Ramadan Hadiyya: Sheikh Zakzaky ya raba kayan abinci ga zawarawa da sauran mabukata yau a garin Kaduna.

 



A yau lahadi Sheikh Zakzaky ya raba kayan abinci ga zawarawa, mazauna garin kaduna.

Kamar yadda zaku gani a hoto cewa; wakilan zawarawa din ne ke karban kayan abincin domin rarrabawa a junansu.

Kada a manta a jiya asabar ma jagoran Harkar Musulunci a Najeriya, Shaikh Ibraheem Zakzaky din ya aike da gudummawar abinci ga 'Yan Gudun Hijira da ke sansanin Marafa, jihar Zamfara, arewa maso yammacin Nijar . Wannan tallafin ana bawa marasa galihu ne, akasari ana aiwatar da shi ne a cikin watan Ramadan.

Inda a yau kayan abincin suka isa ga yan gudun hijirar. Wannan shehin malamni, ya kasance malami mai kira zuwa ga addinin Muslunci na gaskiya, a kokarin sa na ganin kowa yayi tayuwa cikin aminci, a gobe kiyama kima ya zama yana da uzuri gaba ga Allah (T)


Amma Azzalumar gwamnatin Najeriya tana tsare dashi ba tare da laifin komi ba, tun bayan harin da sojojin Najeriya suka kai masa a gidansa, a shekarar 2015.

25/04/2021 



Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post