Ra'ayin Ibn Katheer game da matsayin mahaifin Annabi (S.A.W.W) ...!



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


BABU WANI KOKONTON CEWA SU 'YAN WUTA NE 


Tabbas mun san ba soyayya bace ka bawa mutum matsayin da Allah bai bashi ba, ko kuma ka kai shi inda Allah bai kai shi. Wannan dalili yasa kuke ji ko ganin muna fitowa muyi dogon bayani akan wani abu idan ya kasance an shigo da qarya cikinsa ko kuma an murguda shi daga haqiqanin yadda yake. 


Abu wanda yanzu haka malamai ke yin luguden labba (💋) a kansa game da matsayin mahaifan Manzon Allah (S. A. W. W). Wasu na cewa lalle su 'yan Aljannah ne, yayin da wasu ke tabbatar da cewa su 'yan Wuta ne babu wani kokonto. 


To, a yau munyi nufin dauko fahintar wani babban malami ne daga cikin manyan malaman Salafiyya wanda aka fi saninsa da suna IBN KATHEER. 


Shi wannan malami ya kawo cikin Tafsirinsa qarqashin ayar nan dake cewa; 


👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇


" إِنَّا أَرْسَلْنَاكَ بِالْحَقِّ بَشِيراً وَنَذِيراً وَلاَ تُسْأَلُ عَنْ أَصْحَابِ الْجَحِيمِ."


" LALLE MUN AIKO KA DA GASKIYA, MAI BUSHARA DA KUMA GARGADI, (amma fa) KADA KAYI TAMBAYA GAME DA 'YAN WUTA ."



(SURATUL-BAQARATA:119)



To, cikin qoqarinsa na tabbatar da cewa wannan aya ta sauka akan mahaifan Annabi Muhammad (S. A. W. W), da kuma qoqarinsa na qaryata masu cewa ai an rayar da mahaifan nasa (S. A. W. W) har ma sunyi imani dashi sannan aka qara karbar ransu, shine yake cewa; 


👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇



وقد ذكرنا في التذكرة أن الله أحيا له أبويه حتى آمنا به وأجبنا عن قوله : " إن أبي وأباك في النار !" « قلت » والحديث المروي في حياة أبويه عليه السلام ليس في شيء من الكتب الستة ولا غيرها وإسناده ضعيف والله أعلم 


Haqiqa an ambata mana cikin TAZKIRAT cewa lalle Allah ya rayar masa da mahaifansa har sai da suka yi imani dashi. Sai muka yi mamaki game da fadinsa (S. A. W. W) ;


" LALLE BABANA DA BABANKA SUNA WUTA ."


Nace (in ji Ibn Katheer), lalle hadisin da aka riwaito na rayar da mahaifansa (S. A. W. W) basu daga cikin wani abu na littafan Ahlus-Sunnati, ko ma waninsu, domin Isnadin nasa mai rauni ne (weak). 


Abinda ya yarda dashi shine wannan hadisi da aka riwaito wanda ke nuna cewa wai Annabi (S. A. W. W) yace Babansa da baban wani duk suna wuta. Wannan hadisi kuwa ya zo ne cikin wadannan littattafai na Ahlus-Sunnati :-


-Baihaqiy, J:7, Sh:190.


- Sunan Abu Dawud, Sh:17


- Muslim, Kitabul-Iman, Hadisi na 347


- Dabarani, cikin Kabeer nasa, J:4, Sh:32


Wannan shine ra'ayinsa kuma ra'ayin wasu malaman Ahlus-Sunnati na wannan zamani da suke fitowa cikin kafafen yada labarai da guraren wa'azozinsu suna tabbatar da haka. 


Shi kuma Ibn Jareer Ad-Dabariy ya kawo wata riwaya ce wacce ke tabbatar da cewa wannan ayar kan mahaifan Annabi Muhammad (S. A. W. W) ta sauka. Ga yadda riwayar take; 


👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇


قال ابن جرير وحدثني القاسم أخبرنا الحسين حدثني حجاج عن ابن جريج أخبرني داود بن أبي عاصم به أن النبي صلى الله عليه وسلم قال ذات يوم أين أبواي فنزلت « إنا أرسلناك بالحق بشيرا ونذيرا ولا تسأل عن أصحاب الجحيم » 


Ibn Jareer yace, Qasim ya bamu labari, Hussaini ya bamu labari, Hajjaj ya bamu labari daga Ibn Juraij, Dawud Bn Abiy Aseem ya bamu labari cewa, " Lalle wata rana Annabi (S. A. W. W) yace; " A INA MAHAIFANA SUKE NE ?"


Sai aka saukar; 


" LALLE MUN AIKO KA DA GASKIYA, MAI BUSHARA DA GARGADI, KUMA KADA KAYI TAMBAYA GAME DA 'YAN WUTA ."


-AT-HAADUS-SAADAT, J:8, SH:440


Wannan dai shine ra'ayin malaman Ahlus-Sunnah masu ambaton kansu da IZALA ko SALAFIYYA, amma babu irin wannan fahinta cikin malaman Sunnah na dukkan 'Dariqu. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.


       (08137925034)


29th April, 2021, 17th Ramadan, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post