Daga Ammar M. Rajab
Kamar yadda ya saba a duk shekara a lokaci irin wannan na Ramadana, jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, Shaikh Ibraheem Zakzaky na raba kayan abinci ga mabukata a duk lokacin da watan Ramadana ya gabato. Kayan abincin wanda suka hada da shinkafa, Masara, Gero, Suga ,Taliya da dai sauran su sun sha rabo a tsakanin mabukata.
A bana ma kamar kowacce shekara, duk da Shehin Malamin na daure a hannun gwamnatin Nijeriya tun bayan auka masa da gwamnatin ta yi a ranar 12 g watan 12 na shekarar 2015, amma ya yi umurni ga 'yan'uwansa na jini da wasu ba'adin almajiransa da a baiwa duk wadanda aka san yana baiwa wannan tallafi a lokacin da yake nan a duk Unguwannin Zariya. Kuma tallafin na bana na kayan abincin ya nunka. Kuma tuni aka mika su ga inda ya dace.
Al'ummar da suka amfana da wannan tallafi sun yi matukar godiya bisa wannan karamcin da Shehin Malamin yake nuna musu duk da kuwa yana daure, harda mamakinsu na ganin yadda bai manta da su ba. Tare da yi masa addu'ar fatan alheri.
-Ammar Muhammad Rajab
19/4/2021