Zainab Bnt Jahashin na alfaharin aurenta da Annabi (S.A.W.W) a kan sauran matansa !!!


 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


SAYYIDAH KHADIJA (S. A) KADAI AKA YIWA BUSHARA DA GIDAN ALJANNAH 


A daidai lokacin da kowacce mace ke fahari da matsayinta a wajen mijinta sai ya zamana ana samun wasu daga waje ma su taimakawa wata wajen nema mata matsayi ko falala. 


Duk matar da ke gani tana da wani matsayi ta kanyi amfani da wannan matsayi nata don ta nuna cewa ta fi kowacce mace matsayi wajen mijinsu. 


Ummul-muminina Zainab Bnt Jahshin ita ce matar Manzon Allah (S. A. W. W) ta 7 wacce ya aure ta a shekara ta 4 ko 5 bayan Hijra bisa sadaqi Dirhami 400 bayan sakin da Zaid Bn Haarithata yayi mata .


Manzon Allah (S. A. W. W) ya aure ta tana 'yar shekara 35 bisa umarnin Allah (S. W. A). Wannan dalili yasa take yin fahari cikin sauran matansa (S. A. W. W). 


Ya zo cikin riwaya cewa; 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


(7420)- حدثنا أحمد: حدثنا محمد بن أبي بكر المقدمي: حدثنا حمَّاد بن زيد، عن ثابت، عن أنس قال: 

جاء زيد بن حارثة يشكو، فجعل النبي صلى الله عليه وسلم يقول: (اتق الله، وأمسك عليك زوجك) قال فكانت زينب تفخر على أزواج النبي صلى الله عليه وسلم تقول: زوَّجكنَّ أهاليكنَّ، وزوجني الله تعالى من فوق سبع سماوات 

وعن ثابت: "وتخفي في نفسك ما الله مبديه وتخشى الناس" نزلت في شأن زينب وزيد بن حارثة ."


Ahmad ya bamu labari, Muhammad Bn Abubakar Al-Maqdamiy ya bamu labari, Hammad Bin Zaid ya bamu labari daga Thabit, daga Anas yace :


Zaid Bn Harith ya zo yana kokawa, sai Annabi (S. A. W. W) yake cewa; 


" KAJI TSORON ALLAH KUMA KA RIQE MATARKA " Yace, Zainab ta kasance tana alfahari cikin matan Annabi (S. A. W. W) tana cewa; 


" Iyalanku ne suka aurar da ku, ni kuma Allah (T) ne ya aurar dani daga saman bakwai kuma aka tabbatar dashi (a doron qasa). "


" KUMA KANA BOYEWA CIKIN ZUCIYARKA KUMA ALLAH YANA BAYYANAR DASHI, KUMA KANA TSORON MUTANE.... "


Ta sauka ne kan sha'anin Zainab da Zaid Bn Haarithata. 


(KITABUL-TAUHID, BABI NA 22, HADISI NA 7420)


Kuma maganar gaskiya abinda Ummul-muminina Zainab ta fada gaskiya ne kuma abin alfahari ace auranka yazo ne da umarnin Allah kai tsaye daga sama.


Wannan magana kuwa ta yi shi ne bayan wafatin Nana Khadijah (S. A), domin Annabi (S. A. W. W) bai auri wata mace ba har sai bayan wafatinta (S. A). Sannan kuma ba a sami wata wacce ta ja da ita kan wannan alfahari nata ba. 


Ita kuwa Sayyidah Khadijah (S. A) ita ce matar Manzon Allah (S. A. W. W) ta farko wacce ya aure ta shekar goma sha biyar (15) kafin aiko shi a matsayin Manzo bisa sadaqi na Uqiya goma sha biyu da rabi 12.5 na daga Zinari. 


Ita ce mace guda (1) wacce akayi mata albishir da gidan Aljannah cikin matan Manzon Allah (S. A. W. W) .


Riwaya ta zo daga Ummul-muminina A'isha kamar haka; 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


(3816)- حدثنا سعيد بن عفير: حدثنا الليث قال: كتب إلي هشام، عن أبيه، عن عائشة رضي الله عنها قالت: 

ما غرت على امرأة للنبي صلى الله عليه وسلم ما غرت على خديجة، هلكت قبل أن يتزوجني، لما كنت أسمعه يذكرها، وأمره الله أن يبشرها ببيت من قصب، وإن كان ليذبح الشاة فيهدي في خلائلها منها ما يسعهن 


Sa'ad Bn Ufair ya bamu labari, Laithee ya bamu labari yace; An rubuta zuwa ga Hishaam, daga babansa, daga A'ishatu (R. A) tace; 


" Ban taba yin kashi ga wata daga matan Annabi (S. A. W. W) ba, amma nayi kishi akan Khadijah. Ta halaka tun ma kafin ya aure ni, amma yayin da naji shi (S. A. W. W) yana ambatonta kuma Allah ya umarce shi da yayi mata bushara da wani gida na beni (Upstairs) sai naji kishinta ya kamani har nake yi mata hassada). 


Sannan kuma ya kasance in ya yanka Akuya ya kanyi kyauta zuwa ga qawayenta (saboda tsananin Soyayyarsa gare ta) gwargwadon abinda zai wadace su. "


(SAHIHUL-BUKHARI, HADISI NA 3816)


Tabbas wadannan matsayi guda biyu abin alfahari ne, ace umarnin aurenki ya zo ne daga sama ko kuma ace Allah ya aiko miki da busharar Aljannah tun daga duniya. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.


        (08137925034)


10th April, 2021/ 28th Sha'aban, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post