Ayau Laraba 5/05/2021 Jagoran harka islamiyya Sayyid Ibrahim Zakzaky (H) ya shiryawa Iyayen shahidai buda baki na musamman a muhallin *MAC DALAS Restaurantst and Cartering Services* (Vanilla) dake garin Bauchi.
Shan ruwan wanda ya kunshi iyayen shahidai maza da mata yara da manya ya samu halartar mahalarta da yawa, bayan bude taron da addua, sai wakilin 'yan uwa na garin Bauchi Shaikh Ahmad Yusuf Yashi ya gabatar da takaitaccen hadafi da manufar wanan shan ruwa da cewa
"Adai dai wannan lokaci ne mukasami wani tagomashi daga jagorancin wannan harka na kasa baki daya, a wasu wurare na kasar ma yanzu haka ana shirya irinsa, kuma ya takaita kadai ga iyalan shahidai, mahaifi, mahaifiya, kani ko yayan shahidai wanda su malam (H) suka shirya,
Bamu da kalmomin godiya ga su Malam sai addu'a dafatan cikar burinsu na ganin tabbatuwar addini a wannan nahiya tamu baki daya".
Bayan kammala jawabinsa din ne sai aka fara gabatar da shan ruwa.
Iya kallonka kowane tuburi dauke yake da Iyayen shahidai cikin yanayi na farinciki da annashuwa a fuskarsu din.
Shiek Ahmad Yusuf Yashi shi ya jagoranci samun ladan hidimtawa shuhada'u ta hanyar raba abinci gaban kowani mahalarci, An sanya Kankana, lemo, ruwan roba, lemon roba, Maltina da kuma wata shahararriyar Jalop rice da quarter din kaza akai wasu ma rabi suka samu agaban kowa.
Lallai iyayen shahidai ransu ya faranta kwarai da gaske bisa zahirin abinda muka iya hangowa, kuma sunci sunyi hani'an kamar yadda aka shirya tare da addu'a da fatan alkhairi.
Bayan kammalawa ne akayi addu'a aka sallami kowa cikin farin ciki da annashuwa.
Ga kadan cikin hotunan da muka dauko muku.
-Saifullah Ningi