@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
BAMU SAN IRIN DARUSAN DA KUKE NUNAWA ARNA NA DAGA ANNABINMU BA
Ga shi dai Allah ya kawo mu cikin watan Ramadan mai alfarma wanda aka yi mana umarnin azumtarsa baki daya, kuma aka sanar damu abubuwan da za muyi su inganta mana shi, da wadanda idan mun aikata su za su bata mana shi (azumin).
Yana daga cikin abinda Allah ya haramta mana aikata shi cikin azumi shine RUNGUMAR MACE, wannan aiki haramun ne ga mai azumi ya aikata su a halin azumi, amma babu laifi ya aikata shi cikin dare yayin da ba azumi a bakinsu baki daya.
Allah (T) na fada mana cikin Qur'ani;
أُحِلَّ لَكُمۡ لَيۡلَةَ ٱلصِّيَامِ ٱلرَّفَثُ إِلَىٰ نِسَآئِكُمۡۚ هُنَّ لِبَاسٞ لَّكُمۡ وَأَنتُمۡ لِبَاسٞ لَّهُنَّۗ عَلِمَ ٱللَّهُ أَنَّكُمۡ كُنتُمۡ تَخۡتَانُونَ أَنفُسَكُمۡ فَتَابَ عَلَيۡكُمۡ وَعَفَا عَنكُمۡۖ فَٱلۡـَٰٔنَ بَٰشِرُوهُنَّ وَٱبۡتَغُواْ مَا كَتَبَ ٱللَّهُ لَكُمۡۚ وَكُلُواْ وَٱشۡرَبُواْ حَتَّىٰ يَتَبَيَّنَ لَكُمُ ٱلۡخَيۡطُ ٱلۡأَبۡيَضُ مِنَ ٱلۡخَيۡطِ ٱلۡأَسۡوَدِ مِنَ ٱلۡفَجۡرِۖ ثُمَّ أَتِمُّواْ ٱلصِّيَامَ إِلَى ٱلَّيۡلِۚ.....
" AN HALARTA MUKU CIKIN DAREN AZUMI DA KU RUNGUMI MATAYENKU (amma banda cikin rana). SU SUTURA CE GARE KU , KU MA SUTURA CE GARE SU. ALLAH NA SANIN CEWA KU KUN KASANCE KUNA HA'INTAR KAWUKANKU, TO, ALLAH YA KARBI TUBANKU KUMA YA YAFE MUKU. TO, YANZU KU RUNGUME SU (cikin dare 🌃 ) KU NEMI ABINDA ALLAH YA RUBUTA MUKU. KUMA KU CI KU SHA (cikin daren) HAR SAI FARIN ZARE YA BAYYANA MUKU DAGA BAQIN ZARE NA DAGA ALFIJR, SA'AN NAN KU CIKA AZUMINKU ZUWA DARE..... "
(SURATUL-BAQARATA, AYA TA 187)
Wannan shine umarnin Allah da dokokinsa, amma sai ya kasance an kawo cikin littafan sunnah suna nuna cewa Annabi (S. A. W. W) me saba wannan umarni na Allah ne, domin shi yana aikatawa da rana ☀ !
Ga dai riwayoyin nan kamar haka;
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
وقالت عائشة رضي الله عنها:
يحرم عليه فرجها
A'isha tace; " An haramta masa farjinta ."
(1927) - حدثنا سليمان بن حرب قال: عن شعبة، عن الحكم، عن إبراهيم، عن الأسود، عن عائشة رضي الله عنها قالت:
كان النبي صلى الله عليه وسلم يقبل ويباشر وهو صائم، وكان أملككم لإربه
وقال: قال ابن عباس: "مآرب" حاجات قال طاوس: "غير أولي الإربة" الأحمق لا حاجة له في النساء
Sulaiman ya bamu Bn Harb ya labari yace, Daga Shu'ubata, daga Hakaam, daga Ibrahim, daga Aswaad, daga A'isha (R. A) tace;
" Annabi (S. A. W. W) ya kasance yana sumba (kiss) kuma yana runguma alhali yana azumi. Shi ya kasance ya mallaki sha'awarsa. "
Yace, Ibn Abbas yace; " MA'AARIB " (yana nufin) BUQATA . "
'Dawus kuma yace; " Wanda ba ya sha'awa. " Wato wanda ba shi da buqata ga mace.
(BUKHARI, KITABUS-SIYAAM, BABIN RUNGUMA GAME AZUMI, HADISI MAI LAMBA 1927)
Hujjarsu anan ita ce wai Shi Annabi (S. A. W. W) ba ya sha'awar mace shi yasa yake rungumarsu a halin azumi.
TAMBAYA
(1)- Yanzu wannan magana taku ba za tasa wani yace ai shima ko ya rungumi mace ba abinda zai yi? Saboda haka shi ma zai iya yin koyi da shi ?
(2)- Aje ma Shi (S. A. W. W) ba ya sha'awa, amma menene fa'idar yin haka ga matan nasa ? Yana yi don ya tayar musu da sha'awa ce ko yaya ?
(3)- Ko su matan akwai inda aka ce su basu da wata sha'awa ko da an rungume su ? Idan kuwa haka suke sun zama daidai da Annabi (S. A. W. W).
(1928)- حدثنا محمد بن المثنى: حدثنا يحيى، عن هشام قال: أخبرني أبي، عن عائشة، عن النبي صلى الله عليه وسلم (ح) إن كان رسول الله صلى الله عليه وسلم ليقبل بعض أزواجه وهو صائم، ثم ضحكت
Muhammad Bn Musannah ya bamu labari, Yahya ya bamu labari daga Hishaam yace; babana ya bani labari daga A'ishata, daga Annabi (S. A. W. W) cewa;
" LALLE MANZON ALLAH (S. A. W. W) YA KASANCE YANA SUMBAR (kiss) SASHEN MATAYENSA ALHALI YANA AZUMI ."
Sa'an nan tayi dariya (in ji baban Hishaam).
(BABIN YIN SUMBA (kiss) GA MAI AZUMI, HADISI NA 1928)
Idan har wannan maganar gaskiya ce menene kuma abin dariya a cikinta har tayi dariya ?
Yanzu ba ta tunanin wani zai iya daukar wannan magana a matsayin abin wasa ko izgilanci ?
Ga wata riwayar ma wacce tazo cikin Musnad-Ahmad, amma ba za mu fassarata ba tunda maganar iri daya ce data sama.
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
23603- حَدَّثَنَا أَبُو مُعَاوِيَةَ ، حَدَّثَنَا الْأَعْمَشُ ، عَنْ إِبْرَاهِيمَ ، عَنْ عَلْقَمَةَ ، وَالْأَسْوَدِ ، عَنْ عَائِشَةَ ، قَالَت : " كَانَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يُقَبِّلُ وَهُوَ صَائِمٌ ، وَيُبَاشِرُ وَهُوَ صَائِمٌ ، وَلَكِنَّهُ كَانَ أَمْلَكَكُمْ لِإِرْبِهِ " .
(MUSNAD AHMAD, HADISI MAI LAMBA 23,603)
KUN QARYATA KANKU DA KANKU
Kunce wai shi (S. A. W. W) ba ya sha'awar mata ne shi yasa yake sumbatarsu da rungumarsu, amma kuma cikin wannan hadisi na qasa kuka ce yana sha'awa.
Ga maganar taku dai kamar haka;
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
حدثنا عمرو بن علي حدثنا عبد الأعلى حدثنا هشام بن أبي عبد الله عن أبي الزبير عن جابر أن رسول الله صلى الله عليه وسلم رأى امرأة فأتى امرأته زينب وهي تمعس منيئة لها فقضى حاجته ثم خرج إلى أصحابه فقال ان المرأة تقبل في صورة شيطان وتدبر في صورة شيطان فإذا أبصر أحدكم امرأة فليأت أهله فإن ذلك يرد ما في نفسه
Amruu Bn Aliyu ya bamu labari, Abdul-A'alah ya bamu labari, Hishaam Bn Abiy Abdullahi ya bamu labari daga Zubair, daga Jabir cewa;
" Lalle Manzon Allah (S. A. W. W) yaga wata mata (wacce ta ba shi sha'awa), sai ya jewa matarsa Zainab alhali tana jiman fatarta (he was so busy in her leather work) , ya biya buqatarsa sannan ya fito zuwa ga Sahabbansa yace;
" LALLE ITA MACE TAKAN FUSKANTO NE DA SIFFAR SHAIDAN KUMA TA JUYA CIKIN SIFFAR SHAIDAN. IDAN 'DAYANKU YA HANGI MACE (har ta bashi sha'awa), TO, YA JEWA MATARSA, DOMIN YIN HAKAN SHI ZAI KAWAR DA ABINDA KE CIKIN ZUCIYARSA ."
Wani hadisin kuma kuka ce;
وحدثني سلمة بن شبيب حدثنا الحسن بن أعين حدثنا معقل عن أبي الزبير قال قال جابر سمعت النبي صلى الله عليه وسلم يقول إذا أحدكم أعجبته المرأة فوقعت في قلبه فليعمد إلى امرأته فليواقعها فإن ذلك يرد ما في نفسه
Sulaiman Bn Shubaib ya bamu labari, Hassan Bn U'aini ya bamu labari, Ma'aqaal ya bamu labari daga baban Zubair yace; Jabir yace, ya ji Annabi (S. A. W. W) yana cewa;
" IDAN 'DAYANKU MACE TA BASHI SHA'AWA HAR YAJI (sha'awar ta kama shi) CIKIN ZUCIYARSA, TO, YA JEWA MATARSA YA AFKA MATA, DOMIN YIN HAKAN SHI ZAI KAWAR DA ABINDA KE CIKIN ZUCIYARSA (na sha'awar) ."
(SAHIHUL-MUSLIM, KITABUN-NIKAH, BABIN WANDA YAGA MACE TA BA SHI SHA'AWAH YA JEWA MATARSA YA BIYA BUQATARSA)
Yanzu dan Allah idan kun hada hadisan farko dake nuna cewa Shi ba ya sha'awar mata ne yasa yake runguma da sumbatarsu, sannan kuma anan kuka kawo cewa yaga mace har ta bashi sha'awa, ya mai hankali zai kalle ku ?
Ba ya sha'awa/yana sha'awa, wannene gaskiya cikinsu ?
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.
(08137925034)
15TH APRIL, 2021