujjoji kan wasiyyar Halifantar da Abubakar da Umar akan kowa bayan Annabi (S. A. W. W) .


ANNABI BAI HALIFANTAR DA KOWA BA INJI UMAR BN KHADDAB 

----------------------------------------------------------


BARI MU NAZARCI WADANNAN HADISAI UKU 


👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇


«4050» حدثنا سلمة بن شبيب حدثنا المقرئ عن حيوة بن شريح عن بكر بن عمرو عن مشرح بن هاعان عن عقبة بن عامر قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: ((لو كان بعدي نبي لكان عمر بن الخطاب)). قال: هذا حديث حسن غريب 


Salmanu Bn Shabeeb ya bamu labari, Maqarriyyu ya bamu labari daga Hayauta Bn Shuraih, daga Bukar Bn Amruu, daga Mashruh Bn Haa'aani, daga Uqbatu Bn Ameer yace : Manzon Allah (S. A. W. W) yace; 


" DA ACE AKWAI WANI ANNABI A BAYANA DA UMAR BN KHADDAB NE ."


Yace, wannan hadisi mai kyau ne. 


(SUNAN TIRMIDHI, KITABUL FADHA'IL, BABUN FADHA'ILU UMAR, HADISI MAI LAMBA  4050)


Kunga abinda wannan hadisi ke karantarwa shine, in da ace akwai wani da za a aiko a bayan Annabi (S. A. W. W) to, da Umar ne saboda girman matsayinsa da fifikonsa. Amma da shike babu wani Annabin shike nan. Wannan kuwa na nuna mana ne cewa ashe Umar ya fi Abubakar. Saboda haka in ma akwai wani wanda zai gaji Annabi (S. A. W. W) shine Umar a wannan riwaya.


Wannan kuwa yana qaryata Matsayin da ake cewa ne Abubakar ya fi kowa a bayan Annabi (S. A. W. W). 


Yanzu dan Allah a wajen masu hankali da tunani in dai har Annabi ya fadi wannan magana za a sami wani wanda zai gaje shi in ba Umar ba tun da akwai wani Annabi wanda za a aiko da shi ne ? 


Umar ya qara da cewa; 



323- حَدَّثَنَا حَدَّثَنَا عَبْدُ الرَّزَّاقِ ، حَدَّثَنَا مَعْمَرٌ ، عَنِ الزُّهْرِيِّ ، عَنْ سَالِمٍ ، عَنِ ابْنِ عُمَرَ : أَنَّهُ قَالَ لِعُمَرَ : إِنِّي سَمِعْتُ النَّاسَ يَقُولُونَ مَقَالَةً ، فَآلَيْتُ أَنْ أَقُولَهَا لَك ، زَعَمُوا أَنَّكَ غَيْرُ مُسْتَخْلِفٍ ، فَوَضَعَ رَأْسَهُ سَاعَةً ، ثُمَّ رَفَعَهُ ، فَقَالَ : " إِنَّ اللَّهَ عَزَّ وَجَلَّ يَحْفَظُ دِينَهُ ، وَإِنِّي إِنْ لَا أَسْتَخْلِفْ ، فَإِنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ لَمْ يَسْتَخْلِفْ ، وَإِنْ أَسْتَخْلِفْ ، فَإِنَّ أَبَا بَكْرٍ قَدْ اسْتَخْلَفَ " ، قَالَ : فَوَاللَّهِ ، مَا هُوَ إِلَّا أَنْ ذَكَرَ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ وَأَبَا بَكْرٍ ، فَعَلِمْتُ أَنَّهُ لَمْ يَكُنْ يَعْدِلُ بِرَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَحَدًا ، وَأَنَّهُ غَيْرُ مُسْتَخْلِفٍ .


Abdurrazaq ya bamu labari, Ma'amar ya bamu labari daga Zuhriy, daga Saleem, daga Ibn Umar, cewa ya cewa Umar (babansa) : 


" Ni fa naji mutane ne suna fadin wata irin magana, shine nayi nufin na fada maka. Suna riyawa cewa wai kai baka Halifantar da kowa ba. "


Sai (Umar) ya sanya kansa qasa na tsahon lokaci (yana nazari ba tare da sanin amsar da zai bashi ba), sa'an nan ya dago shi yace; 


" AI LALLE ALLAH MAI GIRMA DA 'DAUKAKA ZAI TSARE ADDININSA (ba sai an Halifatar da wani ba). TO, IDAN MA BAN HALIFANTAR DA WANI (wanda zai gaje ni ba), AI MANZON ALLAH (S. A. W. W) MA BAI HALIFANTAR (da kowa ba). IDAN KUMA NA HALIFANTAR (da wanda zai gane ni) AI ABUBAKAR MA YA HALIFANTAR (dani). "


Yace; " NA RANTSE DA ALLAH WANNAN (maganar daka ambata min) BA KOMAI TA TUNA MIN BA FACE MANZON ALLAH (S. A. W. W) DA ABUBAKAR, SAI NASAN CEWA SHI BABU WANI KAMAR MANZON ALLAH (S. A. W. W) A ADALCI, (domin shi) BAI HALIFANTAR BA, (Abubakar kuma ya Halifantar dani don bin son zuciyarsa). "


(MUSNAD AHMAD, MUSNAD KHULAFA'AR-RASHIDEEN, MUSNAD UMAR BN KHADDAB, HADISI MAI LAMBA 323).


Kunga wannan magana ta Umar ta rushe dukkan hadisan qarya da kuka kawo cewa wai Annabi (S. A. W. W) yayi wasicci da Abubakar, kuma cikin Wasiccin ma har da shi Umar din. 


Sannan kuma akwai wani hadisi cikin Bukhari kamar haka; 


(2741)- حدثنا عمرو بن زرارة: أخبرنا إسماعيل، عن عون، عن إبراهيم، عن الأسود قال: 

ذكروا عند عائشة: أن عليا - رضي الله عنهما - كان وصيا، فقالت: متى أوصى إليه، وقد كنت مسندته إلى صدري، أو قالت: حجري، فدعا بالطست، فلقد انخنث في حجري، فما شعرت أنه قد مات، فمتى أوصى إليه؟ 


Amru Bn Zurarata ya bamu labari, Ismael ya bamu labari daga Auni, daga Ibrahim, daga Aswaad yace; An ambata a wajen A'ishatu cewa, Aliyu (R. A) shine wasiyyi? " Sai tace; 


" YAUSHE YAYI WASIYYA ZUWA GARE SHI  ! ALHALI NI NA JINGINAR DA KANSA (Manzon Allah) AKAN QIRJINA. Ko kuma tace; " CIKIN 'DAKINA. ......BAN GUSHE BA TARE DASHI HAR YA MUTU. TO, DA YAUSHE YAYI MASA WASICCI  ?


(SAHIHUL-BUKHARI, KITABUL-WASAAYAH, BABUN WASIYYATUR-RAJULI MAKTUBATUN INDAHU, HADISI MAI LAMBA 2741)


Wannan hadisi da aka jingina shi ga Ummul-muminina A'isha qarya ne, domin kuwa jinyar da Annabi (S. A. W. W) yayi har ya umarci Sahabbansa da cewa su kawo masa abin rubutu ya rubuta musu abinda in sunyi riqo dashi a bayansa ba za su bata ba, duk maza ne tare dashi (S. A. W. W) amma aka ce wai ita take cewa wai akan jirjinta ya rasu. Idan kuma ita ta fada da bakinta sai muce, ko kuma tana nufin ita tana cikin mazan kenan da suke zaune dashi? Ko kuma tana qoqari ne ta kare wadancan maganganu da tayi cewa wai Annabi (S. A. W. W) ya fada mata cewa babanta ne wanda zai gaje shi. 


To, bamu san dai mai gaskiya cikin Ummul-muminina A'isha da Umar ba, domin sun kawo maganganu masu cin karo da juna. 


KU QARA QIRQIRO WATA QARYAR MUNA NAN DAKU  !


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.


       (08137925034)


23rd May, 2021/  12th Shawwal, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post