Hadiyar Ramadan na Buhunan kayan Abinci daga Sheikh Zakzaky sun nufi sansanin ƴan Gudun Hijira .
In ba a manta a satin da ya gabata ne dai shehin malamin ya raba kayan abincin azumi a garin Zaria. Wannan kuma ba sabon abu bane ga shehin don kamar kullum , duk shekara sai yayi wannan aikin lada duk da yau shekaru biyar yana tsare qarqashin Azzalumar hukumar Najeriya.