Mlm Zakzaky (h) Shekaru 72 a duniya Amma Babu Awanni Saba'in na Ta'addanci a Da'awar sa..!!!



... Umar Hassan Gololo... 

Bamu ji ba, wadanda suka gabace mu basu fada mana anyi ba,bamu gani a rubuce a cikin tarihin Harkah Islamiyyah karkashin jagorancin Malam Zakzaky(H) cewa ta kai hari gidaje, Shaguna, Ofisoshin Gwamnatin Nigeria ko kasuwanni da sunan jihadi ba. 

Tun Malam Zakzaky(H) yana University ake kiransa da wadanda suka amsa da'awarsa 'yan tashin hankali, amma babu Wanda zai iya kawo suna ko garin da wani Amir ya bada umurnin akai hari Police station ko Kotun garinsu. 

Bamu san wani mutum da Harkah Islamiyyah ta bada umurnin a kashe shi saboda ya aikata wani laifi ba. 

A dukkan kotuna, Ofisoshin 'Yansanda ko tribunal babu sunan Almajiransa a cikin ta'addanci, sace-sace, kone-kone da kashe-kashen jama'ar da ba su ji ba basu gani ba da sunan addini ko kabilanci.. 

Muna rokon Allahu Ta'ala ya tabbatar damu karkashin jagorancin jagoran da yake kiran al'umma zuwa ga tsira Duniya da Lahira alfarmar Imam Mahdi Ajjalallahu Farajahum....

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post