-Idan mutum ya bibiyi tarihin rayuwar Imam Ali to zai ga misalai masu yawa na irin hakurinsa ga bangarorin mutane daban-daban wato masoyansa da kuma makiyansa wanda suka yi gaba da kiyayya dashi kai har ma suka yake shi sun tabbatar da haka ga misalan wasu daga cikin wannan dabi’a nasa na hakuri da kuma afuwa:
-A Lokacin yakin Jamal bayan Imam Ali (as) ya samu nasara da kuma galaba akan wadanda suka jagoranci yakin to baki dayansu haka yayi hakuri kuma ya yafe masu wato dai kamar yadda Manzon Allah ya yi afuwa ga mushirikai a fatahu Makka.
-Haka nan a lokacin yakin Siffin sojojin Mu’awiya suka zagaye kogin Furat da nufin hana Imam Ali da sojojinsa amfani da ruwan kogin, wanda sai da takai Imam Ali yayi masu magana akan su bari a yi amfani da ruwan amma suka ce a’a har ma da yin isgili suka ce masa ko digo daya ba zamu baku sai dai
ku mutu da kishi,
-to shine a lokacin Imam Ali ya bada umarnin a fafata dasu domin a kwace kogin furat din, ba a dauki lokaci ba aka samu galaba akansu aka kore su daga wannan kogi na Furat, to shine a lokacin wasu daga cikin sojojin Imam Ali suka ce masa mu hana su amfani da ruwan kamar yadda suka hana mu sai Imam Ali ya ce masu, “Wallahi ni ba zan yi masu abinda suka yi mana ba na hana mu ruwa saboda haka ku barsu in suna da bukata su zo su diba.”
-Haka nan dai a wannan yaki na Siffin lokacin da ake fafatawa shi wanda ya jagoranci yakin a lokacin da ya ga Imam Ali ya tunkaro shi da takobi kawai sai ya tube kayansa wato yayi tsirara ganin haka sai Imam Ali ya kauda kansa ya kyale shi wato bai kashe shi ba.
-Akwai lokacin da Imam Ali ya kira wani daga cikin bayinsa sai bai amsa masa ba, shine Imam Ali yake tambayar sa me yasa kana jin ina kiranka amma baka amsa man ba?
-Sai bawan yace na san ba zaka yin komi bane shi yasa ban amsa ba, shine Imam Ali ya ce, “Ina godiya ga Allah Ta’ala da ya sanya ni halittunsa sun aminta dani wato su yi min laifi amma ba zan yi masu komi ba daga karshe Imam Ali yace masa ka tafi na ‘yanta ka saboda Allah.”
-Mu dubi irin wannan gayar hakuri da kuma kyautatawa na Imam Ali (AS).
-Muhammad Jiddah Nguru