Malaman farko sun yi aiki, sai dai sun yi mummunan gazawa ta wani bangaren !


 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


ZA KA IYA KARANTA LITTAFIN MUTUM KUMA KA FI SHI FAHINTAR ABINDA YA RUBUTA 


Dole ne a fara yabon wadannan malamai bisa gwazon da suka yi na tafiye-tafiye da kuma sallama komai nasu ta fuskacin lokaci, dukiya dama komai nasu wanda ya taimaka musu har suka kai ga samun ilimi da kuma taskake shi har yazo gare mu. 


Da ba don wannan gwagwarmaya da kuma sadaukarwar da suka yi ba haqiqa da bamu sami wannan ilimi da muke amfanuwa dashi har muke gutsuro muku wani abu daga cikinsa kuna amfana ba. 


Ban san kalmar data dace nayi amfani da ita anan ba, rashin sani ne ko siyasa ko kuma wata mummuniyar manufa ce tasa sai kaga cikin littafi daya (1) an kawo maganganu masu cin karo da juna kuma ace maka dukkansu sun inganta. 


Idan ya zamana rashin sani ne yasa aka inganta abubuwa masu cin karo da juna sai a yiwa marubucin uzuri, domin shi dan Adam mai gazawa ne (ajizi). Idan kuma ya zama siyasa ce don fifita wasu akan wasu ba bisa hujja daga Allah ko Ma'aikinsa (S. A. W. W) ba, ko kuma wata mummuniyar manufa ce, to, a gaskiya yin hakan bata ayyukan mutum ne na alkhairi. 


Da shike ita baiwa Allah kan bada ita ne ga wanda yake so sai kaga marubuci ya rubuta abu amma bai gano matsalar dake ciki ko tufka-da-warwara ba, har ma daga mutane da dama sun karanta basu gano wannan matsalar ba. 


To, idan haka ta faru ya zama an cakuda qarya da gaskiya kenan wanda hakan ke gurbata tunanin mutane har su kalli qarya a matsayin gaskiya, ita gaskiyar kuma ayi mata kallon qarya. Idan haka ta kasance, to, haqqi ne akan wanda ya fahinci hakan ya fayyacewa mutane gaskiya don su bambanceta daga qarya. 


Bari dai mu kawo wasu misalai daga hadisin Bukhari don auna su da hankali da kuma mahanga ta ilimi. 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


MATSAYIN A'ISHA DA BABANTA 


(3662)- حدثنا معلى بن أسد: حدثنا عبد العزيز بن المختار قال: خالد ؟؟ الحذاء حدثنا، عن أبي عثمان قال: حدثني عمرو بن العاص رضي الله عنه: 

أن النبي صلى الله عليه وسلم بعثه على جيش ذات السلاسل، فأتيته فقلت: أي الناس أحب إليك؟ قال: (عائشة) 


Mu'allah Bn Asad ya bamu labari, Abdul-Azeez Bn Mukhtar ya bamu labari, Khalidu Al-Hazzaa'i yace ; an bamu labari daga baban Usmanu yace, Amruu Bn Aas (R. A) ya bamu labari cewa : Annabi (S. A. W. W) ya aika shi cikin wata runduna a wata rana, sai naje masa nace; " Wanne mutum ne yafi soyuwa gare ka ? Yace; 


" A'ISHATU. "


Sai nace, daga maza kuma fa ? Sai yace; 


" BABANTA. "


Nace, sannan waye ? Yace; 


" SANNAN UMAR BN KHADDAB. "


Ya lissafa mutane.


(Babin Falalar Abubakar, hadisi na 3662)


NB:- Anan za kuga abinda yazo cikin fassarar ya fi abinda ke cikin rubutun larabcin, dalili kuwa shine an datse hadisin ne, amma in ka duba shi cikin littafin za kaga dukkan abinda na ambata. 



              NAZARI

           ------------------


Abinda za ku fara dubawa anan shine, Manzon Allah (S. A. W. W) fa na da 'yarsa ta cikinsa, sannan yana da dan'uwa na jini amma yace ya fi son matarsa fiye da 'yarsa? Sannan kuma ya fi son aboki fiye da dan'uwansa ?


    MATSAYIN IMAM ALI (A. S) 


وقال النبي صلى الله عليه وسلم لعلي: (أنت مني وأنا منك) [ 



وقال عمر: توفي رسول الله صلى الله عليه وسلم وهو عنه راض 


 Annabi (S. A. W. W) ya cewa Aliyu; 


" KAI DAGA GARE NI KAKE, KUMA NIMA DAGA GARE KA NAKE ."


Umar yace; 


" MANZON ALLAH (S. A. W. W) YA RASU YANA MAI YARDA DASHI (Aliyu) ."


Maganar nanan tsakanin hadisi na 3699 dana 3700 a farkon babin.


           NAZARI

          ---------------


Idan muka nazarci wannan hadisi kuma za muga Annabi (S. A. W. W) na nuna cewa shi da Imam Ali (A. S) abu guda ne, amma a tunaninku mutum zai so wani fiye da kansa ?



MATSAYIN SAYYIDAH FATIMA (S. A) 


(3767) - حدثنا أبو الوليد: حدثنا ابن عيينة، عن عمرو بن دينار، عن ابن أبي مليكة، عن المسور بن مخرمة رضي الله عنهما: 

أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: (فاطمة بضعة مني، فمن أغضبها أغضبني)


Baban Waleed ya bamu labari, Ibn Uyainata ya bamu labari daga Amruu Bn Dinaar, daga Ibn Abiy Mulaikata, daga Miswaru Bn Mukhrimata (R. A) cewa: Manzon Allah (S. A. W. W) yace; 


" FADIMATU TSOKA CE DAGA GARE NI, DUK WANDA YA FUSATATA YA FUSATA NI !"


(Falalar Fatimah, Bukhari, hadisi mai lamba 3767)


Duk wadannan riwayoyi uku sun fito ne cikin Sahihul-Bukhari wanda ake tabbatar da cewa dukkan riwayoyin ingantattu ne. Idan kuwa ya zama haka, to, akwai cin karo da juna. 


Domin cikin riwayar farko an nuna kaf cikin matan duniya babu wacce Annabi (S. A. W. W) ke so kamar A'isha, wanda hakan ke nuna mana 'yarsa ma ba komai bace in an kwatanta soyayyar matarsa a wajensa. Sannan kuma babu wanda yake tsananin sonsa cikin maza kamar Abubakar. 


A riwaya ta biyu kuma yana nuna cewa ai shi da Imam Ali (A. S) abu guda ne, amma duk da wannan maganar tasa sannan yace ya fi son wani fiye da wanda suke abu guda ?


Ga kuma tsokar jikinsa wacce yake cewa duk wanda ya fusatata shi ya fusata. Yanzu kai mai karanta wannan rubutu kana ga akwai wata mace cikin matanka wacce ka fi so fiye da 'ya'yanka? 


Maganar gaskiya dai dole a riqa warware irin wadannan shubuhohi don a sanar da mutane haqiqanin gaskiyar magana, don gudun kada su riqi qarya suzo suna fada da gaskiya. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.


        (08137925034)


8th April, 2021/ 26th Sha'aban, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post