Wankan janaba na ɗauke alwala ga wanda zai yi Sallah !


 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


GA WANDA SALLAH KADAI ZAI YI YAKE YIN ALWALA 


Bambancin fahinta ce kawai dake cikin karantarwa makarantu biyu, wato mabiya karantarwar Sahabbai da masu aiki da karantarwa Ahlul-Bait (A. S) wadanda suka tsotso karantarwar mahaifinsu Manzo Muhammad (S. A. W. W). 


Hukuncin da Sunnah (makarantar Sahabbai) suka fitar shine, idan mutum ya tashi yin wankan Janaba dole yayi alwala cikinsa. Sai dai bambancin da suke kawowa shine an bada zabi (option) wajen yin alwalar cikin wanka ko kuma jinkirta da alwalar zuwa qarshen wankan. 


Amma dai qa'ida ce cikin wankan sai anyi alwala, domin har sun kawo yin hakan na daga cikin sunnonin wanka. 


A karantarwa ta Ahlul-Bait (A. S) kuwa wankan Janaba na dauke alwala. Duk wanda ya kasance yana da janaba kuma yana son yin sallah, to, abinda ya hau kansa kawai shine wanka. Idan mutum yayi wanka babu wata buqatar yin alwala domin sallah. Wannan hukunci kuwa shine wanda yazo cikin Alqur'ani mai tsarki kamar haka; 


👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇


" يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِذَا قُمۡتُمۡ إِلَى ٱلصَّلَوٰةِ فَٱغۡسِلُواْ وُجُوهَكُمۡ وَأَيۡدِيَكُمۡ إِلَى ٱلۡمَرَافِقِ وَٱمۡسَحُواْ بِرُءُوسِكُمۡ وَأَرۡجُلَكُمۡ إِلَى ٱلۡكَعۡبَيۡنِۚ وَإِن كُنتُمۡ جُنُبٗا فَٱطَّهَّرُواْۚ.........(6)


" YAA KU WADANDA SUKA YI IMANI ! IDAN KUKA TASHI ZUWA GA SALLAH KU WANKE FUSKOKINKU DA HANNAYENKU ZUWA GWIWAR HANNU, KUMA KU SHAFI SASHEN KANKU DA KUMA QAFAFUNKU ZUWA KA'ABOBI BIYU (wannan tudu dake kan qafafu biyu). IDAN KUWA KUN KASANCE MASU JANABA, TO, KUYI TSAKI (wanka).... "


      (SURATUL-MA'IDA:6)


Hukuncin da ya tabbata anan shine, idan mutum na da Janaba wanka kawai zai yi sai ya gabatar da dukkan wasu ayyuka na ibada da yake son aikatawa. Wato babu batun alwala cikinsa, wankan nasa kadai ya wadatar masa da komai. 


Wannan fahinta kuwa ita tazo daidai da abinda Ummul-muminina A'isha ta kawo cikin wani hadisi kamar haka; 


👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇


23832- حَدَّثَنَا أَسْوَدُ بْنُ عَامِرٍ ، قَالَ : حَدَّثَنَا شَرِيكٌ ، عَنْ أَبِي إِسْحَاقَ ، عَنِ الْأَسْوَدِ ، عَنْ عَائِشَةَ ، قَالَت : " كَانَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ لَا يَتَوَضَّأُ بَعْدَ الْغُسْلِ " .


Aswadu Bn Ameer ya bamu labari yace : Shariku ya bamu labari daga baban Ishaqa, daga Aswadi, daga A'ishata tace; 


" MANZON ALLAH (S. A. W. W) YA KASANCE BA YA YIN ALWALA BAYAN WANKA ."


(MUSNAD-AHMAD, HADISI MAI LAMBA :23,832)


Kunga anan wannan karantarwa ta Ahlul-Bait (A. S) ita tazo daidai da karantarwar Manzon Allah (S. A. W. W) a aikace. 


Saboda haka wankan Janaba na dauke yin alwala, idan kayi wanka shikenan babu batun wata alwala sai dai a gabatar da ayyukan ibada (sallah) in anyi nufin hakan. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.


       (08137925034)


     18TH APRIL, 2021

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post