@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
DA SANNU ZA KU BI SUNNAR WADANDA SUKA GABACE KU IN JI ANNABI (S. A. W. W)
Duk wata magana wacce Annabi (S. A. W. W) ya fade ta sai ta tabbata, sai dai kawai idan lokacin bai yi ba.
Al'ummar Manzon Allah (S. A. W. W) siffantu da al'ummata Annabi Musa (A. S) ta fuskacin aiki. Saboda hakane ma irin abinda al'ummata Annabi Musa (A. S) ta aikata irinta ne al'ummata Manzon Allah (S. A. W. W).
Ku dauki misali da irin tambaye-tambayesu da kuma ayyukansu na riqe wani abu na dabam a matsayin abin bauta ko koyi ba wanda Annabin nasu ya bar musu ba.
Ku biyo mu cikin wannan hadisi na qasa kuji daga bakin Ma'aiki (S. A. W. W).
👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇
ما جاء لتركبن سنن من كان قبلك
حدثنا سعيد بن عبد الرحمن المخزومي حدثنا سفيان عن الزهري عن سنان بن أبي سنان عن أبي واقد الليثي أن رسول الله صلى الله عليه وسلم لما خرج إلى خيبر مر بشجرة للمشركين يقال لها ذات أنواط يعلقون عليها أسلحتهم فقالوا يا رسول الله اجعل لنا ذات أنواط كما لهم ذات أنواط فقال النبي صلى الله عليه وسلم سبحان الله هذا كما قال قوم موسى أجعل لنا إلها كما لهم آلهة والذي نفسي بيده لتركبن سنة من كان قبلكم قال أبو عيسى هذا حديث حسن صحيح وأبو واقد الليثي اسمه الحارث بن عوف وفي الباب عن أبي سعيد وأبي هريرة
Sa'eed Bn Abdurrahman Al-Makzumiy ya bamu labari, Safyanu ya bamu labari daga Zuhriy, daga Sinaan Bn Abiy Sinaan, daga baban Waqidi Al-Laiseey, lalle Manzon Allah (S. A. W. W) yayin da ya fito zuwa Khaibar ya shude/wuce ta kan wata Bishiyar Mushirikai wacce ake kiranta ZATUL-ANWADI, suna lanqaya Takubansu a kanta.
Sai suka ce, " Yaa Ma'aikin Allah ! Ka sanya mana ZATAL-ANWADI kamar yadda su ma suke da ZATIL-ANWADI. Sai Annabi (S. A. W. W) yace,
" TSARKI YA TABBATA ! AI WANNAN SHINE KAMAR YADDA MUTANEN MUSA SUKA FADA, " KA SANYA MANA ABIN BAUTA KAMAR YADDA SU MA SUKE DA ABIN BAUTA. NA RANTSE DA WANDA RAINA KE HANNUNSA, DA SANNU ZA KU BI SUNNONIN WADANDA SUKA KASANCE GABANINKU ."
Abu Isah (Al-Tirmidhi) yace, wannan hadisi mai kyau ne kuma ingantacce. Kuma Abu Qaqidiy Al-Laithee sunansa shine Harith Bn Auf, kuma cikin babin, daga Abiy Sa'eed da Abu Hurairata.
(JAMI'US-SAHIH LI TIRMIDHI, BABIN DA SANNU ZA KU BI TAFARKIN WADANDA SUKA KASANCE GABANINKU)
Kunga abinda ya faru kenan, lokacin da Annabi Musa (A. S) ya tafi yin munajati da Allah ya bar Annabi Haruna (A. S) a matsayin jagora kafin ya dawo sai suka canza suka riqi dan Maraqi.
Hakama yayin da Annabi (S. A. W. W) ya koma ga Ubangijinsa ya bar al'amarin jagorancin al'ummarsa sai suka canza suka riqi wani dan Maraqi irin na al'ummata Musa (A. S).
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.
(08137925034)
4th May, 2021/ 22nd Ramadan, 1442.