GABATARWA
Yunkuri don sauya Fikira ko kuma tunanin da wata Gwagwarmaya (Mass movements) ta doru akansa daga masu mulkin da ake tunkara, ba sabon abu bane a tarihin Yan Gwagwarmaya a fadin duniya. Tarihi ya hakikance sau da yawa Matakin Qarfi bashi yafi bada natija wajen rushe Gwagwarmayoyi ba, amma batun sanya rudu da wargaza tunanin masu rajin kawo sauyi, shine aikin da aka fi dogara dashi don tunbuke dashen da aka gino mutane akan shi.
Kamar yadda wani Masanin Tarihi akan yadda ake Narkar da Gwagwarmayoyi (Neutralization of Mass Movements) ya ambata:
_….‘Ta wannan hanya ne ake iya sanya musu shakku akan ginshikin Imanin su, a mantar dasu hakikanin hanyar da suka biyo, kuma ina suka nufa. Cikin sauki zaa iya bugun Zuciyarsu (Center point) ba tare da sun harzuka ba, a kuma samu damar sanyawa su zamto basu iya bada ayyukansu (responsibilities) sai ya zamto suna raunana daga inda suka fi Karfi, Kuma rushewarsu ta dauko daga tsakiyar su. Nasara akan haka tana samuwa cikin aiki na tsawon lokaci ba da sauri ba, cikin Salo na qwarewa da kula da Natijoji daga Tarihi.’_
Fahimtar wannan yaki na bayan fage ga Masu yunkuri na kawo sauyi ya zamo wajibi, iyakar yadda aka fahimci shirin Makiya a wannan fage, da yadda aka shirya don tunkarar su, shine ma’aunin fata (hope) na Zahiri ga wadannan masu Yunkurin, kuma shine tsawon ajalin wannan Fahimta daga Mutuwa.
*FIKIRAR HARKA DA YUNKURIN MAQIYA*
Harkar Musulunci da Sheikh Zakzaky (H) yake Jagoranta, muna iya cewa tafi fuskantar barazana daga Makiya ta wannan fage fiye da ma’aunin Amfani da Makami.
Harkar da aka faro a Karshen Saba’inoni (1970s) a cikin wani Muhalli na Fikira (Ideological Sphere) ta fara da nau’in mutanen da ya zamo suna iya bambance aya da tsakuwa. Tun daga fahimtar Hadafin ta, irin gudunmuwar da zasu bayar a tare da Fahimtar motsin Makiya ta bayan fage.
Harkar ta kasance cikin tsarin dauki dai, dai, da kuma Kokari wajen fadada tunanin ma’abotanta (Tarurrukan Kwakwkwafa tunani da fikira) sai ya zamo duk da Karancin mabiya a farkonta, amma tasirinsu a Al’umma yana da matuqar yawa… A bayyane yake a Zahiri Fikirar tana cigaba a tare da zama hadari ga masu tsoron hadafinta.
Amma Shigowarta cikin Sauran Muhallai, sai ta cakudu da mutane da yawa masu mabambantan tunani, duk da akwai yunkuri na fadada tunanin masu shigowa… sai yaci karo da Matsalolin da suka ginu akan raayoyin wasu a hade da Yunkurin Jahiliyya na bayan fage wanda tuni suka fara.
Fitintunun Zuhudu, darqawiyya, zaman jagwam na daga Matsalolin Farko da harka din ta fuskanta wadanda suka ginu akan Kokarin wasu na maida harka din ta tafi akan tunanukansu sabanin hadafin da aka gina tafiyar akai.
Amma fitinar tawayiyya na ta al’amarin daban ne, domin tsirowar ta da yaduwarta da dukkan Tasirin da tayi ga Harkar Musulunci ya ginu akan aikin da jahiliyya ta gino na rusa fikirar Harkar ta bayan fage.
A dukkan lokacin da za’a yi duba akan wannan fage, Jawabin Jagora Sheikh Zakzaky (H) na Fitina Tawayiyya da yayi a lokacin da tasirin shirin Makiya ya fara yawa madubi ne da za’a fahimci Zubi da tsarin yadda suka gino aikin nasu da abubuwan da suke fatan samu a kusa da nesa (akan wannan harka).
Kokarin bayyana harka din a matsayin Mazhaba, a tunanin al’ummar dake kewaye da Harka din da kuma ‘yan cikinta, Rusa Karfin Jagorancin Harka din zuwa ga Jagorori da yawa (Samuwar Kwamitin Shura, da Sauye Sauyen da ya samu a tarihin Harka), Samar da gamayyar masu taimaka musu kai tsaye ta cikin Harka wajen dakile cigaban Harka (Infiltration).
*“Akwai wadanda aka tsara su zasu fara fita, su kuma ragowar suka ce, kuje idan kun janye Mutane sai mu biyo bayanku, idan kuma mutane basu bar shi (Sheikh Zakzaky) ba, mu zamu zauna sai mun rusa komai!”* wannan Furuci shine zanen aikin da jahiliyya da gamin gambizar mataimakansu na ciki suka doru akai. Akan shi dukkan Yaki na bayan fage ya ginu, kuma shine Ma’aunin gane irin tasirin da suka samu da kuma aikin dake gaban masu yiwa harkar da hadafinta kyakykyawan fata.
*TASIRIN YUNQURIN ‘NARKARWA’ GA HARKA*
Masana da yawa sun nuna Fikirar gwagwarmaya ta ‘yan Juyin Juya hali tana tafiya akan Turaku uku (3) ne LEADERSHIP (Jagoranci), PROCESS (Hanya) da kuma HOPE (fata), sune abubuwan da suke gina Imani ga Mabiya, su sanya musu Kishin taimakon tafiyar (Feels of responsibility), da kuma jin yiwuwar samun Nasara gare su da al’umma gabadaya.
Idan zamu kalli wadannan abubuwa a fasalin yadda aka gino su a Harka, da kuma irin ayyukan da jahiliyya ta dauka tana yi don rusa ginin da ake akai dogon bahasi ne da zai bude shafi mai girma na Karatuttuka (wanda muna fatan irin wannan takardun da Jawabai da zaa dunga yi don fahimtar da ‘yan uwa akan wannan yaki su zama sun yawaita).
*JAGORANCIN* harka an gino shi akan tsarin Jagorancin Malami akan al’umma ne, Malami da ya zama a aikace ya zama Magajin Annabi (S), irin wannan Jagora mabiyansa zasu kasance suna da cikakken Imani (Wilaya) dashi akan duniyarsu da lahirar su, kuma tunanin sa shine Mashayar Fikirar harka din, kuma akan Mahangar sa za’a dauki dukkan mataki akan abubuwan da zasu bijiro a tafiyar, Samfuri a tarihi shine Sheikh Usman bn fodiye (TR) da Imam Ruhullah Musawi Khomeini (KS). Wani abu ya tabi wannan Jagorancin (Cutarwa a Zahiri ne, ko kuma Yunkurin katange wannan matsayin da darajar) sannan ya zama akwai yarda ko kuma halin ko-in-kula daga Mabiya yana alamta tasirin Yakin Makiya na bayan fage.
*HANYAr* da zaa bi kuwa ita ce wadda Jagoran ya zaba, Jagoran Harkar Musulunci cikin Irshadodinsa ya ambata hanyar da zaa bi don Juyin Musulunci zai zamo bata da bambanci da na Manzo (S), don saukake fahimta ya ambace ta da irin tafarkin Imam Hussein (AS), a aikace don fahimtar wannan al’umma ya suffata aikin da zaa yi irin na Shehu dan fodiye (TR) ne, sannan a fikirance da zubi na wannan zamani ya ambaci gwagwarmayar da yake yi irin ta Imam Khomeini (KS) ce. Don haka ga dukkan masu gudanar da al’amura da tafiyar da ayyuka dole ya zama tarihin Musulunci daga wannan Mahanga ya zama shine hanyar samun Matsaya, a tare da duba tasirin biyayya ga Jagora da akasin haka. A takaice yanzu dukkan wani tunani da kake iya gani a cikin Harka da yake shiryarwa ya zuwa wani tafarki day a sabawa wannan zubi da Jagora (H) ya yiwa harka kana iya aje shi cikin ayyukan Yakin bayan fage da jahiliyya ta samu nasarar gabatar dashi.
*FATA* shine abunda yake cigabantar da tafiyar da Mabiya akan tafarki duk tsanani da muzgunawar da zasu fuskanta daga Makiya, haka nan shine abunda yake matso da al’umma zuwa ga tafarkin da wannan gwagwarmayar take tafiya akai. Wannan harka din an yi mata gini mai kyau na Zahiri a tsare tsaren ayyukanta. Misalin fata akan Shahada ga Mabiyi (Bayan kyakykyawan fata na lahira) shine ya zamo da kyakykyawan fatan bayansa ba zata wulakanta ba, idan Marayun Al’umma da raunanan su ya zama a cikin tsarin ayyukan Gwagwarmaya rayuwarsu ke samun nutsuwa, al’ummar gabadaya zata iya sallamawa Gwagwarmayar addini a matsayin hanyar da zasu iya tseratar da kansu daga Zaluncin jahiliyya da ya baibaye su. Fahimtar ayyukan da harkar ta tsara su a *HANYAr* da take kai shine zai fitar maka da hakikanin fatan Nasara da zai shiga zukatan mabiya da ma al’ummar dake kewaye da harkar gabadaya. Amma idan ka dubi tarihin Harkar kaga cigaban wadannan ayyukan yayi kasa, ko kuma an rushe tubalin ginin wasu ayyukan ma, to abun lura anan, sai ka kalle shi a fuskar wani yunkurin jahiliyya na yakin bayan fage.
*KAMMALAWA*
Harka da 'yan Harka a yanzu suna cikin yanayin da yake kewaye da tasirin Makiya, musamman akan ayyukansu Na Yakin bayan fage.Hare haren da Jahiliyya suka dauka don Kawar da Jagoran Harka tun daga 2009 hade da Yunkurin Jahiliyya Na harin Kwaf daya (Wanda suka faro daga 2014-2015) yana nuna mana yadda suka samu nutsuwa ne da ayyukan Ma'aikatansu Na Yakin bayan fage.
Yanayin da Muke ciki a yanzu, Na motsin da basu tsammata ba a bayan wadannan waqi'o'i ya samu ne daga Yunqurin Gwarzon Shahidi, Sayyid Ahmad Zakzaky, Wanda yayi Kokarin farkar da 'yan uwa musamman matasa akan halin da Jahiliyya ta jefa harkar nan a ciki. Cigaba da samun masu turjiya har yanzu, fage ne da aka Samar dashi a lokacin da Makiya suke hangen Nasara kusa.
Aikin da yake gabanmu ba ya takaitu akan Turjiya ga Azzalumai a wannan marhala bane kadai, fahimtar iyakokin da suka tsara yakin su na bayan fage, hade da gano tasiri da nasarorin da suka samu a lokaci guda da shirya ma ayyukan juyar da nasarorin da suke ganin sun samu shine abunda zai rayar da Jihadin kare wannan Fikira, Wanda basu sanya wajen yunkurin kawar da duk Wanda ya tsayu akai.
_An karanta a Taron Mauludin Abulfadl Abbas (AS) wanda Mu'assasatu Abulfadl Abbas, suka gudanar A Abuja_
Laraba, 5 ga Sha'aban 1440H