Ashe Shaikh Ɗahiru Usman Bauchi Ya Koma Shi'ah


 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UUPDATED @


FAHINTAR MASU GANIN BIN GASKIYA SHI'ANCI NE 


Ko kadan babu wannan kalma cikin furucinsa in ka cire wani aiki da ya aikata wanda wasu ke ganin shi'anci ne ko kuma aiki irin na 'yan Shi'ah. 


Ba shine Karon farko wanda aka sami sabani wajen ganin jinjirin watan Shawwal ko Zul-Hijjah ba, domin akwai lokacin da mabiya Sheikh Sani Yahya Girjir suka yi sallar Idi kafin ranar da Sarkin musulmi ya ambata. Haka ma Sheikh 'Dahiru Usman Bauchi. 


Su kuwa 'yan Shi'ah babu adadi wajen samun irin wannan sabani, domin asali su ba sun dogara da ganin watan Sarkin musulmi ko bayyanawarsa bane. A kowacce rana ta kwanan duniya suna da lissafinsu na muslimci wannan suke qididdigewa, saboda haka dashi suke amfani wajen duban jinjirin wata. Sai ya zamana wani lokaci yakan zo daidai da wanda Sarkin Musulmi ke bayyanarwa, wani lokaci kuma akan sami sabani. 


Ba ya daga cikin sharadin muslimci ya zama cewa ana bin ra'ayin wani cikin ayyuka wajibai, a duk lokacin da gaskiya ta bayyana binta ake yi ko da daga bakin wa ta fito.


Rashin yardar mutum wajen karbar gaskiya ba zai sa Allah ya tabbatar da qarya a mamadinta ba, haka kuma yarda da qarya ba ya sa Allah ya rusa gaskiya. A ko da yaushe Allah na amfani da gaskiya ce ko da kuwa duniya za su hadu su bijire mata. 


An sha tsinewa 'yan Shi'ah da kafirta su kawai don sun bayyanar da gaskiyar ganin jaririn wata ba tare da bin son zuciyar Sarkin Sokoto, alhali babu inda aka ce bin umarninsa na daga cikin sharadin cikar imani. 


To, yau dai Sheikh 'Dahiru Usman Bauchi yayi sallar Idi cikin garin Bauchi bisa hujjarsa ta cewa anga jaririn watan Shawwal ranar talata 11-5-2021. Kuma ba komai ne yasa shi yin wannan sallah ba sai dai kawai bin Umarnin Allah dana Manzonsa (S. A. W. W) na cewa a dau azumi yayin da aka ga jaririn watan Ramadan, kuma asha ruwa yayin da aka ga jaririn watan Shawwal.


Sai dai kuma bisa fahinta ta wasu suna ganin bin gaskiya Shi'anci ne, saboda haka suke gani abinda Sheikh yayi na bin umarnin Allah da Manzonsa (S. A. W. W) goyon bayan ayyukan 'yan Shi'ah ne. 


Shi kuwa Shehi ko a mafarki bai taba yi cewa yana sha'awar Shi'ah ba ballantana shiga cikinta ko yin ayyukanta, to, kamar haka ne ba a taba ji cikin furucinsa ko ayyukansa yana nuna cewa yana tarayya da 'yan Shi'ah ba. 


ASHE DAI BIN GASKIYA DA AIKATATA SHINE SHI'ANCI. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.


        (08137925034)


12th May, 2021/ 1st Shawwal, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post