- Faruq Sani Kudan
Ta yiwu mutum yace mana, to ai lallai dawo da addinin musulunci ba fa zai yiwu ba! Don akwai wanda suke ce min haka haka, ba fa zai yiwu ba sam, saboda an riga anyi nisa! Sai muce masa hatta har in haka nan ne kaga idan muka tsaya muka ce a koma ga Addinin gobe ƙiyama muna da uzuri za a ce me yasa kuka shantake a ƙasar da aka mayar da addinin musulunci tamkar laifi, kuka yi zaman ku.?
Sai muce ya (Rabbi,) a yayin da muka ga ana haka nan, munce ma mutane a dawo ga addini, amma sai basu saurare mu ba, sai suka fasa suka ƙiyi kuma munyi Sa'a ma sun kashe mu, sai muka yi shahada! To kaga mun samu mafita ballantana ma waye yace maka baza a iya komawa ga addini ba? Waye yace maka ba zai yiwu ba? Nan malam bahaushe yace da rashin kira karen Bebe ya ɓace shi bebe yana kallon kare yana ta tafiya, shi kuma bazai iya kiransa ba, har ya ɓace masa da ace zai iya kira ma'ana daya sameshi mai yiwa wa al'ummar nan data zama abin da ta zama ƙila don an ƙyale ta ne, da za a kira data dawo turba.
Waye yace maka Al'ummar nan baza ta iya dawowa addini ba? Mene ne naka na cewa 'Imposible' a wannan al'amarin? me ya mai she shi mustahili ai mu ƙasar nan, yazamu yi, ai akwai mu da waɗanda ba musulmi ba, turawa sunci mu da yaƙi kuma sun kawo wannan abu, gashi kuma sun fi mu ƙarfi, suna da kaza da kaza. haka zakaji suna cewa sai nace waye yace maka haka nan.?
Waye yace maka addini bazai dawo ba? Kwatanta wannan ƙasar da makka kafin bayyanar Annabi (S) wanda in ance '' LA ILAHA ILALLAH '' zasu zaro takobi su bi mutum a guje basu san ''LA ILAHA ILALLAH'' ba. Wanda suka ce ''aja'alal alihata ilahan wahida Inna haaza la'shai'un ujaab!'' Amma manzo nan yayi kira ga ''LA ILA HA ILLALLAH'', aka koma aka kafa tauhidi.
Wanne yafi wahala? A Nigeriya inda in kace kuma in da ba a san addinin ba, aka yi kira gare shi? To kunji maso min da'awar nan kenan.