An karrama Shaikh Adamu Ahmad Tsoho da takardan lambar yabo da girmamawa.
Inda shugaban Dandalin Matasa na Yankin Jos; Malam Musa Umar Chajj-Chaji ya miƙa masa a madadin Matasan Harka Islamiyyah.
Sannan kuma ta baiwa Malam Ibrahim Tahir Gyallesu lambar jinjina ta musamman a gareshi da yayi Tattaki tun daga Zaria, ya jagoranci Zikiran Tunawa da Shahidan Dandalin Matasa na Yankin. Sheikh Adamu Ahmad Tsoho ne ya miƙa masa.
Ta karrama wasu ɗai-ɗaikun Mambobinta, da kuma yankuna da suka haɗa da; Jos, Saminaka, Lafia, Keffi, Doma, Gumau da Doguwa. Sheikh Yusuf Abubakar ne ya miƙa musu lambar girmamawar.
An karrama su jiya Lahadi 30-May-2021, a wajen taron Ƙarawa Juna Sani (Mu’utamar) karo na 10 a garin Doguwa.
#DoguwaMuutamar2021
#DandalinMatasaJosZone
— Muh'd Jawad Assaminaky
@ Media Forum Saminaka
21-Shawwal-1442H. 31-May-2021.