@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UUPDATED @
KOWA DA INDA YAFI QOQARI A WANNAN HARKA
Da gaskine kowa da inda yafi qoqari wajen bada irin tasa gudumowa cikin wannan harka ta gwagwarmaya wacce Sayyid Ibrahim El-zakzaky (H) ke yiwa jagoranci.
Wasu sunfi qoqari wajen rubutu wanda kowa yasan tasirin rubutu wajen isar da saqo ko ma wanne iri ne . Rubutu kan iya isar da saqo fiye da yadda mutum ke tsammani, domin ko a zamanin Manzon Allah (A. A. W. W) yayi amfani da salon rubutu wajen aika saqonni zuwa manyan Sarakuna na wasu qasashe dauke da muryar kiransu zuwa muslimci.
Akwai kuma masu addu'o'i ba dare ba rana wajen ganin anyi nasara wajen isar da abinda ake son isarwa, ko kuma samun nasara cikin abinda aka sa gaba. Za mu iya fahintar hakan musamman cikin irin addu'o'in da Annabi (S. A. W. W) ke yi na neman nasara ko tabbata a guraren yaqoqi daban-dabam.
Mawaqa ma da irin nasu tasiri sosai wajen bayyanar da manufar abinda suke kai tare da nuna zalunci ko danne haqqin da ake yi musu. Za mu iya fahintar hakan idan mun shiga cikin tarihi, domin an sami mawaqa masu bawa Annabi (S. A. W. W) kariya tare da maida martani kan wadanda ke yin waqoqi don cin zarafinsa (S. A. W. W).
Su kuwa aikin malamai ba za mu iya cewa ga iya adadin gudumowar da suke bayarwa ba, domin cikin ayyukan nasu akwai bayyanar da manufar kiran Sayyid Zakzaky (H) tare da charging din dukkan wani bangare na harka wajen dagewa kan abinda za su iya ko suke yi, domin komai na son qarfafawa da irshadi.
Idan muka dawo kan 'yan Abuja Struggle za mu iya cewa ayyukansu ba abu ne mai sauqi wanda baki zai iya furta shi ba, domin ya tattara mafi girman abubuwa masu daraja ko qima (value) a rayuwar dan Adam.
Ayyuka ne da suka hada sadaukar da :-
RAI,
DUKIYA da kuma
LOKACI .
Cikin fafutuka na kowanne irin abu ne idan babu wadannan abubuwa uku ba za a taba samun cin nasara ba . Su kuwa 'yan Abuja Struggle sun hada dukkan wadannan abubuwa, domin kowanne na cikin wannan tafiya tasu .
A tarihin wannan qasa tamu bamu taba jin an sami wata al'umma ko jama'a masu fafutukar wani 'yanci nasu na wani abu da aka ce sun shafe shekaru shida (6) suna yi ana kashe su ana jikkata su ana daure su amma ace a kullum al'amarinsu sai dada cigaba yake yi ba.
Saboda haka akwai buqatar a qara taimaka musu da addu'a da dukiya da kuma yabo tare da qarfafarsu ta kowacce fuska wajen wannan aiki wanda zai zababbun mutane kadai ke iya dakewa da jajurcewa .
YAA ALLAH KA TAIMAKI DUKKAN WANDA KE BADA GUDUMOWA TA KOWACCE FUSKA WAJEN GANIN SAYYID (H) YAYI #FREE 👏🏼👏🏼👏🏼
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.
(08137925034)
28th April, 2021/ 16th Ramadan, 1442.