@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
DA RASHIN KARBAR GASKIYA DAGA WANDA BA 'DAN AQIDARKU BA HUJJA CE, TO, DA YAHUDU SUN TSIRA WAJEN ALLAH
A daidai wannan lokaci muna cikin wani yanayi mai rikitarwa na fuskantar kamawar watan Ramadan, domin bin son zuciya ya zama shine addini ga wasu.
Bisa yadda tarihi yazo mana ance zamanin Manzon Allah (S. A. W. W) an sami Bayahude wanda ya sanar dashi ganin wata, kuma yayi umarni da a dau azumi ba tare da cewa wani musulmi ya gani ba. Malamai da yawa na kafa hujja da irin wannan qissa, sai dai kuma yanzu su ma sun fada cikin wadanda ake kafa musu Hujja.
Azumi watan Ramadan dai farilla ne kamar yadda Allah (T) ke cewa;
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ كُتِبَ عَلَيۡكُمُ ٱلصِّيَامُ كَمَا كُتِبَ عَلَى ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِكُمۡ لَعَلَّكُمۡ تَتَّقُونَ ٣٨١
" YAA KU WADANDA SUKA YI IMANI ! AN WAJABTA AZUMI A KANKU KAMAR YADDA AKA WAJABTA SHI KAN WADANDA KE GABANINKU KO ZA KU SAMI TAQAWA ."
To, shi kuma wannan azumi ba a kowanne lokaci ake yinsa ba kuma ba a kowanne yanayi ba, domin yana da lokaci tare da yanayin yinsa.
أَيَّامٗا مَّعۡدُودَٰتٖۚ فَمَن كَانَ مِنكُم مَّرِيضًا أَوۡ عَلَىٰ سَفَرٖ فَعِدَّةٞ مِّنۡ أَيَّامٍ أُخَرَۚ وَعَلَى ٱلَّذِينَ يُطِيقُونَهُۥ فِدۡيَةٞ طَعَامُ مِسۡكِينٖۖ فَمَن تَطَوَّعَ خَيۡرٗا فَهُوَ خَيۡرٞ لَّهُۥۚ وَأَن تَصُومُواْ خَيۡرٞ لَّكُمۡ إِن كُنتُمۡ تَعۡلَمُونَ ٤٨١
" WASU RANAKU NE QIDIDDIGAGGU. TO, WANDA YA KASANCE DAGA CIKINKU BA SHI DA LAFIYA KO KUMA YANA HALIN TAFIYA, SAI (ya ajiye azumin) YA RAMA SHI CIKIN WASU RANAKU NA DABAM (bayan qarewar watan). SU KUMA GA WADANDA (yin azumin) KE WAHALAR DASU SAI SUYI FANSA DA CIYAR DA ABINCI GA MISKINAI. WANDA YAYI TADAWWI'I (ya qara wani abu kan hakan) BISA KYAUTATAWA HAKAN ALKHAIRI NE GARE SHI. DA KUMA (za ku daure) KUYI AZUMI (cikin wahalar tasa) HAKAN SHI YAFI ALKHAIRI GARE KU IN DA KUN KASANCE KUMA SANI. "
Wannan kuwa na nuna mana ne cewa wannan kwanakin suna cikin farkon kamawar watan Ramadan ne zuwa qarshensa. Da za ka dauka kafin ya kama ka qare a cikinsa ko kuma sai ka shiga wasu kwanaki cikinsa ka qare a waninsa, to, da ka fada cikin fushin Allah.
Sannan kuma yanayin yin nasa shine ya zama kana halin lafiya ba jinyar da ba za ta barka kayi ba, ko kuma ba a halin tafiya kake ba.
Da ace wata zai kama sai kuma yanayi na tafiya ya bijiro maka a lokacin, to, wajibi ne ka ajiye azumin naka ka rama shi daga baya bisa umarnin Allah (T).
Sannan Allah ya cigaba da cewa;
شَهۡرُ رَمَضَانَ ٱلَّذِيٓ أُنزِلَ فِيهِ ٱلۡقُرۡءَانُ هُدٗى لِّلنَّاسِ وَبَيِّنَٰتٖ مِّنَ ٱلۡهُدَىٰ وَٱلۡفُرۡقَانِۚ فَمَن شَهِدَ مِنكُمُ ٱلشَّهۡرَ فَلۡيَصُمۡهُۖ....... ٥٨١
" WATAN AZUMI WANDA AKA SAUKAR DA ALQUR'ANI A CIKINSA SHIRIYA CE GA MUTANE DA KUMA BAYYANARWA DAGA SHIRIYA DA KUMA RARRABEWA. WANDA YA HALARTA DAGA CIKINKU YA AZUMCE SHI........ "
(SURATUL-BAQARATI :183-185)
Wannan na nuna mana ne cewa dole sai watan ya kama kafin a fara azumtarsa.
Tabbatuwar kamawarsa kuwa shine ya zamana an ga jinjirin wata ko kuma cikar kwana 30 na watan Sha'aban. Idan labarin ganin wata ya iso gare ka ya zama wajibi a kanka kayi azumi a ranar farko, idan kuma labari bai zo maka da wuri ba har sai bayan daukewar gari, to, abinda ya hau kanka shine ka kame bakinka daga ci da sha tunda ba a riga anyi niyya ba, sannan ka rama shi daga baya.
Ba zai taba zama hujja gare ka a wajen Allah ba kace wai labarin ganin watan ba daga bakin wanda ke cikin qungiyarku yazo ba. Wannan tunani naka yayi kama dana Yahudawa da suka qi gaskata Annabi (S. A. W. W) kawai wai don ba daga cikin qabilarsu ya fito ba.
Sun sanshi cikin littafansu, amma don ya fito daga cikin larabawa sai suka qaryata shi. Buqatarsu ita ce da daga cikinsu Yahudawa ya fito.
Kunga wannan hujja ta Yahudawa ba za ta kubutar dasu wajen Allah ba ranar alqiyama. Saboda haka ita gaskiya karbarta ake yi ko daga bakin waye ta fito. Domin rashin yardarka ba zai sa Allah ya canza gaskiya ba, sannan kuma yardarka ga qarya ba zai sa Allah ya tabbatar da ita ba.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.
(08137925034)
11th April, 2021/ 29th Sha'aban, 1442.