Wayyo! Mafi Yawa Mahaukatan Samari ne ke Addabar 'Yan Uwa Mata a Social Media !!!

 


Mata yawancin su mazan aure suke nema, shiyasa duk wanda ya musu magana sai su ďauke shi serious. Kuma suna ganin social media ne zai basu daman zaban irin namijin da suke so. Abu mai wuya ka ga namijin da yake neman mace da aure a social media. Yawanci suna yi ne kawai don su samu budurwar da zasu rinƙa hira da ita in suna oline, amma ƙarin aure ko yin auren baya cikin agendan su.


Mata ku fahimta! Ban ce kada ki so wani ba, zaki iya jin kina son wani saboda abubuwan da kika gani na addini, ko kuďi dss. Amma ina so ki sani randa kuka yi ido biyu ranar ne zaki tantance so ne ko hauka. Domin zaki iya ganin banbance-banbance da yawa waɗanda ma baki yi tunaninnu ba. Zaki iya ganinsa a social websites mutum mai tsafta da kamala. Amma in kika haɗu da shi sai ki ji yana wari kuma bashi da nutsuwa ko wasu abubuwa da baki so a wurin ɗa namiji. Kin ga a hoto ko a video duk ba zaki san waɗannan ba. Wani ma ki ga komai nashi karya ne har abubuwan da yake posting a zahiri duk babu su.


Ki Lura da kyau Dakyau a Wuni Zaki Samu Sallamar (Message) Samari 30 a Acount dinki , Amma Duk Acikin su 5 ne Kawai kuke Mutunci saura Duk Sonki Sukeyi, Anya Dagaske Son Gaskiya Ne Wannan???


Muhadu a Rubutu na Gaba Mu Tantance Gaskiya da Karyar Mayaudaran Banza...!!


@Mas'udu Dan Masani Shinkafi 08149993999


Mai Alkalamin Tone-Tone Amma na Gaskiya, 



Barka Da Shan Ruwa

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post