Tun Harin Da Buhari ya Kai Wa Malam Zakzaky (h) Rayukan Mutanen Nigeria Suka Rasa Kima Da Daraja...!!!



... Umar Hassan Gololo... 

Kisan dabbanci, kisan kiyashi, mugunta da rashin imani da aka yiwa Mutanen da basu dauke da makami a Hussainiyya Bakiyyatullah, Darur-Rahma da Gidan Malam Zakzaky(H) dake Gyallesu Zaria ya bude kofar zubar da jinin al'ummar Nigeria musamman Arewa. 

Officially Gwamnatin Buhari karkashin jagorancin General Buratai ta bada umurni aka kashe Mata masu ciki, aka kashe jarirai, aka kashe, Samari Mahaddata Qur'ani, Daliban Sakandare da Sauran Manyan Makarantu da primary, aka kashe Malaman addini da na Jami'a, kisa na wulakanci da dabbanci. 

Bayan an yi Wannan ta'addancin Gwamnatin Kaduna karkashin El-rufa'i ta bada umurni aka rusa kabarin Mahaifiyar Malam Zakzaky(H), aka rusa Fudiyya Islamic center da Gidan Malam Zakzaky(H), bayan ya bada umurnin binne mutane 347 a rami daya maza da mata, yara da manya ba wanka ballantana Sallah.

Wannan ta'addancin da Gwamnatin Buhari ta yi ya budewa mahara kofar zubar da jinin al'ummar Arewa, zai yi wahalar gaske gari ya waye baka ji an kashe Mutane a Niger ko Katsina ba, a Sokoto ko Zamfara ba, haka abin yake a kaduna. 

Gwamnatin Buhari ta bude mulkin Nigeria da zubar da jini kuma har yanzu shi ake yi, daga satar kudade sai shekar da jinanen mutane.. 

Muna rokon Allahu Ta'ala ya gaggauta daukar mana fansar zaluncin da Buhari yayi mana da Wanda yake cigaba da yi na cigaba da tsare Malam Zakzaky da Malama Zeenat duk da kotun Tarayyar Nigeria tace a sake su..

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post