Ladubba ga mai Azumi...!



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


GA MATAR DA JININ YA 'DAUKE MATA DA RANA KO MATAFIYIN DA YA DAWO GIDA DA RANA


Yana daga cikin abubuwan da ke haramta yin azumi yin tafiya kafin zawwali da kuma zuwan jini na biqi ko haidha ga mace.


Sai dai kuma akwai yanayi dake kasancewa ga jinsin wadannan mutane biyu, wato jini ya daukewa mace da rana ko kuma matafiyi ya dawo gida da rana. To, duk wadannan yana halatta su cigaba da shan ruwansu a daidai wannan lokaci, sai dai ladabi ne a kame baki cikin sauran lokacin da ya rage kafin shigowar dare. 


An samo riwayoyi daga A'imma (A. S) kamar haka; 


👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇


نَوَادِرُ الرَّاوَنْدِيِّ، بِإِسْنَادِهِ عَنْ مُوسَى بْنِ جَعْفَرٍ عَنْ آبَائِهِ ع قَالَ قَالَ عَلِيٌّ ع‏ إِذَا قَدِمَ مُسَافِرٌ مُفْطِراً بَلَدَهُ نَهَاراً يَكُفُّ عَنِ الطَّعَامِ أَحَبُّ إِلَيَّ وَ كَذَلِكَ قَالَ فِي الْحَائِضِ إِذَا طَهُرَتْ نَهَارا


Ya zo cikin Nawadirun-Rawandi da isnadinsa zuwa kan Musa Bn Ja'afar, daga iyayensa (A. S) yace; Aliyu (A. S) yace; 


" IDAN MATAFIYI YA ISO GARINSA DA RANA YANA MAI BODE BAKI, TO, YA KAME DAGA CIN ABINCI SHI YAFI SOYUWA GARE MU. HAKA MA YAKE GA MAI HAIDHA IDAN TAYI TSARKI DA RANA. "


Wannan na nuna mana alfarman watan ne, amma ba laifi bane su cigaba da ci da sha cikin abinda ya rage na wannan yini. 



Sai kuma wani ladabi da ake son kiyayewa saboda kada yayi sanadin bacin azumin mutum. 


👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇


 علل الشرائع ابْنُ الْوَلِيدِ عَنْ مُحَمَّدٍ الْعَطَّارِ عَنِ الْأَشْعَرِيِّ عَنِ السَّيَّارِيِّ عَنْ مُحَمَّدِ بْنِ عَلِيٍّ الْهَمْدَانِيِّ عَنْ حَنَانِ بْنِ سَدِيرٍ قَالَ: سَأَلْتُ أَبَا عَبْدِ اللَّهِ ع عَنِ الصَّائِمِ يَسْتَنْقِعُ فِي الْمَاءِ قَالَ لَا بَأْسَ وَ لَكِنْ لَا يَنْغَمِسُ وَ الْمَرْأَةُ لَا تَسْتَنْقِعُ فِي الْمَاءِ فَإِنَّهَا تَحْمِلُ الْمَاءَ بِقُبُلِهَا[10].


علل الشرائع ج 2 ص 73.


Yazo cikin Ilalus-Shara'i'i, daga Ibn Walid, daga Muhammad Addariy, daga Ash-Ariyi, daga Sayyariyyi, daga Muhammad Bn Aliyu Al-Hamdaaniy, daga Hanaan Bn Sadeeri yace; " Na tambayi Abu Abdullahi (A. S) game da mai azumi zai iya shiga ruwa? " Yace; 


" BABU LAIFI, SAI DAI BA ZAI NUTSE (cikinsa) BA. KUMA MACE BA ZA TA NUTSE CIKIN RUWA BA, DOMIN ITA TANA 'DAUKAR RUWA TA GABANTA. "


Wato nutsewar mutum cikin ruwa yana bata azumi, saboda haka sai a kiyaye. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.


       (08137925034)


     18TH APRIL, 2021

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post