Darussa 10 Daga Waqi'ar Gyallesu..!


 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


MAFI GIRMA SHINE 'DAUKAKA AMBATON SAYYID ZAKZAKY (H) 



         " وَرَفَعْنَا لَكَ ذِكْرَكَ "


Alqalami, baki ko tunanin dan Adam ba zai iya kawo darusan da waqi'ar Gyallesu ta haifar wacce ta auku daga ranar 12-14 cikin watan 12 na shekarar 2015 ba, sai dai kawai kowa ya ambaci abinda ya samu ko ya iya fahinta daga wannan waqi'ar. 


Ranar 12-12-2015 ne ta kasance ranar farko wacce Gwamnatin zalunci ta Buhari ta fara aiwatar da babban qudirinta kuma mataki na qarshe wanda a irin tsukakken tunaninsa yake gani zai iya kawo qarshen Sayyid Zakzaky (H) da da'awarsa, kuma aka dau tsahon cikakkun kwana biyu ana ruwan wuta kan raunana marar sa makami zuwa ranar 14-12-2015 kafin zazzafan ta'addancin nasu ya kawo qarshe. 


Mun ambace shi da zazzafa ne domin shine mafi iyakar abinda za su iya yi na ta'addancin, amma waqi'ar bata zo qarshe ba har zuwa yau da nake yin wannan rubutu, domin sakamakon wancan waqi'ar almajiransa sun dau mataki na hankali da ilimi na fafutukar ganin sako musu shi daga hannun wadannan miyagun azzalumai , kuma kan hakan ana yi musu dauki-dai-dai a duk lokacin da suka fito don nuna damuwarsu. 


DARUSAN DAKE CIKIN WAQI'AR 


Daga cikin darusan dake cikin wannan waqi'a akwai :-


(1)- GASKATA ALQAWARIN ALLAH :- Allah yayi alqawarin cewa ba zai taba barin bayinsa su riqi yin wani abu da sunan addini ba har sai ya jarrabe su don ya gane suwaye ke yi dominSa daga cikinsu. 


(2)- ABINDA SAYYID (H) YA FADA YA TABBATA :- Tun farkon kiran da Sayyid (H) ya soma ya bayyanawa mabiyansa cewa lalle wannan hanya akwai mutuwa fa cikinta. Har ma yace duk wanda bai shirya mutuwa ba ya ja da baya. To, lalle anga wannan abu a aikace. 


(3)- AN 'DEBI SHAHIDAI :- Kamar yadda Allah ya debi shahidai cikin mabiyan Annabawan da suka gabata, to, kamar haka ya debi shahidai cikin wannan waqi'a don ya rayar da addininsa. 


(4)- MAQIYA HARKA SUN BAYYANA :- Akwai da yawa wadanda wannan waqi'ar ta bayyanar da qiyayyarsu a fili wadanda kafin wannan lokaci ba za ka taba tsammaninsu haka suke ba.


(5)- AN GANE INDA DA'AWAR GASKIYA TAKE :- Sakamakon yadda kiraye-kiraye suka yi yawa sai ya zamana mutane suna son gaskiya su bita, amma kuma sun kasa gano inda take, sai wannan lokaci ta hanyar ganin alqawarin Allah ya tabbata.


(6)- BA A KAWAR DA GAAKIYA DA BAKIN BINDIGA :- A lokacin da Sayyid Zakzaky (H) yayi wannan furuci an sami wasu mutane masu ganin maganar a matsayin qarya, musamman ma wadanda suke da iko a hannunsu. Amma bayan wannan waqi'a sun yarda cewa lalle bakin Bindiga ba shi ikon komai wajen kawar da gaskiya ko ma'abotanta. 


(7)- TALLATA HARKA ISLAMIYYAH :- Kafin wannan waqi'a Sayyid (H) ya riqa gargadin Hukuma da cewa kada ta kuskura ta dirarwa Harka Islamiyyah, domin duk randa ta dirar mata ta tallata tane. Kuma abinda ya faru kenan, domin adadin wadanda suka fahinci wannan Harka bayan waqi'ar sun kai 40% na wadanda suka fahinceta tsahon shekaru 35 baya kafin wannan lokaci. 


(8)- BAYYANAR SON IYALAN GIDAN ANNABI (S. A. W. W) :- Akwai mutane wadanda suka yi karatu suka san Ahlul-Bait a karatu, amma basu san matsayinsu da haqqoqinsu a wayansu ba har sai bayan wannan waqi'a. A bayan wannan waqi'a ne aka sami wasu muryoyi masu nuna cewa Iyalan Annabi (S. A. W. W) sun fi kowa, kuma duk wanda ya riqe su zai ci karo da musifu da bala'o'i. 


(9)- ALLAH NA NUNA KISHINSA KAN BAYINSA :- Al'ummar Nigeria ta gano cewa taba bayin Allah da akayi a Zaria ne yayi sanadin fadawar Qasa cikin rudani da quncin rayuwa. Kuma wannan shaida ce wacce ke fitowa daga bakunan 'yan qasar, wanda hakan ya tabbatarwa mutane cewa Allah na kishin bayinsa salihai. 


(10)- 'DAUKAKA AMBATON SAYYID (H) :- Yana daga cikin dalilan dake sa wani ya sami wani matsayi madaukaki idan ya bi Allah da kuma jarrabawar da za ayi masa, matuqar ya cinye wannan jarrabawa sai daukakar Allah ta biyo baya. 


Annabi Ibrahim (A. S) bai sami daukaka ta zama Limami ga mutane ba har sai bayan an jarrabce shi ya cinye sannan ya sami wannan matsayi. Allah (T) na cewa; 


👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇



" وَإِذِ ٱبۡتَلَىٰٓ إِبۡرَٰهِـۧمَ رَبُّهُۥ بِكَلِمَٰتٖ فَأَتَمَّهُنَّۖ قَالَ إِنِّي جَاعِلُكَ لِلنَّاسِ إِمَامٗاۖ قَالَ وَمِن ذُرِّيَّتِيۖ قَالَ لَا يَنَالُ عَهۡدِي ٱلظَّٰلِمِينَ." ٤٢١


" KUMA A LOKACIN DA UBANGIJIN IBRAHIM YA JARRABCE SHI DA WASU KALMOMI KUMA YA CIKA SU SAI YACE, " LALLE NI MAI SANYA KA LIMAMI NE GA MUTANE. " YACE, (yaa Allah wannan alqawarin naka ya kasance) KUMA DAGA ZURIYATA. YACE, " LALLE ALQAWARINA BA YA SAMUN AZZALUMAI. "


      (BAQARA:124)


Wannan babban matsayi ne, amma duk da wannan matsayi nasa bai kai wanda aka bawa Annabi Muhammad (S. A. W. W). Domin shi nasa matsayin da ya samu shine daukaka ambatonsa cikin dukkan duniya.


       " وَرَفَعْنَا لَكَ ذِكْرَكَ "


" KUMA MUKA 'DAUKAKA MAKA AMBATON KA ."


Saboda haka a qalla kowacce rana ba za a iya qayyade adadin ambaton da ake yi masa ba. 


Da shike Sayyid Zakzaky (H) ya fito cikin al'ummar Manzon Allah (S. A. W. W) kuma mai koyi da umarninsa sai ya zamana cewa shi ma Allah ya daukaka ambatonsa cikin duniya sakamakon wannan waqi'ar Gyallesu. 


Babu mai musu cewa sanadin wannan waqi'ar ce sunan Sayyid (H) ya ratsa duniya, domin kafin wannan lokaci gurare da dama basu san da sunansa ba ballantana ma ace sun san da'awarsa. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.


       (08137925034)


13th May, 2021/ 2nd Shawwal, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post