@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
AZUMI GARKUWA CE GA MAI YINSA
Ita sadaqa aba ce mai girman matsayi wajen Allah kuma mai daukaka darajar mai yinta. A duk lokacin da mutum yayi sadaqa abubuwa uku za su bayyana a lokacin.
Na farko shine, ya aikata umarnin Allah kuma zai sami lada na wanda yabi umarnin Allah.
Na biyu :- Zai ji dadi cikin zuciyarsa kuma zai sami daukaka wajen wanda ya bawa sadaqar.
Na uku :- Ya faranta zuciyar wanda ya bawa , kuma zai sami lada wajen Allah domin alqawarinsa ne cewa zai faranta zuciyar dukkan wanda ya faranta zuciyar wani, musamman ma mumini.
Shi kuwa azumi yana taqaita ne tsakanin mai yinsa da Mahalicinsa, wato ba za a sami wadannan abubuwa uku wadanda ake samu cikin yin sadaqa ba.
Ya zo cikin riwaya kamar haka;
👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇
بصائر الدرجات ابْنُ عِيسَى عَنْ مُحَمَّدٍ الْبَرْقِيِّ عَنْ إِبْرَاهِيمَ بْنِ إِسْحَاقَ عَنْ أَبِي عُثْمَانَ الْعَبْدِيِّ عَنْ جَعْفَرٍ عَنْ أَبِيهِ عَنْ عَلِيٍّ ع قَالَ قَالَ رَسُولُ اللَّهِ ص قِرَاءَةُ الْقُرْآنِ فِي الصَّلَاةِ أَفْضَلُ مِنْ قِرَاءَةِ الْقُرْآنِ فِي غَيْرِ الصَّلَاةِ وَ ذِكْرُ اللَّهِ أَفْضَلُ مِنَ الصَّدَقَةِ وَ الصَّدَقَةُ أَفْضَلُ مِنَ الصَّوْمِ وَ الصَّوْمُ جُنَّةٌ[27
بصائر الدرجات: 11 في ط و 4 في ط.
Ya zo cikin (BASA'IRUL-DARAJAT) na Ibn Isah, daga Muhammad Al-Barqi, daga Ibrahim Bn Ishaq, daga baban Usmana Al-Abdiy, daga Ja'afar daga babansa daga Aliyu (A. S) yace; Manzon Allah (S. A. W. W) yace;
" YIN KARATUN ALQUR'ANI CIKIN SALLAH YA FI FALALA FIYE DA YIN KARATU BA A CIKIN SALLAH BA. SHI KUMA AMBATON ALLAH YA FI FALALA FIYE DA SADAQA. ITA KUMA SADAQA TA FI FALALA FIYE DA YIN AZUMI, SHI KUWA AZUMI GARKUWA CE ."
Dangane da girman sadaqa kawai an sami wata riwaya kamar haka;
👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇
الخصال الْخَلِيلُ عَنْ مُحَمَّدِ بْنِ إِبْرَاهِيمَ الدُّبَيْلِيِّ عَنْ أَبِي عَبْدِ اللَّهِ عَنْ سُفْيَانَ عَنِ الزُّهْرِيِّ عَنْ سَالِمٍ عَنْ أَبِيهِ قَالَ قَالَ رَسُولُ اللَّهِ ص لَا حَسَدَ إِلَّا فِي اثْنَتَيْنِ رَجُلٍ آتَاهُ اللَّهُ مَالًا فَهُوَ يُنْفِقُ مِنْهُ آنَاءَ اللَّيْلِ وَ آنَاءَ النَّهَارِ وَ رَجُلٍ آتَاهُ الْقُرْآنَ فَهُوَ يَقُومُ بِهِ آنَاءَ اللَّيْلِ وَ آنَاءَ النَّهَارِ[49].
الخصال ج 1 ص 66.
Daga Muhammad Bn Ibrahim Ad-Dubailiy, daga baban Abdullahi, daga Sufyan, daga Zuhriy, daga Saleem, daga babansa yace; Manzon Allah (S. A. W. W) yace;
" BABU YIN HASSADA FACE CIKIN ABUBUWA BIYU.
(1)- MUTUMIN DA ALLAH YA BASHI DUKIYA KUMA YANA CIYAR DA ITA CIKIN DARE DA YINI.
(2)- DA MUTUMIN DA ALLAH YA BASHI ALQUR'ANI KUMA YANA KARANTA SHI CIKIN DARE DA YINI. "
Yin hassada cikin abubuwa biyun nan shine, mutum yayi buri ko kuma yace ina ma ace shine Allah ya bashi wadannan abubuwa domin ya nemi kusancin Allah dasu?
To, shi wannan mutumi mai irin wannan hassada ba shi da laifi wajen Allah. Amma kuma da ace yana yi musu hassadar ne don cewa sun fishi ba wai don yana yin don ya sami abinda zai nemi yardar Allah dasu ba, to, da kuma yayi hasara. Domin ita hassada tana cinye kyawawan ayyukan mutum ne kamar yadda wuta ke cin qirare (fire wood) ."
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.
(08137925034)
26TH APRIL, 2021
Allha yasaka da alkairi
ReplyDelete