Abunda Aka yi Zariya Ko A Lokacin Fir'auna Ba'ayi Shi ba!! _Inji Malamin Darikar Tijjaniya A Shinkafi



"ABINDA AKA YI A ZARIA KO A LOKACIN FIR'AUNA BA A YI SHI BA" Inji Malam Bala(Ala) Shinkafi a jawabinsa a yayin ziyarar Barka da Sallah da Dandaalin Matasa Almajiran Shaikh Zakzaky na Shinkafi suka kai mashi.

_______________________________

fatimaboutique.fh@gmail.com

________________________________


A ci gaba da ziyarar Barka da Sallah da Dandalin Matasa Almajiran Shaikh Ibraheem Ya'aqoub Zakzaky (H) suke gabatarwa ga Malaman garin Shinkafi a lokuttan Sallah,yau ziyarar ta isa a zawiyyar Shaikh Bala Fegen gara.


A ziyarar Malamin ya godewa matasan bisa kyakyawar kulawarsu a kansa da ziyarorin da suke kawo mashi a irin wadannan lokutta.


Malam Bala (Baba Ala) Babban Malami ne a garin Shinkafi Dan Darikar Tijjaniyah,Wanda yake daya daga cikin masu tausayawa Wannan Harka da Sayyeed Zakzaky ke jagoranta.


Shehin Malamin yayi tsokaci akan halin da aka saka Shaikh Zakzaky,inda ya ce "A tarihi abinda aka yiwa Shaikh Zakzaky da Almajiransa ko lokacin Fir'auna ba ayi hakan ba,a saboda haka tunda hakan ta kasance nasan

 wallahi Allah ba zai zura ido ba!"


Shaikh Bala ya kara da cewa "Nasan wannan aiki da aka yi akwai abubuwan da zasu faru,domin ba zai taba yuyuwaba a yi wannan aika-aika kasa ta zauna lafiya.


Daga karshe Malamin ya yi addu'a ta musamman ga jagoran Wannan Harka Shaikh Ibraheem Ya'aqoub Zakzaky (H) ya roki Allah da ya kubutar da shi,ya yi mashi mafita ya kuma isar mashi ga wadanda ke ci gaba da zaluntarsa.





Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post