2021-04-18
MDD ta ce rikice-rikice tsakanin kungiyoyin ‘yan ta’adda da sojojin
gwamnati a jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya, na yi wa
ayyukan jin kai a jihar tarnaki.
Kakakin Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya ce ma’aikatan jin
kai na MDD na ci gaba da samun rahotanni masu tayar da hankali
dangane da arangamar da ake tsakanin ‘yan ta’adda da sojojin kasar a
garin Damasak na jihar.
Stephane Dujarric, Ya kara da cewa, a makon da ya gabata ma, an kai
hari kan kadarorin ma’aikatan jin kai a Damasak, inda aka lalata
ofisoshin kungiyoyin ayyukan jin kai a kalla 5, da tarin motocinsu, da
wajen adana kayayyaki na tafi da gidanka, da tankunan ruwa, da wata
cibiyar kula da lafiya, ta kula da masu fama da tamowa. An kuma samu
karin rahotannin rikice-rikice a wannan makon.
Mista Dujarric, ya yi gargadin cewa, wadannan hare-hare za su yi tasiri
kan ayyukan jin kai da kariyar da ake ba kusan ‘yan gudun hijira 9,000
da wasu mutane 76,000 na yankin dake ba ‘yan gudun hijirar mafaka.
024
Source: BIN MUHAMMAD PRESS
WHATSAPP GROUP
08032147367