Shin Imam Aliy (as) Ne Kadai Mai Shiryarwa A Bayan Annabi (s) ???



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


SAYYID ZAKZAKY (H) NE MAI SHIRYAR DA WANNAN AL'UMMA DA MUKE CIKINTA


Alqawarin Allah ne cewa ba zai bar al'umma haka sakakai suyi ta rayuwa ba tare da mai shiryar dasu ba, wannan dalili yasa yake tayar da Annabawa da Manzanni (A. S) lokaci bayan lokaci. A daidai lokacin da Allah yayi nufin rufe Manzanci cikin bayinsa sai kuma ya sanya wasu bayi wadanda ba Annabawa suka zama shiryayyu don su zama masu shiryar da al'ummata da suke cikinta. 


Allah (S. W. A) na sanar da Manzonsa (S. A. W. W) cewa; 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼



وَيَقُولُ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ لَوۡلَآ أُنزِلَ عَلَيۡهِ ءَايَةٞ مِّن رَّبِّهِۦٓۗ إِنَّمَآ أَنتَ مُنذِرٞۖ وَلِكُلِّ قَوۡمٍ هَادٍ.( ٧)


" KUMA WADANDA SUKA KAFIRTA SUNA CEWA,  " DON MENENE BA A SAUKAR DA WATA AYA A KANSA BA  ? (To, ka fada musu cewa); " ABIN SANI KAI MAI GARGADI NE, KUMA CIKIN KOWACCE AL'UMMA AKWAI MAI SHIRYARWA  ."


        (SURATUL-RA'AD:7)


Anan ana sanar dashi ne cewa ya cigaba dai kawai da yin kiransa kan abinda aka umarce shi, sannan ake qara sanar dashi cewa ko da ya bar duniya  akwai mai shiryar da al'ummarsa bisa iznin Allah. 



Ya zo cikin Tafsir na 'Dabari kamar haka; 


:15313 - حدثنا أحمد بن يحيى الصوفي، قال: ثنا الحسن بن الحسين الأنصاري، قال: ثنا معاذ بن مسلم، ثنا الهروي، عن عطاء بن السائب، عن سعيد بن جبير، عن ابن عباس، قال: لما نزلت {إنما أنت منذر ولكل قوا هاد} وضع صلى الله عليه وسلم يده على صدره، فقال: "أنا المنذر ولكل قوم هاد " ، وأومأ بيده إلى منكب علي، فقال: "أنت الهادي يا علي، بك يهتدي المهتدون بعدي " .


Ahmad Bn Yahya As-Sufiy ya bamu labari yace, Hassan Bn Hussaini Al-Ansariy ya bamu labari yace: Mu'azu Bn Muslim ya bamu labari, Harwiy ya bamu labari daga Adda'i Bn Sa'ib ya bamu labari daga Sa'eed Bn Jubair, daga Ibn Abbas (R. A) yace; 


" Yayin da aka saukar, " ABIN SANI KAI MAI GARGADI NE, KUMA CIKIN KOWACCE AL'UMMA AKWAI MAI SHIRYARWA  ." Manzon Allah (S. A. W. W) ya dora hannunsa akan qirjinsa yace; 


" NINE MAI GARGADI, KUMA CIKIN KOWACCE JAMA'A (Al'umma) AKWAI MAI SHIRYARWA. " 


Sannan kuma ya miqa hannunsa zuwa kafadar (shoulder) Aliyu yace; 


" KAINE MAI SHIRYARWA YAA ALIYU, DAKAI NE MASU SHIRYUWA ZA SU SHIRYU A BAYANA  ."


      (TAFSIRUL-'DABARI)


Wannan shine ke qara tabbatar mana cewa Imam Ali (A. S) shine Khalifan Manzon Allah (S. A. W. W) na farko bayan wafatinsa (S. A. W. W). 


Kada ka rudu don ka ji ance Imam Ali ne mai shiryarwa a bayan Annabi (S. A. W. W) har kayi tambaya ko tuhuma cewa, in hakane yanzu ma shine mai shiryar damu alhali yayi wafati? 


Amsar da za mu baka anan ita ce, shiga cikin riwayoyin nan dake biye :-


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


(1)-    علل الشرائع أَبِي عَنْ سَعْدٍ عَنِ الْيَقْطِينِيِّ عَنْ مُحَمَّدِ بْنِ سِنَانٍ وَ صَفْوَانَ وَ ابْنِ الْمُغِيرَةِ وَ عَلِيِّ بْنِ النُّعْمَانِ كُلِّهِمْ عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ مُسْكَانَ عَنْ أَبِي بَصِيرٍ عَنْ أَبِي عَبْدِ اللَّهِ ع قَالَ: إِنَّ اللَّهَ لَا يَدَعُ الْأَرْضَ إِلَّا وَ فِيهَا عَالِمٌ يَعْلَمُ الزِّيَادَةَ وَ النُّقْصَانَ فَإِذَا زَادَ الْمُؤْمِنُونَ شَيْئاً رَدَّهُمْ وَ إِذَا نَقَصُوا أَكْمَلَهُ لَهُمْ فَقَالَ خُذُوهُ كَامِلًا وَ لَوْ لَا ذَلِكَ لَالْتَبَسَ عَلَى الْمُؤْمِنِينَ أَمْرُهُمْ وَ لَمْ يُفَرَّقْ بَيْنَ الْحَقِّ وَ الْبَاطِلِ‏


Yazo cikin Ilalus-Shara'i'i, daga Sa'eed daga Yaqdiniyyi, daga Muhammad Bn Sinaan da Safwan da Ibn Mugeerata da Aliyu Bn Nu'uman, kowannensu daga Abdullahi Bn Muskaan , daga baban Basir daga Abu Abdullahi (A. S) yace :


" LALLE ALLAH BA YA BARIN QASA FACE A CIKINTA AKWAI MASANI WANDA YAKE SANIN QARI DA RAGI (cikin addini). IDAN MUMINAI SUKA YI QARIN WANI ABU SAI YA DAWO DASU (kan daidai), IDAN KUMA SUKA RAGE SAI YA CIKA SHI GARE SU YACE;  " KU RIQE SHI CIKAKKE  ."


DA ACE BABU WANNAN TO, DA AL'AMRAN MUMINAI BAI DORE A KANSU BA, KUMA DA BA ZA A RARRABE GASKIYA DA QARYA BA  ."



 (2)-  علل الشرائع أَبِي عَنْ سَعْدٍ عَنِ الْخَشَّابِ عَنِ ابْنِ أَبِي نَجْرَانَ عَنْ عَبْدِ الْكَرِيمِ وَ غَيْرِهِ عَنْ أَبِي عَبْدِ اللَّهِ ع‏ أَنَّ جَبْرَئِيلَ نَزَلَ عَلَى مُحَمَّدٍ ص يُخْبِرُ عَنْ رَبِّهِ عَزَّ وَ جَلَّ فَقَالَ لَهُ يَا مُحَمَّدُ لَمْ أَتْرُكِ الْأَرْضَ إِلَّا وَ فِيهَا عَالِمٌ يَعْرِفُ طَاعَتِي وَ هُدَايَ وَ يَكُونُ نَجَاةً فِيمَا بَيْنَ قَبْضِ النَّبِيِّ إِلَى خُرُوجِ النَّبِيِّ الْآخَرِ وَ لَمْ أَكُنْ أَتْرُكُ إِبْلِيسَ يُضِلُّ النَّاسَ وَ لَيْسَ فِي الْأَرْضِ حُجَّةٌ وَ دَاعٍ إِلَيَّ وَ هَادٍ إِلَى سَبِيلِي وَ عَارِفٌ بِأَمْرِي وَ إِنِّي قَدْ قَضَيْتُ‏ لِكُلِّ قَوْمٍ هَادِياً أَهْدِي بِهِ السُّعَدَاءَ وَ يَكُونُ حُجَّةً عَلَى الْأَشْقِيَاءِ ."


علل الشرائع: 76.


Daga Sa'eed daga Kasshaab daga dan baban Najraan, daga Abdulkareem da ma waninsa, daga Abu Abdullahi (A. S) cewa; 


" LALLE JABRA'ILU YA SAUKO ZUWA GA MUHAMMAD (S. A. W. W) YANA BASHI LABARI DAGA UBANGIJINSA MAI GIRMA DA 'DAUKAKA YACE MASA;  " YAA MUHAMMAD  ! BA ZA ABAR QASA BA FACE A CIKINTA AKWAI MASANI YANA SANIN BIYAYYATA DA SHIRIYATA, KUMA YA KASANCE (biyayya gare shi) ITA CE TSIRA CIKIN TSAKANIN KARBAR RAN ANNABI ZUWA FITOWAR WANI ANNABIN NA DABAM. BAN KASANCE MAI BARIN IBLIS YA BATAR DA MUTANE BA BA TARE DA HUJJA (ta Allah) CIKIN QASA BA WANDA KE YIN KIRA ZUWA GARE NI KUMA MAI SHIRYARWA ZUWA TAFARKINA BA, KUMA MASANIN AL'AMRANA. KUMA LALLE NI HAQIQA NA HUKUNTA MAI SHIRYARWA GA KOWACCE AL'UMMA, DASHI NAKE SHIRYAR DA MASU RABAUTA, KUMA YA KASANCE HUJJA AKAN MARAR SA RABO ('yan asara)  ."



(ILALUL-SHARA'I'I:76)


Sannan kuma yazo cikin (Ikhmalud-Deen ) kamar haka, 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼



 إكمال الدين عَنِ الْحِمْيَرِيِّ عَنِ ابْنِ هَاشِمٍ عَنْ مُحَمَّدِ بْنِ حَفْصٍ عَنْ عَيْثَمِ بْنِ أَسْلَمَ‏ عَنْ ذَرِيحٍ الْمُحَارِبِيِّ عَنْ أَبِي عَبْدِ اللَّهِ ع قَالَ سَمِعْتُهُ يَقُولُ‏ وَ اللَّهِ مَا تَرَكَ اللَّهُ الْأَرْضَ‏ مُنْذُ قُبِضَ آدَمُ إِلَّا وَ فِيهَا إِمَامٌ يُهْتَدَى بِهِ إِلَى اللَّهِ عَزَّ وَ جَلَّ وَ هُوَ حُجَّةُ اللَّهِ عَزَّ وَ جَلَّ عَلَى الْعِبَادِ مَنْ تَرَكَهُ هَلَكَ وَ مَنْ لَزِمَهُ نَجَا حَقّاً عَلَى اللَّهِ عَزَّ وَ جَلَ‏.


 اكمال الدين: 127،


Daga Himyariyyi, daga Ibn Hishaam, daga Muhammad Bn Hafsi, daga Aithama Bn Aslaam, daga Zareehi Al-Muharibiy, daga Abu Abdullahi (A. S) yace; Na ji shi yana cewa; 


" WALLAHI ALLAH BAI TABA BARIN QASA BA TUN DA YA KARBI (ran) ADAM (A. S) FACE CIKINTA AKWAI IMAMI WANDA YAKE SHIRYARWA DASHI ZUWA GA ALLAH MAI GIRMA DA 'DAUKAKA, KUMA SHINE HUJJAR ALLAH MAI GIRMA DA 'DAUKAKA AKAN BAYI, DUK WANDA YA BARSHI YA HALAKA, KUMA WANDA YA LAZIMCE SHI YA TSIRA, WANNAN HAQQI NE AKAN ALLAH  MAI GIRMA DA 'DAUKAKA ."


     (IKHMAALUD-DEEN:127)



Saboda haka a daidai lokacin da ya zama babu Annabi ko Imami dole ya zama akwai wani shiryayye wanda Allah ke amfani dashi wajen shiryar da bayinsa. 


Sayyid Zakzaky (H) kuwa shine wannan shiryayye mai shiryar da wannan al'umma a daidai wannan zamani bisa iznin Allah. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼Ado Isah Guda. 


          (08137925034)


1st April, 2021/  19th Sha'aban, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post