@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
FALALAR DA ALLAH YA YIWA 'YAN 'DARIQU DA 'YAN SHI'AH
Ba kowa ne yayi irin wannan nazari ba domin a iya tunani na wasu ba za su taba daukar wannan a matsayin wani abin nazari ko la'akari ba ballantana suyi nazarin hakan.
Duk da cewa Annabi (S. A. W. W) yace al'ummarsa za ta kasu gida 73 (a bangaren fahinta ko da'awa), amma idan kayi nazari za kaga gaba daya cikin tushe (base) biyu ne za a sami wadannan adadi, saboda haka anfi bada qarfi cewa tushen guda biyu ne.
(1)- Idan kaji a yanzu wani na da'awar cewa shi dan Shi'ah ne, to, idan ka bibiya za kaga ya fito ne daga cikin wadanda ake kira 'yan 'Dariqa ne, ma'ana za kaga ya taso ne cikin makarantun 'Dariqu. Wannan dalili yasa za kaga anfi samun kusantaka a tsakaninsu ta bangarori da dama. Misali:-
- Guraren karatukansu na addini.
- Guraren sallolinsu da kuma
- Haduwarsu kan soyayyar Manzon Allah (S. A. W. W) da iyalan gidansa tsarkaka (A. S).
Dalilin wannan kusantaka tasu kuwa shine, idan ka bibiyi sassalarsu za kaga ta sun hadu akan Imam Hassan ko Imam Hussaini (A. S) 'ya'yan Sayyidah Fatimah (S. A) ne.
Wanda ka sami nasabarsa ta hadu da wadannan mutane biyu, to, jikoki ne na Manzon Allah (S. A. W. W). Saboda haka yasa cikinsu ne kadai ake samun Sharifai ko Waliyyai.
Akwai yiwuwar wani yace in wannan magana tawa gaskiya ce me yasa ba a hadu dukka an zama Sharifai ko Waliyyai ba tunda jikokin Manzon Allah (S. A. W. W) ne?
Amsar da zan bawa mai wannan tambaya ita ce, ka duba qissar Annabi Nuhu (A. S) game da abinda ya faru tsakaninsa da dansa yayin da akayi ruwan 'Dufana har Allah ya kawo mana cikin Alqur'ani kamar haka.
👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇
وَنَادَىٰ نُوحٞ رَّبَّهُۥ فَقَالَ رَبِّ إِنَّ ٱبۡنِي مِنۡ أَهۡلِي وَإِنَّ وَعۡدَكَ ٱلۡحَقُّ وَأَنتَ أَحۡكَمُ ٱلۡحَٰكِمِينَ ٥٤
" KUMA NUHU YA KIRAYI UBANGIJINSA YACE, " UBANGIJI LALLE 'DANA FA NA DAGA CIKIN IYALINA (amma za ka halakar dashi) KUMA ALQAWARINKA GASKIYA NE (na taimakon bayinka), KUMA KAINE MAFI (sanin) HUKUNCIN MASU HUKUNCI ."
Sai Allah (S. W. A) ya amsa masa da cewa;
قَالَ يَٰنُوحُ إِنَّهُۥ لَيۡسَ مِنۡ أَهۡلِكَۖ إِنَّهُۥ عَمَلٌ غَيۡرُ صَٰلِحٖۖ فَلَا تَسۡـَٔلۡنِ مَا لَيۡسَ لَكَ بِهِۦ عِلۡمٌۖ إِنِّيٓ أَعِظُكَ أَن تَكُونَ مِنَ ٱلۡجَٰهِلِينَ ٦٤
" YACE, " YAA NUHU ! LALLE FA SHI (wannan da naka) BA YA DAGA CIKIN IYALINKA (na kirki), DOMIN SHI WANI AIKI NE BA NA KIRKI BA, SABODA HAKA KADA KA TAMBAYE NI GAME DA ABINDA BAKA DA ILIMI A KANSA. LALLE NI INA GARGADINKA KADA KA KASANCE (masu yin aiki) A RASHIN SANI. "
(SURATUL-HUD, AYA TA 45-46)
Kunga anan bisa tunani irin na Annabi Nuhu (A. S) shine wannan yaro nasa ne daga cikin iyalinsa, amma Allah da Kansa ya cire shi daga cikin iyalan nasa yace shi wani aiki ne ba na gari ba.
Irin haka ta faru a yaqin JAMAL, yayin da Imam Ali (A. S) ya tura dansa Ibn Hannafiyyah cewa ya ratsa cikin wannan runduna ta su 'Dalha, Zubair da Ummul-muminina A'isha ya riqo Linzamin Raqumin da ta hau ya saukar da ita qasa, amma sai ya kasa kutsawa cikin wannan runduna. Sai ya tura Imam Hassan (A. S) ya aiwatar da abinda aka sa shi.
Ibn Hannafiyyah bai ji dadi cikin zuciyarsa ba da yaga ya kasa yin abinda Hassan ya aikata. Sai Imam Ali (A. S) ya daga kafadarsa yace masa, " KAYI HAQURI ! AI KAI 'DANA NE, HASSAN KUMA 'DAN MANZON ALLAH (S. A. W. W) NE. "
Duk da cewa Imam Ali (A. S) na daga cikin Ahlul-Bait (A. S) kuma Sharifi Waliyyi amma dansa Ibn Hannafiyyah bai sami jaruntaka irin tasa ba, shi kuma Imam Hassan (A. S) jininsa ne kuma jinin Sayyidah Fatimah (S. A). Saboda haka matsayinsa yafi na wanda ya hadu da Annabi (S. A. W. W) ta bangare daya.
(2)- Sannan kuma duk inda kaji ana cewa wani Basalafe ne ko Boko Haram ko Shabbab ko ISIS da sauransu za kaga tushensu shine IZALAH. Ita kuma Izalah tushenta shine UMAYYAH wadanda anan qasa ake kiransu Banu Umayyah (L. A).
Banu Umayyah kuwa sune mafi tsananin gaba da Annabi (S. A. W. W) da iyalan gidansa (A. S), sannan kuma sune suka qyanqyashe wadanda suka yi rubuce-rubuce na cin zarafin Manzon Allah (S. A. W. W) don su nuna wata falala ta wani daga cikin Sahabbansa a kansa, tare da kare martabarsu ko da kuwa ace ta Manzon Allah (S. A. W. W) za ta qasqanta.
Wannan dalili yasa ba za ka taba samun Sharifai ko Waliyyai cikin 'yan IZALA ba, domin zuriyar Banu Umayyah ce wadanda suka daukarwa kansu alqawarin sai sun bice hasken gidan Manzon Allah (S. A. W. W).
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.
(08137925034)
16th May, 2021/ 5th Shawwal, 1442.
Al'hamdulillah tunda a Cikin Maganar ka tun farko ka kafirtar Da Dan Dariqa Tunda ka kwantan ta Shi Da Annabi Nuhu A S Da Dansa Da ubangiji ya Sanar Dashi cewan Shi ba Ahlinsa Bane
ReplyDeleteKuma Ka Jin Gina su Daga tushe Daya Amma munyi GABA kun barsu
Sai Se Kuma ka manta Da cewan Babu Wani littafin Da mu Yan izala Muke Riqo Dashi face shine yan Dariqa Ke tunqaho Dashi Mun Hadu a komai Da Yan Dariqa Kaman yanda Babu Wani Dan Dariqa Da Zai yarda a jefa zargi ma Wani Daga Cikin sahabban Annabi Rahma s.a.w.