@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
BABU ANNABIN DA YA TABA CANZAWA SABODA TSANANIN BALA'I
A yanayin dabi'a irin ta dan Adam bai taba yin wani abu ba tare da wata manufa ba, ko da kuwa Mahaukaci ka gani yana tsintar wani abu kan Bola, to, shi manufarsa ita ce mutane sun bar abubuwa masu amfani, saboda haka bari shi ya kawar dasu ya alkinta su.
To, cikin 'yan Adam din kuma sai Allah ya tayar da Annabawa daga cikinsu bisa wata manufa. Shine Allah (T) ke cewa;
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
كَانَ ٱلنَّاسُ أُمَّةٗ وَٰحِدَةٗ فَبَعَثَ ٱللَّهُ ٱلنَّبِيِّـۧنَ مُبَشِّرِينَ وَمُنذِرِينَ وَأَنزَلَ مَعَهُمُ ٱلۡكِتَٰبَ بِٱلۡحَقِّ لِيَحۡكُمَ بَيۡنَ ٱلنَّاسِ فِيمَا ٱخۡتَلَفُواْ فِيهِۚ........... (٣١٢)
" MUTANE SUN KASANCE AL'UMMA GUDA, SAI ALLAH YA AIKA ANNABAWA (cikinsu) SUNA MASU BAYAR DA BUSHARA KUMA MASU GARGADI, KUMA YA SAUKAR DA LITTAFI TARE DASU BISA GASKIYA DOMIN (littafin) YAYI HUKUNCI A TSAKANIN MUTANE CIKIN ABINDA SUKA SABAWA JUNA.
(SURATUL-BAQARATA:213)
Kenan dukkan Annabawan da Allah ya aiko su shine domin su yiwa mutane bushara da samun Aljannah matuqar sun amsa kiransu, sannan kuma suna yi musu gargadi (tsoratarwa) game da wuta idan sun qi amsa wannan kira nasu.
Sannan kuma ya zama Allah ya saukar da littafi a matsayin abinda zai zama shine jagora wajen hukunta komai nasu wanda suke samun sassabawa tsakaninsu.
Akan wannan kira nasu aka riqa cutar dasu bisa nau'in cutarwa kala-kala. Mutum na farko wanda aka fara cutarwa kuwa kan wannan kira nasu shine Annabi Nuhu (A. S).
Sun qaryata shi, sunyi jayayya dashi, sunyi masa qazafi kan cewa qiren qarya ce kawai yake yi musu, har a qarshe suka neme shi da ya roqar musu azaba in har abinda yake fada gaskiya ne.
Shine Allah yake bamu labari cikin littafinSa kamar haka;
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
وَلَا يَنفَعُكُمۡ نُصۡحِيٓ إِنۡ أَرَدتُّ أَنۡ أَنصَحَ لَكُمۡ إِن كَانَ ٱللَّهُ يُرِيدُ أَن يُغۡوِيَكُمۡۚ هُوَ رَبُّكُمۡ وَإِلَيۡهِ تُرۡجَعُونَ (٤٣)
أَمۡ يَقُولُونَ ٱفۡتَرَىٰهُۖ قُلۡ إِنِ ٱفۡتَرَيۡتُهُۥ فَعَلَيَّ إِجۡرَامِي وَأَنَا۠ بَرِيٓءٞ مِّمَّا تُجۡرِمُونَ (٥٣)
" (Na san) NASIHATA BA ZA TA AMFANAR DAKU BA IN HAR NAYI NUFIN YI MUKU NASIHA, IN DAI HAR ALLAH YAYI NUFIN HALAKA KU (saboda bijirewarku). SHINE UBANGIJINKU, KUMA ZUWA GARE SHI AKE MAYAR DA KU ."
" KO KUMA SUNA CEWA: (Nuhu ne) YA QIRQIRE SHI. (To), KACE, " IDAN NINE MA NA QIRQIRE SHI AI LAIFINA A KAINA YAKE (ba a kanku ba), KUMA NI MAI BARRANTA NE DAGA ABINDA KUKE YI NA LAIFI ."
(SURATUL-HUD:34-35)
To, Sayyid Zakzaky (H) kan irin wannan kira ya taso kuma yake kanta, sai dai da shike ya san tabbatar addini ba a hannunsa yake ba shine yake ce mana shi yana yin wannan kira ne don neman yardar Allah.
Matuqar dai zai sami yardar Allah to, ya shiryawa fuskantar kowacce irin jarrabawa da bala'o'i, kuma akan hakane ya hadu da wannan bala'i a matsayin mafi girman jarrabawar da Allah ya shirya masa.
Tabbas, ya sami wannan yarda ta Allah domin komai bala'i ba zai canza daga kan wannan kira nasa ba. Wannan dalili ne ma yasa azzalumar gwamnatin Buhari taqi ta sake shi don ta san ba zai taba canzawa ba.
Da ace wannan azzalumar gwamnatin ta san cewa in har ta sake shi zai bar abinda yake yi, wallahi da tuntuntuni sun sake shi ya dawo cikinmu ya dau qasqanci.
Annabi Ibrahim (A. S) bai sami matsayin da ya samu ba har sai da aka jarraba shi da mafi girman jarrabawa kuma ya cinye.
Anyi jayayya dashi an qaryata shi kuma an jefa shi cikin wuta , amma duk da haka bai zama me babban matsayi ba har sai da akayi masa umarnin yanka dansa kuma ya sallama.
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
فَبَشَّرۡنَٰهُ بِغُلَٰمٍ حَلِيمٖ ١٠١
فَلَمَّا بَلَغَ مَعَهُ ٱلسَّعۡيَ قَالَ يَٰبُنَيَّ إِنِّيٓ أَرَىٰ فِي ٱلۡمَنَامِ أَنِّيٓ أَذۡبَحُكَ فَٱنظُرۡ مَاذَا تَرَىٰۚ قَالَ يَٰٓأَبَتِ ٱفۡعَلۡ مَا تُؤۡمَرُۖ سَتَجِدُنِيٓ إِن شَآءَ ٱللَّهُ مِنَ ٱلصَّٰبِرِينَ ٢٠١
فَلَمَّآ أَسۡلَمَا وَتَلَّهُۥ لِلۡجَبِينِ ٣٠١
وَنَٰدَيۡنَٰهُ أَن يَٰٓإِبۡرَٰهِيمُ ٤٠١ قَدۡ صَدَّقۡتَ ٱلرُّءۡيَآۚ إِنَّا كَذَٰلِكَ نَجۡزِي ٱلۡمُحۡسِنِينَ ٥٠١
إِنَّ هَٰذَا لَهُوَ ٱلۡبَلَٰٓؤُاْ ٱلۡمُبِينُ ٦٠١
وَفَدَيۡنَٰهُ بِذِبۡحٍ عَظِيمٖ ٧٠١
وَتَرَكۡنَا عَلَيۡهِ فِي ٱلۡأٓخِرِينَ ٨٠١
سَلَٰمٌ عَلَىٰٓ إِبۡرَٰهِيمَ ٩٠١
كَذَٰلِكَ نَجۡزِي ٱلۡمُحۡسِنِينَ ٠١١
إِنَّهُۥ مِنۡ عِبَادِنَا ٱلۡمُؤۡمِنِينَ ١١١
" SAI MUKA YI MASA BUSHARA DA YARO (Isma'il) MAI HAQURI. "
" A YAYIN DA YA ISO KAI-KAWO TARE DASHI SAI YACE; " YAA KAI 'DANA ! LALLE NI NA GANI CIKIN BACCINA INA YANKA KA, DUBA (yi nazari) ME KA GANI (game da wannan al'amari) ? (Isma'il) YACE; " YAA BABANA ! AIKATA DUK ABINDA AKA UMARCE KA, DA SANNU IN ALLAH YASO ZA KA SAME NI CIKIN MASU HAQURI ."
" TO, A YAYIN DA SUKA SALLAMA (dukka su biyun) KUMA (Ibrahim) YA KWANTAR DASHI TA BANGAREN GOSHINSA (da nufin yanka) ."
" SAI MUKA KIRA SHI (cewa) YAA IBRAHIM !"
" HAQIQA KA GASKATA MAFARKINKA. LALLE KAMAR HAKA MUKE SAKAWA MASU KYAUTATAWA (a ayyukansu) ."
" LALLE WANNAN ITA CE JARRABAWA BAYYANANNIYA (practically) ."
" SAI MUKA FANSHE SHI (Isma'il) DA WANI ABIN YANKA MAI GIRMA ."
" KUMA MUKA BAR (kalmar yabo abin tattaunawa) A KANSA CIKIN MUTANEN QARSHE (wadanda suka zo a bayansa har zuwa kanmu) ."
" AMINCI YA TABBATA AKAN IBRAHIM ."
" KAMAR HAKANE MUKE SAKAWA MASU KYAUTATAWA ."
" KUMA LALLE SHI YANA DAGA CIKIN BAYINMU MUMINAI ."
(SURATUL-SAFDAT:101-111)
Yi nazari sosai dan'uwana ka kalli irin jarrabawar da Allah ya yiwa Annabi Ibrahim (A. S) da kuma ta Sayyid Zakzaky (H), za kaga iri daya ce babu bambanci.
Kuma yadda Annabi Ibrahim (A. S) bai canza ba hakama Sayyid Zakzaky (H) yake ba zai canza ba har karbar numfashinsa.
YAA ALLAH KA TABBATAR DAMU TARE DA SHI HAR ZUWA KARBAR NUMFASHINMU !
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
(08137925034)
9th April, 2021/ 27th Sha'aban, 1442.