Munyi nufin zamuyi Muzahara na farko a 1980 a cikin watan Mayu to, amma sai wani abu yafaru a watan Afrilun wannan shekarar, wanda yasama muka fito ( Muzaharar) tun kafin watan mayun, shine rugujewar shirin Amuruka na kai hari #Iran, wanda suka ce da nufin ƙwato ma'aikatan ofishin jakadancinsu da aka yi garkuwa dasu, da kuma kai ma ita Iran ɗin hari wanda shirin yaruguje a wajan Dabas Lud- Salt (?).
To, wannan loƙacin sai muka fito da nufin murna. Shi ne muzahararmu ta farko kenan a April 1980, da nunin cewa Amurka taji kunya, harinta na farko data kai ga shi kuma tayi asara wannan muna iya cewa shi ne muzaharar ta farko.
Sai muzahararmu ta biyu a may 1980, wanda muka saka masa MUSULUNCI KAWAI (wato ISLAM ONLY ), da kuma bayanin me wannan yake nufi cewa addini kawai za a koma ma tsantsa, To kuma daga nan ALHAMDULILLAHI, daidai gwargwado muka shiga karatuttuka wanda muka sani, har ma a loƙacin suna mamaki, don ana yayin tafsirin ( Alƙur' ani ) ne a watan Ramadan, sai suka gani ma ina iya tafsirin Alkur'anin.
Har suna ganin kamar yaya? Don suna ta mamakin ya akayi wanda yayi jami'a ya karanta Economics' kuma yana iya fassara Alkur'ani? Suba su san cewa dama ina da 'kal fiyya' (wato Background) irin na karatun gida ba, wanda yake ya wace karatun jami'a ɗin.
Sheikh zakzaky (H)
Faruq sani Kudan