-Malam idan Zaka aikata aiki da Nufin Neman Yardar Allah ta'ala, to kar ka damu da Haushin Makiya da Mahassada Saboda ladan ka Yana Wurin Allah, daman basu Kake Yiwa aikin ba.



-Idan Kana aiki da iklasi Wallahi hatta Shaidan zai Yanke tsammani daga gareka, Saboda haka Malam duk aikin da za ka yi ka rinka gina shi a kan asasin Iklasi, to hatta Shaidan zai zamo bai da iko gareka, kamar Yadda Yazo a cikin Alkur'ani Mai girma fadin Shaidan "Zan halakar da su baki daya face bayinka Masu Iklasi".


-Idan Kana Yin aikin don Allah to babu Shakka zaka Samu tsira gobe Kiyama, Komin Karantar ayyukanka, Kamar Yadda Yazo a Hadisi an tambayi Manzon Allah (S) Menene tsira gobe Kiyama?


-Sai Manzon Allah (S) Yace, tsira Shine kada Mutum Ya Yaudari Allah Sai aka ce ta Yaya Mutum zai Yaudari Allah?


-Sai Manzon Allah (S) Yace: "Shine Mutum Ya aikata abin da Allah ya yi Umarni, amma Kuma Ya Kasance Manufarsa Neman Yardar Mutane ne Ko Wani abin Duniya.


-Malam idan Kayi Nazari akan Wannan Hadisi zaka ga Cewa Yin Aiki badan Allah ba Nau'in Yaudarar Allah ta'ala ne.


-'Yan uwa Mu tsaya Kyam akan tafarkin Jagoranmu Sayyid Zakzaky (H), Kar Mu damu da Masu Yin Kushe da Hassada.


-Ya Allah ka tsarkake Mana Niyyar mu. Bihaqqi Sayyid (H).


-Muhammad Jiddah Nguru.

1 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post