@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
'DABI'AR KAFIRAI CE KASHE ANNABAWA DA MASU YIN UMARNIN AIKATA ADALCI DAGA CIKIN MUTANE
Wannan ita ce sunnah ta magabata wacce ake samunta cikin kowanne qarni daga cikin qarnoni. Allah kan tayar da Annabawa (A. S) da wasu bayinsa salihai wadanda babu dama suga ana aikata zalunci sannan suyi shiru ba tare da yin hani ba.
Su kuwa kafirai da azzalumai burinsu shine aikata zalunci, saboda haka aka samu da yawa daga cikinsu sun karkashe Annabawa (A. S) da kuma wasu bayin Allah salihai wadanda suka dage wajen tabbatar da gaskiya da adalci.
Allah (T) ya gargadi irin wadannan mutane ta hanyar yi musu bushara kamar haka;
👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇
" إِنَّ ٱلَّذِينَ يَكۡفُرُونَ بِـَٔايَٰتِ ٱللَّهِ وَيَقۡتُلُونَ ٱلنَّبِيِّـۧنَ بِغَيۡرِ حَقّٖ وَيَقۡتُلُونَ ٱلَّذِينَ يَأۡمُرُونَ بِٱلۡقِسۡطِ مِنَ ٱلنَّاسِ فَبَشِّرۡهُم بِعَذَابٍ أَلِيمٍ." (١٢)
" LALLE WADANDA SUKE KAFIRCEWA GAME DA AYOYIN ALLAH KUMA SUKE KASHE ANNABAWA BA BISA WANI HAQQI BA, SANNAN KUMA SUNA KARKASHE WADANDA SUKE YIN UMARNI DA ADALCI DAGA CIKIN MUTANE, KUYI MUSU BUSHARA DA AZABA MAI RADADI. "
(SURATUL-AL IMRAAN :21)
Iya wa'azi da hikima babu kamar Annabawa da Manzanni (A. S), amma hikimar yin wa'azin nasu bai tsare su daga cutarwa da kuma kashewa daga mutanen da suke yiwa wa'azin ba.
Hakan kuwa sai zama tamkar wata sunnah da azzalumai yin fada da Annabawansu da bayin Allah daga cikinsu masu kiransu zuwa ga tsarkaka. Saboda haka ba zai taba yiwuwa ace kana bin haqiqanin sunnar Annabawa da Manzanni (A. S) ba sannan kuma ace an barka ba tare da an cutar dakai ko kashe ka ba.
An bamu labarin irin wannan kisa da aka yiwa Annabawa da bayin Allah salihai cikin wani hadisi, saboda haka muka ga ya dace mu kawo muku shi don ku auna da da'awarku kuga shin, irin abinda ya same su shine ke faruwa cikin da'awarku? Ga riwayar nan kamar haka;
👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇
وقال ابن أبي حاتم حدثنا أبو الزبير الحسن بن علي بن مسلم النيسابوري نزيل مكة حدثني أبو حفص عمر بن حفص يعني ابن ثابت بن زرارة الأنصاري حدثنا محمد بن حمزة حدثنا أبوالحسن مولى لبني أسد عن مكحول عن أبي قبيصة ابن ذؤيب الخزاعي عن أبي عبيدة بن الجراح رضي الله عنه قال قلت يا رسول الله أي الناس أشد عذابا يوم القيامة قال رجل قتل نبيا أو من أمر بالمعروف ونهى عن المنكر ثم قرأ رسول الله صلى الله عليه وسلم « إن الذين يكفرون بآيات الله ويقتلون النبيين بغير حق ويقتلون الذين يأمرون بالقسط من الناس فبشرهم بعذاب أليم » الآية ثم قال رسول الله صلى الله عليه وسلم يا أبا عبيدة قتلت بنو إسرائيل ثلاثة وأربعين نبيا من أول النهار في ساعة واحدة فقام مئة وسبعون رجلا من بني إسرائيل فأمروا من قتلهم بالمعروف ونهوهم عن المنكر فقتلوهم جميعا من آخر النهار من ذلك اليوم فهم الذين ذكر الله عز وجل وهكذا رواه ابن جرير عن أبي عبيد الوصابي محمد بن حفص عن ابن حمير عن أبي الحسن مولى بني أسد عن مكحول به وعن عبد الله بن مسعود رضي الله عنه قال قتلت بنو إسرائيل ثلاثمئة نبي من أول النهار وأقاموا سوق بقلهم من آخره رواه أبو حاتم ولهذا لما أن تكبروا عن الحق واستكبروا علىالخلق قابلهم الله على ذلك بالذلة والصغار في الدنيا والعذاب المهين في الآخرة فقال تعالى « فبشرهم بعذاب أليم » أي موجع مهين « أولئك الذين حبطت أعمالهم في الدنيا والآخرة وما لهم من ناصرين »
Ibn Abiy Haateem yace, Abu Zubair Al-Hassan Bn Aliyu Bn Muslim Annaisaburi ya bamu labari, Abu Hafsi Umar Bn Hafsi, ana nufin Ibn Thabeet Bn Zurarata Al-Ansariy ya bani labari, Muhammad Bn Hamzata ya bamu labari, Abu Hassan majibinci ga Bani Asad ya bamu labari daga Makahul, daga Abu Qubaisata Ibn Zu'uyibu Al-Kuzaa'eey, daga Abu Ubaidata Bn Jarraaha (R. A) yace;
" Nace, yaa Ma'aikin Allah ! Wadanne mutane mafiya tsananin azaba ranar alqiyama ? Yace;
" MUTUMIN DA YA KASHE ANNABI KO KUMA YA KASHE WANDA KE YIN UMARNI GAME DA KYAKKYAWA DA KUMA YIN HANI GAME DA MUMMUNA. "
Sa'an nan Manzon Allah (S. A. W. W) ya karanta;
" LALLE WADANDA KE KAFIRCEWA AYOYIN ALLAH KUMA SUNA KASHE ANNABAWA BA BISA HAQQI BA, KUMA SUNA KARKASHE WADANDA SUKE YIN UMARNI DA ADALCI DAGA CIKIN MUTANE, TO, KUYI MUSU BUSHARA DA AZABA MAI RADADI !"
Sa'an nan Manzon Allah (S. A. W. W) yace;
" YAA BABAN UBAIDATA ! BANU ISRA'IL SUN KASHE ANNABAWA 43 A FARKO YINI CIKIN SA'A 'DAYA. SA'AN NAN (bayan wannan kisan da aka yiwa Annabawa) SAI MUTANE 170 SUKA TASHI DAGA (cikin) BANU ISRA'ILA SUNA UMARNIN KYAKKYAWA GAME DA WADANDA SUKA KISAN, KUMA SUNA YI MUSU HANI GAME DA AIKATA MUMMUNA. SAI SUKA KASHE SU GABA 'DAYANSU SU (170) DAGA QARSHEN WANNAN YINI NA WANNAN RANA . SUNE WADANDA ALLAH MAI GIRMA DA 'DAUKAKA YA AMBATA "
To, kamar hakane ma Ibn Jareer ya riwaito daga Abu Ubaida Al-Waasabiy Muhammad Bn Hafsi, daga Ibn Humair, daga baban Hassan bawan Banu Asad, daga Makahul, kuma daga Abdullahi Bn Mas'ud (R. A) yace;
" Banu Isra'ila sun kashe Annabawa dari uku (300) daga farkon yini,.....daga qarshensa. "
Sannan kuma Abu Haateem ya riwaito cewa, saboda hakane yayin da suka yi girman kai daga gaskiya sannan kuma suka yi girman kai akan halittu sai Allah ya kama su akan haka da qasqanci da qasqanci cikin duniya, da kuma mummuniyar azaba a lahira.
Allah madaukakin Sarki yace;
" KAYI MUSU BUSHARA DA AZABA MAI RADADI !" Abin nufi shine makoma ta tozarci.
" WADANNAN SUNE WADANDA AYYUKANSU YA BACI A DUNIYA DA LAHIRA, KUMA BA SU DA MATAIMAKI GARE SU. "
(TAFSIR IBN KATHEER)
Kenan dole ya zama ana kashe masu yin umarni da kyakkyawa kuma suna yin hani game da mummuna.
ASHE DAI KASHE BAYIN ALLAH 1000 CIKIN KWANA BIYU A ZARIA BA ABIN MAMAKI BANE.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.
(08137925034)
30th May, 2021/ 19th Shawwal, 1442.