@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
DON KADA ACE YA SABA SUNNAR ANNABI (S. A. W. W) YAKE SUMBANTAR HAJARUL-ASWAAD
Sanin kowa ne cewa Umar Bn Khaddab na daga cikin mafiya tsanani wajen shan giya, kashe 'ya'ya mata da kuma bautar Gumaka, amma ya muslimta bayan shekaru bakwai daga aiko Annabi Muhammad (S. A. W. W) a matsayin Manzo.
Shine wanda ya gaji Abubakar na hawa karagar mulkinsa bayan rayuwarsa, kuma yayi shekaru 12 yana kan wannan kujera.
An riwaito hadisai da dama masu magana kan falalarsa kan abubuwa daban-dabam, cikinsu akwai wannan hadisi dake cewa;
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
230- حَدَّثَنَا أَبُو مُعَاوِيَةَ ، حَدَّثَنَا عَاصِمٌ الْأَحْوَلُ ، عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ سَرْجِسَ ، قَالَ : رَأَيْتُ الْأُصَيْلِعَ يَعْنِي عُمَرَ يُقَبِّلُ الْحَجَرَ ، وَيَقُولُ : إِنِّي لَأُقَبِّلُكَ ، وَأَعْلَمُ أَنَّكَ حَجَرٌ لَا تَنْفَعُ وَلَا تَضُرُّ ، وَلَوْلَا أَنِّي رَأَيْتُ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يُقَبِّلُكَ ، لَمْ أُقَبِّلْكَ " .
Baban Mu'awiyata ya bamu labari, Aseem Al-Ahwaal ya bamu labari daga Abdullahi Bn Sarjisa yace; " Naga Usaili'a (yana nufin Umar) yana sumbatta Dutse yana cewa;
" NI FA (kawai) INA SUMBANTARKA NE ALHALI NA SAN KAI DUTSE NE (ba abin bauta ba), BA ZA KA AMFANAR BA (don an sumbanceka) KUMA BA ZA KA CUTAR BA (don anqi a sumbanceka). DA BA DON DAI NI NAGA MANZON ALLAH (S. A. W. W) NA SUMBANTARKA BA DA (wallahi) BA ZAN SUMBANCEKA BA (don kai ba komai bane) !"
(Musnad-Ahmad, kitabin falalar Khalifofi shiryayyu, babin falalar Umar Bn Khaddab, hadisi mai lamba 230).
DARASI
-----------------
(1)- Akwai wani dutse wanda Annabi (S. A. W. W) ke sumbantarsa wanda ya zama sunnah ga musulmi su sumbance shi in har sun same shi.
(2)- Umar ya gyamaci sumbantar wannan dutse don kada wasu su dauke shi abin bauta, amma ganin Annabi (S. A. W. W) na sumbantarsa yasa shi ma (Umar) ya sumbance shi, amma dai ya tabbatarwa dutsen cewa kada fa yaji wani abu cikin zuciyarsa na cewa bauta masa ake yi, a'a, kawai don anga Annabi (S. A. W. W) na yi ne.
(3)- Idan kaga wani babba yana aikata wani abu, to, kaima ka aikata shi kawai ko da ba kaga amfanin wannan abin ba don gudun kada ace ka bar aikin magabacinka.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.
(08137925037)
9th April, 2021/ 27th Sha'aban, 1442.