Yin Imani da Allah da kuma biyayya ga ManzonSa (S.A.W.W) har zuwa mutuwa shine fifikon Imani !



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

ZA KA IYA IMANI A WANNAN ZAMANI KAFI WASU DA SUKA RAYU A QARNIN FARKO 

Bisa irin tsantsar imani da sallamawa wanda wasu daga cikin Sahabban Annabi (S. A. W. W) suka yi ba zai taba yiwuwa wani wanda zaiyi imani da kuma irin nasu aikin ya kai su a matsayi ba. Wanda ya rigaye ka a aiki kuma ya dore a kansa zuwa mutuwa ba zai taba zama daidai da wanda yazo a wannan zamani ba .


Sai dai kuma akwai wata magana da ake kawowa wai cewa duk aikin da kayi a yanzu ba za ka kai wadanda suka yi a qarnin farko ba. Ana kafa hujja ne da wannan hadisi dake biye; 


👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇


(3650) - حدثنا إسحاق: حدثنا النضر: أخبرنا شعبة، عن أبي جمرة: سمعت زهدم بن مضرب: سمعت عمران بن حصين رضي الله عنهما يقول: 

قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: (خير أمتي قرني، ثم الذين يلونهم، ثم الذين يلونهم - قال عمران: فلا أدري أذكر بعد قرنه قرنين أو ثلاثا - ثم إن بعدكم قوما يشهدون ولا يستشهدون، ويخونون ولا يؤتمنون، وينذرون ولا يوفون، ويظهر فيهم السمن) 


Ishaq ya bamu labari, Nadhr ya bamu labari, Shu'ubata ya bamu labari daga baban Kamarta : Ya ji Zuhdamu Bn Mudhrabu, ya ji Imrana Bn Hussain (R. A) yana cewa; Manzon Allah (S. A. W. W) yace :


" MAFI ALKHAIRIN AL'UMMATA ITA CE QARNINA, SA'AN NAN WADANDA SUKA BIYO SU, SA'AN NAN WADANDA SUKA BIYO SU. "


Imrana yace; " Ban sani ba ko qarni biyu ko uku ya ambata a bayan qarninsa. 


" SA'AN NAN BAYANKU ZA A SAMI WASU MUTANE SUNA SHAIDAWA AMMA BA SA BAYAR DA SHAIDA (kan abinda suka sani), SUNA HA'INCI KUMA BA SU DA AMANA, KUMA SUNA ALQAWURA AMMA BA SA CIKAWA, SANNAN KITSE (fat) ZAI BAYYANA GARE SU (za suyi qiba saboda cin haram) ."


(KITABUL FADHA'ILUS-SAHABA )


Idan muka nazarci wannan hadisi za muga cewa yana nuna mana gwargwadon kusancin zamanin da Annabi (S. A. W. W) ya rayu shine fifikon mutane ba wai matsayin imaninsu da ayyukansu ba. Idan kuma aka tafi a haka ya zama cewa komai munin aikin mutum matuqar dai ya rayu da Annabi (S. A. W. W) ba za ka kai shi a matsayi ba komai aikinka. 


Sai dai kuma wannan hadisi ya ci karo da wasu hadisai da za mu kawo su kamar haka :-


👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇


رواه الحسن بن عرفة العبدي حدثنا إسماعيل بن عياش الحمصي عن المغيرة بن قيس التميمي عن عمرو بن شعيب عن أبيه عن جده قال قال رسول الله صلى الله عليه وسلم أي الخلق أعجب إليكم إيمانا قالوا الملائكة قال وما لهم لا يؤمنون وهم عند ربهم قالوا فالنبيون قال وما لهم لا يؤمنونوالوحي ينزل عليهم قالوا فنحن قال وما لكم لا تؤمنون وأنا بين أظهركم قال فقال رسول الله صلى الله عليه وسلم ألا إن أعجب الخلق إلي إيمانا لقوم يكونون من بعدكم يجدون صحفا فيها كتاب يؤمنون بما فيها.


(1)- Hassan Bn Arfata Al-Abdiy ya riwaito cewa, Isma'il ya Bn Iyash Al-Hamsiy ya bamu labari daga Mugirata Bn Qais Al-Taimiy, daga Amruu Bn Shu'aib, daga babansa daga kakansa yace, Manzon Allah (S. A. W. W) Yace; 


" WACCE HALITTA CE (daga cikin halittun Allah) IMANINTA YAFI BAKU MAMAKI ?" 


Suka ce; " MALA'IKU ." Yace; 


" SU KUWA MENENE ZAI HANA SU YIN IMANI ALHALI SUNA TARE DA UBANGIJINSU ?" Suka ce; 


" TO, ANNABAWA . " Yace; 


" SU KUWA MENENE ZAI HANA SU YIN IMANI ALHALI WAHAYI NA SAUKA A KANSU ?" Suka ce; 


" TO, MUNE (Sahabbai). " Yace; 


" KU KUMA MENENE ZAI HANA KU YIN IMANI ALHALI INA NAN A TSAKANINKU (kuna ji kuma kuna gani daga gare ni). " 


(Amruu Bn Shu'aib) Yace, sai Manzon Allah (S. A. W. W) yace; 


" HALITTUN DA IMANINSU YAFI BADA MAMAKI SUNE MUTANEN DA ZA SUZO A BAYANKU, ZA SU SAMI WANI LITTAFI CIKINSA AKWAI RUBUTU (Alqur'ani), SUNA IMANI DA ABINDA KE CIKINSA (ba tare da sunga wanda yazo da littafin ba) ."


(MUSNAD-AHMAD, J:4, SH:106)



قال أبو بكر بن مردويه في تفسيره حدثنا عبد الله بن جعفر حدثنا إسماعيل عن عبد الله بن مسعود حدثنا عبد الله بن صالح حدثنا معاوية بن صالح عن صالح بن جبير قال قدم علينا أبو جمعة الأنصاري صاحب رسول الله صلى الله عليه وسلم ببيت المقدس يصلي فيه ومعنا يومئذ رجاء بن حيوة رضي الله عنه فلما انصرف خرجنا نشيعه فلما أراد الإنصراف قال إن لكم جائزة وحقا أحدثكم بحديث سمعته من رسول الله صلى الله عليه وسلم قلنا هات رحمك الله قال كنا مع رسول الله صلى الله عليه وسلم ومعنا معاذ بن جبل عاشر عشرة فقلنا يا رسول الله هل من قوم أعظم منا أجرا آمنا بالله واتبعناك قال ما يمنعكم من ذلك ورسول الله بين أظهركم يأتيكم بالوحي من السماء بل قوم بعدكم يأتيهم كتاب من بين لوحين يؤمنون به ويعملون بما فيه أولئك أعظم منكم أجرا ."


(2)- Abubakar Bn Mardawihi ya fada ciki Tafsirinsa, Abdullahi Bn Ja'afar ya bamu labari, Isma'il ya bamu labari daga Abdullahi Bn Mas'ud, Kuma Abdullahi Bn Salih ya bamu labari, Mu'awiyata Bn Salih ya bamu labari daga Salih Bn Jubair yace : Baban Jam'ata Al-Ansariy Sahabin Manzon Allah (S. A. W. W) ya zo gare mu a Baitil-Maqdis yana sallah cikinsa, kuma tare damu a wannan rana akwai Raja'a Bn Haiwata (R. A). 


Yayin da ya fito (daga sallah) sai muka fito muna yi masa rakiya. Yayin da yayi niyyar tafiya sai; 


" Lalle gare ku kuna da wani matsayi da kuma haqqi, zan baku labari da wani hadisi wanda naji shi daga Manzon Allah (S. A. W. W) ."


Sai muka ce, ka fada mana Allah yayi maka rahma. Yace; 


" Mun kasance tare da Manzon Allah (S. A. W. W) kuma tare damu akwai Mu'azu Bn Jabal daya daga cikin mutane goma (wadanda aka yi musu bushara da Aljannah). Sai muka ce; 


 " Yaa Ma'aikin Allah (S. A. W. W) ! Shin, akwai daga cikin mutane wadanda suka fi mu girman lada ? Munyi imani da Allah kuma mun bi ka? " Yace; 


" TO, MENENE KUWA ZAI HANE KU DAGA HAKA ALHALI MANZON ALLAH NA TSAKANINKU YANA ZUWA MUKU DA WAHAYI DAGA SAMA? EH, JAMA'A CE A BAYANKU, LITTAFI ZAI ZO MUSU DAGA TSAKANIN LAUHI BIYU (Lauhil-Mahfuuz), ZA SUYI IMANI DASHI KUMA ZA SUYI AIKI DA ABINDA KE CIKINSA, WADANNAN SUNE MAFIFITANKU A LADA ."



حدثنا أبو المغيرة أخبرنا الأوزاعي حدثني أسيد بن عبد الرحمن عن خالد بن دريك عن ابن محيريز قال قلت لأبي جمعة حدثنا حديثا سمعته من رسول الله صلى الله عليه وسلم قال نعم أحدثك حديث جيدا تغدينا مع رسول الله صلى الله عليه وسلم ومعنا أبو عبيدة بن الجراح فقال يا رسول الله هل أحد خير منا أسلمنا معك وجاهدنا معك قال نعم قوم من بعدكم يؤمنون بي ولم يروني .



(3)- Baban Mugeerata ya bamu labari, Auza'iy ya bamu labari, Usaid Bn Abdurrahman ya bamu labari daga Khaleed Bn Dareek, daga Ibn Muhairizy yace; " Na cewa baban Ja'afar , ka bamu wani labari mana wanda ka ji shi daga Manzon Allah (S. A. W. W). Yace;


" Na'am, zan baka labari kuwa mai kyau, mun yi sammako tare da Manzon Allah (S. A. W. W) kuma tare damu akwai Ubaidata Bn Jarraaha, sai yace; Yaa Ma'aikin Allah, shin, akwai wani kuwa wanda ya fi mu alkhairi ? Mun sallama tare da kai, sannan kuma munyi jihadi tare da kai ." Yace; 


" HAKANE, WASU JAMA'AH CE A BAYANKU, ZA SUYI IMANI DANI BA TARE DA SUN GANNI BA ."


(MAJMA'UZ-ZAWAA'ID, J:10, SH:65)


Wannan ta cikin hadisai ukun nan kuwa sun zo daidai da ayar nan dake cewa; 


👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇


" ٱلَّذِينَ يُؤۡمِنُونَ بِٱلۡغَيۡبِ ........ ( ٣)


" SUYI WADANDA SUKA YI IMANI DA GHAIBU....... 


(SURATUL-BAQARATI :3)


Ashe kuwa wanda yayi imani da abinda bai gani ba zai fi zama abin mamaki fiye da wanda yaga abu (physically). 


Saboda haka abin ba wai batun farko ko qarshe bane, a'a, tsananin imani da sallamawa ne kadai ke daukaka darajar mutum wajen Allah. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.


        (08137925034)


       17TH APRIL, 2021.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post