@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
YANA SANE DA ABINDA ZAI FARO A KANSA CIKIN WANNAN RANA
Bayan yarjejeniyar da aka yi ta yaudara a yaqin Siffin, abinda ake kira TAHKIM tsakanin Amr Bn Al-As da Abu Musal Al-As'ariy, sai aka sami wata qungiya daga cikin musulmi wadanda ake kira KHAWARIJ suka fandare daga rundunar Imam Ali (A. S) suka yi masa tawaye, duk da cewa su suka yi sanadin faruwar duk abinda ya faru, domin Imam Ali (A. S) ya qi, su kuma suka ce yin wannan yarjejeniyar ita ce mafita.
To, bayan ganin nasarar da rundunar Imam Ali (A. S) a wannan yaqi sai wasu daga cikinsu suka yi taro a Makkah, suka tsayar cewa Amirul-muminina, Mu'awiyyah Bn Abiy Sufyan da kuma Amr Bn Al-As wadanda a tunaninsu wadannan mutane uku su suka hanawa ruwa gudu.
Saboda haka sai suka tsayar cewa Abdurrahman Ibn Muljam (L. A) shi zai kashe Imam Ali (A. S), saboda haka sai ya fara shiri zuwa Kufah inda Imam (A. S) ke da iko, ya ya tsara cewa zai kashe shi ne ta hanyar sara da Takobi yayin da yake sallah.
Wannan al'amari bai zame baqo ba, domin Manzon Allah (A. A. W. W) ya sanar da Imam Ali (A. S) faruwar wannan mummunan aiki.
Ya zo cikin wata riwaya kamar haka;
👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇
. 1- عيون أخبار الرضا عليه السلام لي، الأمالي للصدوق الطَّالَقَانِيُّ عَنْ أَحْمَدَ الْهَمْدَانِيِّ عَنْ عَلِيِّ بْنِ الْحَسَنِ بْنِ الْفَضَّالِ عَنْ أَبِيهِ عَنِ الرِّضَا عَنْ آبَائِهِ عَنْ أَمِيرِ الْمُؤْمِنِينَ ع فِي خُطْبَةِ النَّبِيِّ ص فِي فَضْلِ شَهْرِ رَمَضَانَ فَقَالَ ع فَقُمْتُ فَقُلْتُ يَا رَسُولَ اللَّهِ مَا أَفْضَلُ الْأَعْمَالِ فِي هَذَا الشَّهْرِ فَقَالَ يَا أَبَا الْحَسَنِ أَفْضَلُ الْأَعْمَالِ فِي هَذَا الشَّهْرِ الْوَرَعُ عَنْ مَحَارِمِ اللَّهِ عَزَّ وَ جَلَّ ثُمَّ بَكَى فَقُلْتُ يَا رَسُولَ اللَّهِ مَا يُبْكِيكَ فَقَالَ يَا عَلِيُّ أَبْكِي لِمَا يُسْتَحَلُّ مِنْكَ فِي هَذَا الشَّهْرِ كَأَنِّي بِكَ وَ أَنْتَ تُصَلِّي لِرَبِّكَ وَ قَدِ انْبَعَثَ أَشْقَى الْأَوَّلِينَ وَ الْآخِرِينَ شَقِيقُ عَاقِرِ نَاقَةِ ثَمُودَ فَضَرَبَكَ ضَرْبَةً عَلَى قَرْنِكَ فَخَضَبَ مِنْهَا لِحْيَتَكَ قَالَ أَمِيرُ الْمُؤْمِنِينَ ع فَقُلْتُ يَا رَسُولَ اللَّهِ وَ ذَلِكَ فِي سَلَامَةٍ مِنْ دِينِي فَقَالَ ص فِي سَلَامَةٍ مِنْ دِينِكَ ثُمَّ قَالَ ص يَا عَلِيُّ مَنْ قَتَلَكَ فَقَدْ قَتَلَنِي وَ مَنْ أَبْغَضَكَ فَقَدْ أَبْغَضَنِي وَ مَنْ سَبَّكَ فَقَدْ سَبَّنِي لِأَنَّكَ مِنِّي كَنَفْسِي رُوحُكَ مِنْ رُوحِي وَ طِينَتُكَ مِنْ طِينَتِي إِنَّ اللَّهَ تَبَارَكَ وَ تَعَالَى خَلَقَنِي وَ إِيَّاكَ وَ اصْطَفَانِي وَ إِيَّاكَ وَ اخْتَارَنِي لِلنُّبُوَّةِ وَ اخْتَارَكَ لِلْإِمَامَةِ فَمَنْ أَنْكَرَ إِمَامَتَكَ فَقَدْ أَنْكَرَ نُبُوَّتِي يَا عَلِيُّ أَنْتَ وَصِيِّي وَ أَبُو وُلْدِي وَ زَوْجُ ابْنَتِي وَ خَلِيفَتِي عَلَى أُمَّتِي فِي حَيَاتِي وَ بَعْدَ مَوْتِي أَمْرُكَ أَمْرِي وَ نَهْيُكَ نَهْيِي أُقْسِمُ بِالَّذِي بَعَثَنِي بِالنُّبُوَّةِ وَ جَعَلَنِي خَيْرَ الْبَرِيَّةِ إِنَّكَ لَحُجَّةُ اللَّهِ عَلَى خَلْقِهِ وَ أَمِينُهُ عَلَى سِرِّهِ وَ خَلِيفَتُهُ عَلَى عِبَادِهِ[1].
Ya zo cikin Uyunil-Akbar na Ridha (A. S) da Amaliy Lis-Sudduq Ad-'Dalaqaniyyu, daga Ahmad Al-Mahdaniy, daga Aliyu Bn Hassan Bn fadhal, daga babansa daga Ridha (A. S), daga iyayensa, daga Amirul-muminina (A. S) cikin Khudubar Annabi (S. A. W. W) game da falalar watan Ramadana, sai (A. S) yace;
" Sai nace, yaa Ma'aikin Allah ! Menene mafificin aiki cikin wannan wata ? Sai yace, " YAA BABAN HASSAN ! MAFIFIN AIKI CIKIN WANNAN WATA SHINE KAMEWA DAGA ABUBUWAN DA ALLAH MAI GIRMA DA 'DAUKAKA YA HARAMTA ."
" Sa'an nan yayi kuka. Sai nace, yaa Ma'aikin Allah! Kukan me kake yi ? Sai yace, " YAA ALIYU ! INA KUKA NE SABODA ABINDA ZA HALATTA SHI A KANKA CIKIN WANNAN WATA, KAMAR INA TARE DA KAI, KAI KUMA KANA SALLAH GA UBANGIJINKA, SAI A AIKO MAFI SHAQAWAR NA FARKO DANA QARSHE WANDA YA SOKE TAGUWAR SAMUDAWA , ZAI SARE KA A TSAKIYAR KANKA JINI YA KWARARA DAGA GARE SHI ZUWA GEMUNKA. "
Sai Amirul-muminina (A. S) yace, " Sai nace, yaa Ma'aikin Allah ! In ce dai hakan akwai aminci cikin addinina ? Sai yace, " CIKIN AMINCI DAGA ADDININKA. "
Sa'an nan (S. A. W. W) yace, " YAA ALIYU ! DUK WANDA YA KASHE KA NI YA KASHE, KUMA DUK WANDA YA FUSATA KA NI YA FUSATA, KUMA DUK WANDA YA ZAGE KA NI YA ZAGA, DOMIN KAI A WAJENA TAMKAR RUHINA NE, RUHINKA DAGA RUHINA YAKE . LALLE ALLAH (T) YA HALICCENI NI DA KAI, KUMA YA ZABENI NI DA KAI, SANNAN YA KEBANCENI DA ANNABTA, KAI KUMA YA KEBANCEKA DA IMAMANCI. DUK WANDA YAYI INKARIN IMAMANCINKA HAQIQA YAYI INKARIN ANNABTA TA.
YAA ALIYU ! KAINE WASIYYINA KUMA BABAN 'YA'YANA KUMA MIJIN 'YATA KUMA KHALIFANA AKAN AL'UMMATA CIKIN RAYUWATA DA BAYAN MUTUWATA. UMARNINKA UMARNINA NE, KUMA HANINKA HANINA NE. INA RANTSUWA DA WANDA YA AIKO NI DA ANNABTA KUMA YA SANYA NI MAFI ALKHAIRIN AL'UMMA, LALLE KAINE HUJJAR ALLAH AKAN HALITTUNSA KUMA AMINTACCENA AKAN SIRRINSA, KUMA KHALIFANSA AKAN BAYINSA. "
Ya zo cikin wata riwaya kuma kamar haka;
2- ن، عيون أخبار الرضا عليه السلام أَبِي عَنْ سَعْدٍ عَنِ ابْنِ أَبِي الْخَطَّابِ عَنِ الْحَكَمِ بْنِ مِسْكِينٍ عَنْ صَالِحِ بْنِ عُقْبَةَ عَنْ أَبِي جَعْفَرٍ ع[2] قَالَ: جَاءَ رَجُلٌ مِنَ الْيَهُودِ إِلَى أَمِيرِ الْمُؤْمِنِينَ ع فَسَأَلَهُ عَنْ أَشْيَاءَ إِلَى أَنْ قَالَ كَمْ يَعِيشُ وَصِيُّ نَبِيِّكُمْ بَعْدَهُ قَالَ ثَلَاثِينَ سَنَةً قَالَ ثُمَّ مَهْ يَمُوتُ أَوْ يُقْتَلُ قَالَ يُقْتَلُ يُضْرَبُ عَلَى قَرْنِهِ فَتُخْضَبُ لِحْيَتُهُ قَالَ صَدَقْتَ وَ اللَّهِ إِنَّهُ لَبِخَطِّ هَارُونَ وَ إِمْلَاءِ مُوسَى ع الْخَبَرَ[.
Daga Sa'eed, daga dan baban Khaddab, daga Hakaam Bn Miskeen, daga Salih Bn Uqbata, daga Abu Ja'afar (A. S) yace;
" Wani mutum daga cikin Yahudawa ya zo wajen Amirul-muminina (A. S), sai ya tambaye shi game da abubuwa masu yawa har inda yace, " Shin shekaru nawa wasiyyin Annabinku zai yi a bayansa? " Yace, " SHEKARU TALATIN (30)."
Yace, " Sa'an nan ta yaya zai mutu ko ta yaya za a kashe shi ?" Yace, " ZA A KASHE SHI NE TA HANYAR SARANSA A KANSA HAR SAI GEMUNSA YA JIQE.
Yace, " Ka yi gaskiya. Wallahi haka yake a rubutun Haruna wanda Musa yayi Imla'insa. "
بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج42، ص: 191
To, a yayin da Imam Ali (A. S) ya isa masallaci ya kira sallah ya fara jagorancin mutane sai wannan la'anannen Allah (Abdurrahman Bn Muljam) ya fito daga cikin sahu ya sare shi da Takobi mai guba a tsakiyar kansa yayin da yayi sujadah. Sahabban Imam Ali (A. S) sunyi nasarar kame wannan dan ta'addan. Wannan abu kuwa ya faru ne ranar 19th Ramadan, 40 (B. H).
Imam ya cigaba da jinyar wannan mummunan sara da akayi masa har zuwa lokacin da yayi shahada ranar 21th Ramadan, 40 (B. H). Kuma cikin wannan kwanaki ya miqa ragamar jagoranci zuwa ga dansa Imam Hassan (A. S).
Kafin shahadar tasa (A. S) yayi wasiyya mai tsaho ga 'ya'yansa Imam Hassan da Husaini (A. S), cikin Khudubar ya shafi tsarda sallah, bayar da zakkah, taimakon wanda aka zalunta, dagewa kan gaskiya, tsanani kan azzalumai, haqqin marayu, maqwabtaka, dakin Ka'abah da dai sauransu.
AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARE KA YAA AMIRUL-MUMININA, A RANAR DA AKA HAIFE KA DA RANAR DA KAYI SHAHADA DA KUMA RANAR DA ZA A TASHE KA KANA RAYAYYE !"
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.
(08137925034)
3rd May, 2021/ 21th Ramadan, 1442.