@MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
MAFI YAWAN WANDA SAQO YAZO MUSU SUNFI KIYAYEWA FIYE DA WADANDA SUKA JI
A yanayi ko babin abinda yafi dacewa bai kamata ace wanda labarin gaskiya ya iso masa ace ya fi wanda yaji gaskiyar da kunnensa daga bakin wanda ya fadeta ba. Sai dai kuma haka lamarin yake, domin wasu zamanzu da mutanen kirki bai amfanar dasu komai ba sai hasara.
Kowa na iya fahintar haka cikin sauqi idan yaji qissar matar Annabi Nuhu da matar Annabi Lud (A. S), da kuma qissar wadanda suka zauna da Manzon Allah (S. A. W. W) suka ji daga gare shi amma basu aikata ba, sai kuma wadanda suka ji labarin abinda ya faru cikin littafai suka kiyaye tare da aikatawa sau da qasa.
To, Annabi (S. A. W. W) na farin ciki tare da yin fatan alkhairi ga wadanda suka saurari abinda ya fada kuma suka isarwa wadanda basa nan, wannan kuma shine riqe amana . Domin ta hanyar rubuta gaskiya cikin rubutun magabata yasa muka san gaskiyar abinda Annabi (S. A. W. W) ya fada ko yayi wasicci wadanda wasu suka yi watsi dashi a bayan bayansu.
👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇
239- حدثنا محمد بن بشار حدثنا يحيى بن سعيد القطان- أملاه علينا- حدثنا قرة بن خالد حدثنا محمد بن سيرين عن عبد الرحمن بن أبي بكرة عن أبيه وعن رجل آخر هو أفضل في نفسي من عبد الرحمن عن أبي بكرة قال خطب رسول الله صلى الله عليه وسلم يوم النحر فقال: ((ليبلغ الشاهد الغائب فإنه رب مبلغ يبلغه أوعى له من سامع)).
Muhammad Bn Bashar ya bamu labari, Yahya Bn Sa'eed Al-Qudniy ya bamu labari, Qarratu Bn Khaleed ya bamu labari, Muhammad Bn Sireena ya bamu labari daga Abdurrahman Bn Abiy Bakrata, daga babansa daga wani mutum na dabam wanda yafi falala fiye dani, daga Abdurrahman daga Abiy Bakrata yace; " manzon Allah (S. A. W. W) yayi Khudba a ranar suka (NAHRIN), sai yace;
" WANDA KE NAN YA ISARWA WANDA BAI NAN GURIN, DOMIN SHI MAFI YAWAN WANDA AKA ISARWA YA ISO MASA YA FI KIYAYE SHI (abinda aka isar masa) FIYE DA WANDA YAJI (da kunnensa). "
240- حدثنا أبو بكر بن أبي شيبة حدثنا أبو أسامة (ح) وحدثنا إسحاق بن منصور أنبأنا النضر بن شميل عن بهز بن حكيم عن أبيه عن جده معاوية القشيري قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: ((ألا ليبلغ الشاهد الغائب)).
Abu Bakrata Bn Shaibata ya bamu labari, baban Usamata ya bamu labari, kuma Ishaq Bn Mansur ya bamu labari, Nadri Bn Shumail ya bamu labari daga Bahazu Bn Hakeem, daga babansa daga kakansa Mu'awiyata Al-Qushairiy yace; Manzon Allah (S. A. W. W) yace;
" KU SAURARA ! WANDA KE NAN YA ISARWA WANDA BAI NAN. "
241- حدثنا أحمد بن عبدة أنبأنا عبد العزيز بن محمد الدراوردي حدثني قدامة بن موسى عن محمد بن الحصين التميمي عن أبي علقمة مولى ابن عباس عن يسار مولى ابن عمر عن ابن عمر أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: ((ليبلغ شاهدكم غائبكم)).
Ahmad Bn Ubadata ya bamu labari, Abdul-Azeez Bn Muhammad Al-Daraawaradiy ya bamu labari, Qudamatu Bn Musa ya bamu labari daga Muhammad Bn Hussain Al-Tamimiy, daga baban Alqamata bararren bawan Ibn Abbas, daga Yasaari bararren bawan Ibn Umar, daga Ibn Umar cewa, lalle Manzon Allah (S. A. W. W) yace;
" WANDA KE NAN DAGA CIKINKU YA ISARWA WANDA BAI NAN DAGA CIKINKU. "
(IBN MAJAH, KITABUL-ILMI, BABUN MAN BALAGA ILMAN)
Duk wannan gargadi da Manzon Allah (S. A. W. W) yayi ta yi yayi ne kan Khudubarsa ta Ghadeer wanda ya nasabta Imam Ali (A. S) a matsayin Khalifah bayansa, shine ya riqa jaddada musu cewa lalle su isar da wannan saqo zuwa ga wadanda basu ji (irin mu) domin yawancin wadanda saqo yaje musu sunfi kiyayewa fiye da wadanda suka ji da kunnensu.
Kuma hakan ne ya tabbata, domin su mafi yawan wadanda suka ji sunyi watsi da abinda suka ji daga gare shi (S. A. W. W). Mu kuma wadanda saqon ya iso mana ta hanyar rubutun marubuta masu amana sai muka kiyaye fiye da wadanda suka ji.
To, kamar haka ake so dukkan wani mabiyin Sayyid Zakzaky (H) ya kasance mai sauraron gaskiya da kunne basira kuma ya isarwa wadanda basu ji ba, domin zai iya yiwuwa wadanda saqo zai isa gare su sufi kiyayewa fiye da ku masu ji, wataqila kiyayewar wadanda kuka isarwa ya amfanar daku ko ta hanyar yi muku addu'a ne, domin ta sanadinku gaskiya tazo musu.
YAA ALLAH KA BAMU IKON KIYAYE DUKKAN ABINDA YAZO MANA NA GASKIYA !
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.
(08137925034)
21st May, 2021/ 10th Shawwal, 1442.