Sayyid Ibraheem Zakzaky Hafizahullahu shine Jagoran duk wani mumini a kasar nan, musamman mai motsi wanda yake jin shi dan gwagwarmayar tabbatar addinin Allah ne, yana garqame a kurkuku kusan kwanaki 2000 bayan ta'addancin da aka yi masa.
Yau da nake maganar nan kwana 1997 da cin mutuncin sa,
Zubar da jinin sa,
Kona dukiyar sa, rusa muhallinsa,
tarwatsa littaffan sa,
Ruguza tattalin arziqin sa,
Kona abubuwan tarihi masu tasiri a gaban sa,
Kona duk suturar sa,
Da duk wanda yake gidan sa,
Konawa da sace motocin sa,
Kona na'urorin computer da sauran duk wani abu da yake nasa,
Kashe 'Ya' yan sa hudu (4) a gaban sa,
Kona yayar sa a gaban sa,
Yiwa Matar sa ruwan harsasai a gaban sa,
Kashe kusan duk wadanda suke gidan sa,
Bayan hallaka mutum dubu na almajiran sa,
An masa ruwan wuta na harsasai marasa adadi.
Sun tafi dashi cikin mawuyacin hali da sai da jinin sa ya tsiyaye.
Suna murna sun kashe shi suka tafi da shi cikin mawuyacin hali zuwa in da su ka so. Allah ya isa !!! 😭
Ya ku 'yan uwa na na Imani me kukeyi don ganin ya samu yanci?
Me mukeyi domin taimaka ma sa?
Ina dimbin almajiran sa? da mu ke gani a gaban sa lokacin Tattakin Arba'in ko Yaumus shuhada?
Ina miliyoyin Mabiyan sa da muke gani ranar Mauludi?
Ga jarabawa kan Jagora ina mabiya?
Ina mataimaka?
Shin Mabiyan nasa sun hada kai sun zage ne wurin neman hakkin sa da 'yan cin sa, suna fuskantar azzaluman mahukunta?
Ko sun rarraba, sun tarwatse, sun rafkane sun koma fada tsakanin su?
Nawa ne cikin su suka tare a Abuja ko suke tura tallafin su Abuja?
Mutum nawa ke Muzahara a Kaduna ko suke karfafar tsirarun dake Muzahara a Kaduna?
Lokacin da Azzalumi Buhari yasa ake kashe masu fafutikar neman yancin Jagora a Abuja da lokacin da Elrufa'i ke kashe masu neman yancin Jagora a Kaduna
Kana ina? Kuma me kake yi?
Allamah Hafizahullahu ya sha gaya mana "taron yawa ya fi taron karfi"
"Ba Allah suke tsoro ba yawan ku suke tsoro"
Jagora na bin mu bashin alkawarin nan da muka dauka a gaban sa na cewa
*BIDDAM WAR RUH LABBAIKA YA ALZAKZAKY*
Free Sayyid Zakzaky!
Free Shaikh Zakzaky!!
Free Allamah Zakzaky!!!
#Kwana2000 ba kwana2 bane✌️
#AllahSaveZakzaky
31/05/2021