@ MA'ASUMAH NIGERIAN NIGERIAN NEWS UPDATED @
SHEKARU BAKWAI (7) NAYI INA SALLAH KAFIN WANI
Yana daga cikin makircin da aka tsara don rushe da'awar Manzon Allah (S. A. W. W) ya zamana cewa komai an canza shi daga muhallinsa. Za ka iya cin karo da irin wadannan cikin karatuttukan kowacce makara na musulmi.
'Daya daga cikinsu shine don qoqarin bishe hasken Imam Ali (A. S) da kuma qoqarin fifita wani aka qirqiro sunan Bogi ana kiran wani dashi wai shine SIDDIQU !
Amma dai duk da irin wannan qarerayi ba a rasa malamai kawo maganganun gaskiya cikin littafansu ba. Wannan kuwa na da alaqa ne da alqawarin Allah na cewa sai ya cika haskenSa.
Ku biyo mu cikin wadannan riwayoyi insha Allah.
👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇
121- حدثنا علي بن محمد حدثنا أبو الحسين أخبرني حماد بن سلمة عن علي بن زيد بن جدعان عن عدي بن ثابت عن البراء بن عازب قال أقبلنا مع رسول الله صلى الله عليه وسلم في حجته التي حج فنزل في الطريق فأمر الصلاة جامعة فأخذ بيد علي فقال: ((ألست أولى بالمؤمنين من أنفسهم)). قالوا بلى. قال: ((ألست أولى بكل مؤمن من نفسه)). قالوا بلى. قال: ((فهذا ولي من أنا مولاه اللهم وال من والاه اللهم عاد من عاداه)).
Aliyu Bn Muhammad ya bamu labari, baban Hussaini ya bani labari, Hammad Bn Salamata ya bamu labari daga Aliyu Bn Zaid Bn Jada'aan, daga Adeey Bn Thabeet, daga Bara'a Bn Azeeb yace,
" Mun juyo tare da Manzon Allah (S. A. W. W) daga Hajjinsa wanda yayi, sai muka sauka a hanya, yayi umarni da yin sallah a hade, sai ya riqe hannun Aliyu yace, " ASHE BA NINE MAFI CANCANTA AKAN MUMINAI FIYE DA KANSU BA ? Suka ce, "Na'am ! Sai ya qara cewa, " ASHE BA NINE MAFI CANCANTA AKAN KOWANNE MUMINI FIYE DA KANSA BA ?" Suka ce, " Na'am. "
Yace, " TO, WANNAN SHINE MAJIBINCIN WANDA NA KASANCE MAJIBINSA. YAA ALLAH KA JIBINCI WANDA YA JIBINCE SHI, YAA ALLAH KA KAYI ADAWA DA DUK WANDA YAYI ADAWA DASHI. "
Imam Ali (A. S) shine Siddiqin gaskiya wanda ya cancanci komai na Manzon Allah (S. A. W. W) kamar yadda yazo cikin hadisin dake biye.
125- حدثنا محمد بن إسماعيل الرازي حدثنا عبيد الله بن موسى أنبأنا العلاء بن صالح عن المنهال عن عباد بن عبد الله قال: قال علي أنا عبد الله وأخو رسوله صلى الله عليه وسلم وأنا الصديق الأكبر لا يقولها بعدي إلا كذاب صليت قبل الناس بسبع سنين.
Muhammad Bn Isma'il Al-Raziy bamu labari, Ubaidullahi Bn Musa ya bamu labari, Ala'a Bn Salih ya bamu labari daga Minhaal, daga Ubadah Bn Abdullahi yace, Aliyu yace;
" NI BAWAN ALLAH NE KUMA 'DAN'UWAN MANZON ALLAH (S. A. W. W), KUMA NINE SIDDIQU MAFI GIRMA. BABU WANDA YA ISA FADAR WANNAN KALMA A BAYANA FACE MAQARYACI ! SANNAN KUMA NAYI SALLAH TSAHON SHEKARA BAKWAI KAFIN MUTANE (koma bayan Annabi da Khadijah). "
Abinda yasa Imam (A. S) yace shine Siddiqu mafi girma saboda kowanne Annabi na da nasa Siddiqin ne, kuma Siddiqi Manzon Allah (S. A. W. W) shine mafi girma cikin Siddiqan Annabawa (A. S).
Amma duk da wannan matsayi nasa bai hana Mu'awiyyah (L. A) ya zage shi ba.
126- حدثنا علي بن محمد حدثنا أبو معاوية حدثنا موسى بن مسلم عن ابن سابط- وهو عبد الرحمن- عن سعد بن أبي وقاص قال قدم معاوية في بعض حجاته فدخل عليه سعد فذكروا عليا فنال منه فغضب سعد وقال تقول هذا لرجل سمعت رسول الله صلى الله عليه وسلم يقول: ((من كنت مولاه فعلي مولاه)). وسمعته يقول: ((أنت مني بمنزلة هارون من موسى إلا أنه لا نبي بعدي)). وسمعته يقول: ((لأعطين الراية اليوم ر�
Muhammad Bn Aliyu ya bamu labari, baban Mu'awiyata ya bamu labari, Musa Bn Muslim ya bamu labari daga Ibn Saabid (shine Abdurrahman), daga Sa'ad Bn Abiy Waqqas yace, " Mu'awiyyah ya zo cikin sashen Hajjinsa, sai Sa'ad ya shiga gare shi suka yi ta ambaton Aliyu (da munanan maganganu) har Sa'ad ya fusata yace, " Yanzu za ku riqa fadin irin wadannan maganganu ga mutumin da naji Manzon Allah (S. A. W. W) na cewa a kansa;
" DUK WANDA NA KASANCE SHUGABANSA ALIYU SHUGABANSA NE. "
Kuma na ji shi yana cewa;
" KAI MATSAYINKA A WAJENA KAMAR MATSAYIN HARUNA NE WAJEN MUSA, SAI DAI KAWAI BABU ANNABI NE A BAYANA ."
Sannan na qara jinsa (S. A. W. W) na cewa;
" YAU ZAN BADA TUTA GA WANI WANDA ALLAH DA MANZONSA KE SONSA , KUMA SHI MA YANA SON ALLAH DA MANZONSA. "
(IBN MAJAH, KITABUN-FADHA'IL, BABUN MANAQIBUL-ALIYU )
Mun kawo wannan hujjoji ne a matsayin ishara ga masu hankali da tunani.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.
(08137925034)
11th May, 2021/ 29th Ramadan, 1442.