Muh'd Bala Afuwa Yayi Tirr da Halayen Wasu Matasan 'Yan Uwa A Lokacin Bukukuwan Auren Su !!!

 


Yayi Wannan Rubutun ne Frofile dinshi na Facebook Inda yake Cewa:-

"A 'Bridal Shower' taci Kwalliya irinta Amaa, a dinner a sanya waqar Hausa ana jujjuyawa tare da Angon a gaban Yan Uwa da Abokan Arziki, Kawayen Amarya suyi Anko Kala su shafe fuska da Kwalliya su riqo jaka a kafada, 


In aka matsa kadan ai ta yakutar Juna akan Mahanga da Fahimta ta gwagwarmaya, Imagine, lokacin da Iyayenmu suka Auri junansu ba a irin wannan Iya shegen? Gaba-daya shekaru nawa ne? Meyasa suka haqura da irin wannan takadirancin da sunan taya juna Murna suka zabi ai Walima tare da Nasiha ma Ango da Amarya akan kiyaye hakkokin Allah? 


Masu raya cewa su na tare da Fikra Salima ta gidan Jagora, meya hanaku koyi da biki irinna Syed Muhammad Zak-zaky (H)? Munso ace su Shahid Syed Ahmad su na nan, tabbas da tasirin bikinsu ya katange matasanmu da yawa fadawa irin wannan Sharholiyar da sunan taya Ango da Amarya murna.


Harkarnan ba ta uban kowa bane, kayan Allah ne, Sheikh Zakzaky (H) kuwa bawansa ne da ya tasheshi ya ga damar bashi Jagorancin wannan tafiya, mu ji tsoron Allah mu sakaye wasu bukatun kawukanmu, mu haqura da wasu al'amuran tunda akwai kyakkyawan fatan Jagora dangane damu,


A daina hantarar Yan mata masu sanya Hijabi kala, madamar ba za'ai irin wadannan bidi'o'in birki ba, biki ranar murna ce, dole a gwada farinciki cikinta, amma su Malam sunce duk kidan da zai sanya kamanta Allah ta'ala haramun ne sauraransa, kuyi aiki mai kyau yayin bikinku, don wataran Hotunan za'a haskawa 'yayan ku, mukam Alhamdulillah in muka tuna yadda iyayenmu suka auri junansu, ba dogon buri, ba 'Qauyawa day', casun Amarya da kawayenta ko dinner da ta saba lamba.


Sheikh Zakzaky yana cewa "Mu komi namu Addini ne".


-Muhd Bala Afuwa

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post