Matsayin Rubutu da Wallafa A Mahangar Muslimci ! _Sayyid Abdullahi Ashura Bauchi.

 


MU'UTAMAR NA CIBIYAR WALLAFA DA YADA AYYUKAN SAYYID ZAKZAKY (H) KARO NA 2 A GARIN BAUCHI 


@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


JAWABIN RANA TA BIYU ZAMA NA BIYU 


Bayan kammala jawabai na zaman farko a rana ta 2 wanda aka saurara daga bakin Malam Ibrahim Gamawa da kuma Alhaji Hassan Abdullahi Garo sai aka tafi zuwa yin salloli da cin abinci. 


Misalin 4:30pm aka fara zama na biyu cikin rana ta biyu, malami mai jawabi shine Sayyid Abdullahi Ashura Bauchi. 


MATSAYIN RUBUTU DA WALLAFA A MAHANGAR MUSLIMCI shine Maudhu'in da malamin ya gabatar a wannan taro. 


Abu na farko daya fara shine bayyana yadda rubutu ya samo asali cikin Qur'ani kamar yadda Allah (T) yayi rantsuwa da Alqalami da abinda alqalami ke rubutawa. 


بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ


نٓۚ وَٱلۡقَلَمِ وَمَا يَسۡطُرُونَ (١)


" NUUN!  INA RANTSUWA DA ALQALAMI DA ABINDA YAKE RUBUTAWA. "


Malamin yace saboda muhimmanci rubutu ne yasa Allah yin rantsuwa da alqalami da abinda alqalamin ke rubutawa. Sannan yayi ta'arifin rubutu da cewa shine tattara wasu kalmomi a rubuta su yadda za su bada ma'ana, kuma wallafa ya kasance harhada wadannan kalmomi/jimloli a guri guda yadda za su zama wani dawwanannen abu. 


Malamin ya qara da cewa shi rubutu ba 'yan Adam ne kadai ke yinsa ba, 'a'a, harda Aljanu da Mala'iku suna yinsa, kuma babu wani Annabi wanda bai iya rubutu ba. 


Ya cigaba da cewa rubutu yafi matuqar tasiri fiye da fada da baki, wannan dalili ne ma yasa  cikin da'awar Manzon Allah (S. A. W. W) an riqa isar da ita ne ta hanyar rubutu ga wadanda saqon muslimcin bai kai gare su ba, domin wasiqa ce ya riqa rubutawa yana aika 'yan saqo zuwa ga wasu Sarakuna wadanda yake kiransu zuwa ga muslimci, duk da cewa akwai 'yan saqon amma bai barsu suyi bayani da bakinsu ba. 


Malamin ya qara kawo muhimmanci rubutu ta hanyar kawo ayar dake magana kan bashi 


يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِذَا تَدَايَنتُم بِدَيۡنٍ إِلَىٰٓ أَجَلٖ مُّسَمّٗى فَٱكۡتُبُوهُۚ ....


" YAA KU WADANDA SUKA YI IMANI  !  IDAN KUKA YI WANI ALQAWARI /YARJEJENIYA DA BASHI, TO, KU RUBUTA..... 


(BAQARA :282)


Yace wannan tasirin da rubutu ne ke da shi yasa akayi wannan umarni, domin duk abinda aka rubuta shi yana nan dawwane komai dadewar sa. 


Ya kawo wasu hadisai biyu na Imam Sadiq (A. S) dana Ibn Umar cewa, Imam (A. S) yace; 


" KU RUBUTA, DOMIN IDAN BAKU RUBUTA BA BA ZA KU KIYAYE BA. "


Ibn Umar kuma ya tambayi Annabi (S. A. W. W) cewa zai iya yiwuwa ya qayyade /daure ilimi  ? Manzon Allah (S. A. W. W) ya amsa masa da cewa eh zai iya. Malamin yayi sharhi da cewa duk abinda aka daure (tie) shi ba zai wargaje ba, amma abinda aka barshi haka zai iya wargajewa. 


Malamin ya kawo cewa littafai uku ne aka fara rubutawa a zamanin Annabi (S. A. W. W), sune :-


(1)- AMAALI LI RASUL :- Abubuwan da Annabi (A. A. W. W) ya riqa fada kuma Imam Ali (A. S) yana rubutawa. 


(2)- ALQUR'ANI :- Wanda Imam Ali (A. S) ya rubuta da farko bayan wafatin Manzon Allah (S. A. W. W). 


(3)- MUSHAF-FATIMA :- Zantukan Sayyidah Fatimah (S. A) wanda take fada Imam Ali (A. S) na rubutawa. 


Malamin ya kawo labarin ziyarar da suka taba kaiwa Sayyid (H) a lajanarsu ta Ittihadu, sai Sayyid (H) ya umarce su da su kasance masu tafiya da alqalumansu suna rubuta duk wani abinda suka ga ya dace suyi waqa a kansa. 


Yace, Imam Sadiq (A. S) ya umarci almajirinsa Batheet da cewa; 


" KAYI RUBUTU KUMA YADA SHI CIKIN MUTANE, KUMA KA BARWA 'YA'YANKA ABIN GADO. DOMIN DA SANNU WANI ZAMANI ZAIZO YADDA........ "


Malamin yace idan ka cire rubutu to babu komai wanda zai rage har ma Qur'ani, domin shima rubutu ne. 


ذَٰلِكَ ٱلۡكِتَٰبُ لَا رَيۡبَۛ فِيهِۛ هُدٗى لِّلۡمُتَّقِينَ ٢


" WANNAN LITTAFI NE (rubutu) WANDA BABU KOKONTO CIKINSA. "


A qarshen jawabin nasa yace lalle idan babu rubutu za a rasa abubuwa da dama. Sannan ya qara da cewa ko da ma an rubuta wani lokaci wani abu kan faru a rasa shi, ko kuma ma mutum ne da kansa zaiyi sanadin rasa su saboda wani yanayi. Har ya bada labari game da wani almajirin wani Imami mai suna  AHMAD BN ABIY HUMAIR zamanin mulkin Haruna Al-Rasheed wanda ya rubuta littafai kimanin 92, amma saboda ganin cewa shi dan Shi'ah ne aka riqa gallaza masa wanda a qarshe 'yarsa ta bisne littafan daya rubuta don gudun kada a gano su, wanda hakan yayi sanadin salwantarsu. 


               TA'ALIQI 


Malam Nurudden Aliyu Alqaleri shine yayi ta'aliqin wannan jawabi, inda ya fara jawabinsa da cewa, su bayin Allah ma kawai don sanin muhimmanci rubutu suke buqatar a rubuta su .


" KUMA KA RUBUTA MU CIKIN MASU SHAIDA  ."


Sannan kuma yace lalle Allah ma na rubutu (ta hanyar Mala'ikunsa) inda ya bada misali da ayoyin dake cewa; 


" LALLE MU MUNA RUBUTA ABINDA KUKE AIKATAWA. "


Yace a ranar alqiyama sai Allah ya cewa bayin nasa; 


" KA KARANTA LITTAFINKA DA KANKA A YAU KUMA KA YIWA KANKA HISABI ."


Yace bayan bayin sun karanta littafin sunga dukkan abinda ke ciki sai suce; 


" MENENE GA WANNAN LITTAFI BA YA BOYE WANI ABU QANQANI KO MAI GIRMA FACE YA KIYAYE SHI ? "


Malamin yace wani lokaci rubutu kan iya zama wajibi ko mustahabbi. Zai iya zama wajibi idan ya kasance aya yin wasu abubuwa kamar batanci ga harka ko muzantata ka fito kayi rubutu don kare wannan al'amari. 


Sai dai malamin ya qarqare jawabin nasa ne da cewa shi rubutu yana da wasu qa'idoji wadanda wajibai ne mai yinsa ya kiyaye su. 


Dole ya zama an fadi gaskiya, 


Mai gaskiya cikin abinda zai fada, 


Mai adalci kuma kada ya cutar.  Sai ya kawo sharudan dake cikin ayar bashi inda yace; 


وَلۡيَكۡتُب بَّيۡنَكُمۡ كَاتِبُۢ بِٱلۡعَدۡلِۚ .............وَلَا تَسۡـَٔمُوٓاْ أَن تَكۡتُبُوهُ صَغِيرًا أَوۡ كَبِيرًا إِلَىٰٓ أَجَلِهِۦۚ ذَٰلِكُمۡ أَقۡسَطُ عِندَ ٱللَّهِ وَأَقۡوَمُ لِلشَّهَٰدَةِ وَأَدۡنَىٰٓ أَلَّا تَرۡتَابُوٓ........وَلَا يُضَآرَّ كَاتِبٞ وَلَا شَهِيدٞۚ ........


" KUMA SHI MAI RUBUTUN A TSAKANINKU YA RUBUTA DA ADALCI(kada yayi qarya cikinta)..... KUMA KADA KUYI RAUNI WAJEN RUBUTA SHI QANQANI NE KO MAI GIRMA ZUWA AJALINSA. HAKAN SHINE MAFI ADALCI WAJEN ALLAH KUMA MAFI DAIDAI WAJEN SHAIDA, KUMA MAFI KUSA DON KADA KU KARKATA..... KUMA KADA SHI MAI RUBUTUN YA CUTAR KO KUMA MAI (bayar) DA SHAIDAR... "


       (BAQARA:282).


Ya qarqare jawabin nasa da cewa kowanne marubuci za azo dashi ne ranar alqiyama yana cikin wani akwati na wuta, wannan alqalami (abinda ya rubuta) shi zai kubutar dashi. 


Kenan idan yayi qarya ko cutar da wani ko boye gaskiya sai ya tafi wuta ta sanadin wannan rubutu nasa. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼Ado Isah Guda. 


       (08137925034)










          3rt April, 2021

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post