Almajiran Sheikh Ibraheem Zakzaky Sun Gudanar Da Taron Tunawa Da Ranar Haihuwar Shaheed Sayyid Muhamud Ibraheem Zakzaky A Darur-Rahma, Zaria



 SHAHED SAYYID MAHMUD ZAKZAKY(shehi)

 SARKIN HAQURI.


 Litini 31/5/2021 Almajiran Sheikh Ibraheem Zakzaky suka gabatar da taron tunawa da ranar Haihuwar Shaheed Sayyid Muhamud Ibraheem Zakzaky a makwancinsa dake maƙabatar Shahidai Daru-rahama dake danbo Zaria.

Taron ya samu halartar Wasu daga cikin Malamai, cikinsu har da Sheikh Abdulhameed Bello.





Malam Tahir Ibraheem shi ne mai jawabi na farko inda ya batar da taƙaitaccen tarihin Shehid Sayyid Muhamud. Malam ya ta6o wasu 6angarori da dama na halayyar wannan babban gwarzo. 





A cikin jawabin na sa, Malam Tahir ya kawo wasu ƙissoshi masu muhimmanci a kan rayuwar Shahidin, daga ya kawo 6angaren karatunsa inda ya ce, Shahid Muhamud ya kasance mutum mai hazaƙa fiye da tunanin mutane,domin kuwa kafin Shahadarsa ya haddace Alqur'ani, domin shi mutun mai baiwar haddace karatu komai tsawonsa a cikin gajeren lokaci, sannan kuma mutum ne mai hakuri, wanda har su 'Yan uwansa su Shaheed Sayyid Ahmad sun yi masa shaida a kan hakurinsa.

Bayan Malam Tahir ya kammala jawabin na sa ne sai Malam Musa T/jukum ya gabatar da jawabin ƙarfafa Yan uwa musamman matasa a kan al'amarin fita Muzaharar neman sakin Sheikh Ibraheem Zakzaky, Malamin ya gabatar da jawabai masu muhimmanci sosai a wannan 6angaren.

Sai kuma Sheikh Abdulhameed Bello shi ne ya mai jawabi na ƙarshe a wurin taron, a cikin jawabin na sa da farko Malamin ya fara ne da yin jaje ga Manzon Allah ya da Iyalansa da kuma taya murnar ranar haihuwar wannan gwarzon Shahidi, malamin ya bayyana cewa duk da dai taron maulidi ne na haihuwarsa amma kuma a lokaci guda za mu tuna da ranar shahadarsa shi da 'Yan uwansa da sauran Shahidai gaba ɗaya.

Shehin malamin ya yi nasiha ga mahalarta taron da su dage da neman ilimi da kuma ƙara kusantar Allah, kuma ya yi kiran ga Yan uwa da mu so junanmu mu tausaya wa juna,mu guji yaɗa jita-jita, Sheikh Abdulhameed ya yi albishir da cewa tabbatas sai Abuja ta zama cibiyar wannan gwagwarmayar da Sheikh Zakzaky ke ma jagoranci, kai ma ta zama. 

Daga karshe malamin ya yi addu'ar Allah ya sakawa waɗanda suke ci gaba da shirya irin wannan tarukan na tunawa da Shahidai albarka kuma da sake ƙarfafan Mahalarta taron da tsayuwa kyam a kan al'amarin addini, sannan ya yi addua ga Sheikh Ibraheem Zakzaky(H).

Daga karshe kuma aka gabatar da yanka "Cake" domin girmamawa ga Shaheed Sayyid Muhamud Ibraheem Zakzaky, sai aka yi adduar rufe taron.

Allah ya ƙarawa Sheikh Ibraheem Zakzaky(H) lafiya kuma ya gaggauta fitowarsa.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post