Falsafar Gwagwarmaya: Halin Da Yan Uwa Suka Tsinci Kansu Na Rashin Jagora A Cikinmu


Daga Wakilinmu Sadar Yusuf Kano

Ni ina ganin wannan bakar fitina da ta taso, ba wani abu bane ya bata damar baje koli illah rashin jagoran gaskiya Allamah Sayyidi Ibraheem Zakzaky (H) a cikin 'yan uwa.

Amma banda hakan abin da mamaki, yaya Dan Gwagwarmaya Almajirin malam Zakzaky (H) zai yadda har ya saurari wani batu daga mugunyar akidar 'yan shiraziyya?!!!

Ana ta fama, wani dan uwa yace mini ai wai suna cewa rigimar maraji'ai ce, nace tom dama da yake bai san maraji'an ba kuma lallai wannan zagin maraji'ai ne domin maraji'ai gabadaya basu da sabani kan munin akidar shirazanci!!!

Idan wani ya karbo kudi, ya karbo kwangila yazo yana kokarin yada akidar da gwamma wahabiyanci da ita bai kamata mukhlisin dan uwa ya rufta tarkon shaidan ba.

Duk shakiyancin 'yan kwamashiyal amma neman tsari suke da shirazawa domin shi shirazaci asalin tushen sa ne rubabbe kuma kayan shedan da shedanu.

Ni ban san wani almajirin Malam Zakzaky (H) da yake goyon bayan shirazawa ba, wannan mauqifin ba mujamala domin jan layin mu ne.

Bissalam.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post