Sakon Na Yau Dakai Kadai Nake Dan Uwa na Ka Taimaka Ka Karanta Kuma kafahimci Kalmomina Tsawon Dadewar da Mukayi tare dakai a Social media !!!

 



Koda 'Dan Uwa Dan Buraza Zai Daddatsani ya Konani da Raina Bazan Fito Inzageshi da Aibatashi A Social media ba..



Kamar Yadda Almajiran  'Dan Fodiyyo Suke da Suna Jama'a Haka Almajiran Zakzaky Muke da Suna 'Yan Uwa.



Bayan Tarukan Harka da Akeyi Na Cikin Gida da Sassa Daban Daban Banga Abunda Yasa Na Tara 'Yan Uwa da Abokkai, Malamai da Yanne  Na Nesa Dana Kusa Kamar Social media ba. 


Me kayiman Me nayi ma Dazan Zageka ko Kazage Ni ?? 


Idan ka yabeni ko Ka kusheni Hakan Duka Kanka Kayiwa Hidima, Idan Na yabeka ko Nakushe ka Duka kaina nayiwa Hidima...


Miyasa Wani  Dan Uwa Zakaji Anan Social Media bakinsa zai zama babu linzami irin na mahaukaci. Ta yanda zai zagi mutum duk girmansa, duk matsayinsa duk iliminsa, kuma duk shekarunsa ba tare da ya ji komai ba a Zuciyar shi ba ! Tunanen yake ya Burge Kuma Addini yake Yiwa Hidima!!.


Duk da Ra'ayi Rigane Amma Kasaka Mai Kyau zaifi, Kuma Addini ba Ra'ayi bane Furuci ne da aiki....


Ƴan’uwa mu ɗauki social media wani wuri ne da muke shigansa don ganin abun da duniya ke ciki kuma don mu rubuta abun yake cikin ranmu tun daga addini da fannin rayuwa. Amma kada mu bashi wani muhimmanci da muke jin babu wanda zai iya raba mu da shi. Ya zamana a yau in muka bar wani wuri da muke chatting ba zamu shiga damuwa da tashin hankali ba.


Musamman mata waɗanda basu da aure su saka a ransu cewa, za su iya auren wanda zai iya hanasu chatting ma gaba ɗaya. Kenan in tana so kada ta haɗu da ƙalubalen rayuwa sai ta saisaita tunaninta tun wuri. Kuma ta daina ɗaukan tsatstsauran ra’ayin da ba zasu kai ta ga tudun mun tsira ba.


@Dan Masani 08149993999

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post