Shugaban majalisar koli ta gwamnatin rikon kwarya ta kasar Sudan
Abdel Fattah Al-Burhan ya bayyana cewa gwamnatin kasar Sudan tana
son fahintar juna tsakanin kasashen wadanda kogin Nilu ta ratsa a
kasashensu, su rattaba hannu kan yarjejeniya wacce zata lamuncewa
ko wace kasa kasonta na ruwan Nilu.
Jaridar Egypt Daily ta kasar Masar ta nakalto Al-Burhan yana fadar
haka a wata hira da ta hada shi da tashar talabijin ta Al-Arabiyya a
ranar jumma’an da ta gabata. Ya kuma kara da cewa, gwamnatin Sudan
tana bukatar Habasha ta janye sojojinta daga bangaren kasar Sudan da
take mamaye da su.
Banda haka Al-Buryan yayi magana kan wasu al-amura da suka shafi
kasarsa wadanda suka hada da rikicin madatsar ruwa ta Renaissance
ta kasar Habasha da rikikin yankin Darfur da kuma matsalolin tattalin
arziki wanda kasar take fama da su.
Source: BIN MUHAMMAD PRESS
WHATSAPP GROUP
08032147367