Karkashin Jagorancin Malam Ibrahim Imam wakilin Yan uwa Almajiran Sheikh Zakzaky (H) na garin Kontagora da kewaye.
Tawagar 'Yan uwa da suka kai wannan ziyarar ta ta'aziya Gidan Mai Martaba Sarkin Kontagora akan Kashe masa 'Dan sa Alhaji Bashir Sa'idu Namasaka, da wasu mutane biyu Daga cikin Hadiman gidan da wasu 'Yan BINDIGA sukayi a Ranar Alhamis 20/05/2021. Ta hada wakilin Yan uwa Almajiran Sheikh Zakzaky (H) na Garin Kontagora Malam Ibrahim Imam, Malam Muhammad Tukur wakilin Yan uwa na garin Babban Rami, da wakilan Academic Forum, da wakilan Dandalin Matasa, wakilan Mu'assatush Shuhada,Wakilan Harisawa, da wakilan Ahaludusur, Wakilan Media, Isma da dai sauransu.
An gudanar da wannan ziyarar ta'aziya cikin aminci. Tare da yin addu'a ga mamacin.
Haka zalika Sarkin ya
nuna Jin dadin sa ga Yan uwa Almajiran Sheikh Ibrahim Zakzaky (H). Bisa wannan jajen ta'aziyyar da suka zo masa.
Daga Kuma aka yi gaisuwa ta mutunci da ban kwana ga juna.
Kamar yadda zaku iya ganin yadda Ta'aziyar ta Gudana a cikin Hotona.
Daga wakilinmu
Shana Islam.
23 May, 2021