Yan Uwa Masu Daraja !!!




Akan fadawa wanda akeso  da kauna, kuma ba'a son bacin ransa kuskure ne cikin wasa da dariya, bawai cikin bacin rai da zafin zuciya ba, hakan zaya saka cikin wasa da dariyan da nishadi ku warware dukkan matsalan dake damunku.


 Idan matsala ta faru tsakaninmu, kuma munaso mu warware hakan cikin sauki ba tare da kara samarwa da kanmu wata matsalan ba, to lallai muna bukatar tattaunawa ne a tsakani, sannan bawai tattaunawa ta fada da nuna bacin rai ba, cikin hikima,ana wasa ana dariya zamu kawo matsalan kuma mu tattaunata mu samar da mafita.


 Dayawan mutane basa bukatar lokacin da aka Bata masu rai ayi kokarin rarrasansu a lokacin, sunfi so a Bari sai sun huce sannan a fahintar dasu ko a basu hakuri, kaso mafi rinjaye na matan mu na hausawa, hada wannan matsalan yake damun zaman auren su, bata san ya zata bawa mijinta hakuri ba, batasan wane lokaci ya kamata ta bashi hakuri ba, batasan lokacin da yake bukatar tattaunawa akan muhimman abubuwa ba, Bata san yadda zata shawo kansa idan yana cikin damuwa ba, dama ire iren wannan da daman gaske.


Sanin waye mijin ko waye zaki aura, da sanin irin Yanayin abubuwan dayake so da wa'yanda baya so, da lokutan da yake bukatar hakan da wa'yanda baya bukata, yana taimakawa sosai a rayuwarku ne, karki kuskura ki nuna bacin ranki a lokacin da ran mijinki ya baci, kiyi kokarin danne ranki da tausan zuciyar ki, ki Bari sai idan ya sauko kinyi masa bayani, sannan saiki nuna masa ranki ya baci akan abinda ya faru din, yin fushinku a tare lokaci guda, yana iya haifar da matsalan da ba'a tunani domin zcy batada kashi.


Sannan, kuma maza ya kamata ku rika nuna tausayawa a garemu, muma mutane ne irinku, ranmu yana baci, muna shiga damuwa, amma da yawan lokuta mukan kauda Kaine don kar ranku ya Kara baci, wallahi tallahi dayawan mata suna jure bacin rai da rashin daidai mazajensu akansu, saboda samawa mazajen maslaha,sukan duba maslahan mijinsu akan nasu, amma bance ba'a samun akasin hakan ba, tabbas ana samu duka daga mazan da muka matan.

 

Hakuri a kowane lokaci da kauda kai gami da fahintar juna shine yake zama jagora wurin tafiyar da ma'amalar mu, uwa uba idan akwai so da kauna da tausayawa.


Allah ka bamu ikon jure dukkan kurakuran mazajen mu da abokanan zamanmu, ka bamu ikon yi musu uziri da kuma jin uzirinsu. Nagode taku har kullum


✍️_ Zarah A Zamsarf

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post