Ko ka san ma'anar Azumi kuwa?



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


QALU-BALE GA MASU NADAWA KANSU RAWANIN MALANTAKA


Abinda mafi yawan mutane suka sani game da azumi shine suyi Sahur kafin ketowar alfijr da kuma shan ruwa bayan faduwar rana. Iya abinda suka sani shine subar ci da sha daga hudowar alfijri har zuwa faduwar rana sai kuma su cigaba da ci da sha.


Na'am, wannan na daga cikin alama na cewa mutum na azumi, amma ba shine ma'anar azumin ba. Idan mutum ya dogara da wannan siffa kadai zai iya zama mai hasara a qarshe azumin nasa, domin bai sami ladar wani abu cikinsa ba. 


An kawo haqiqanin ma'anar azumi cikin riwaya kamar haka ;


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


 عَنِ الْحُسَيْنِ بْنِ عُبَيْدِ اللَّهِ عَنْ أَحْمَدَ بْنِ مُحَمَّدِ بْنِ يَحْيَى عَنْ أَبِيهِ عَنْ أَحْمَدَ بْنِ مُحَمَّدِ بْنِ عِيسَى عَنْ عَلِيِّ بْنِ مَهْزِيَارَ عَنِ الْحَسَنِ بْنِ سَعِيدٍ عَنِ النَّضْرِ بْنِ سُوَيْدٍ عَنِ الْقَاسِمِ بْنِ سُلَيْمَانَ عَنْ جَرَّاحٍ الْمَدَائِنِيِّ عَنْ أَبِي عَبْدِ اللَّهِ ع قَالَ: إِنَّ الصِّيَامَ لَيْسَ مِنَ الطَّعَامِ وَ الشَّرَابِ وَحْدَهُ ثُمَّ قَالَ قَالَتْ مَرْيَمُ‏ إِنِّي نَذَرْتُ لِلرَّحْمنِ صَوْماً أَيْ صَمْتاً فَإِذَا صُمْتُمْ فَاحْفَظُوا أَلْسِنَتَكُمْ وَ غُضُّوا أَبْصَارَكُمْ وَ لَا تَنَازَعُوا وَ لَا تَحْسُدُوا قَالَ وَ سَمِعَ رَسُولُ اللَّهِ ص امْرَأَةً تُسَابُّ جَارِيَةً لَهَا وَ هِيَ صَائِمَةٌ فَدَعَا بِطَعَامٍ وَ قَالَ لَهَا كُلِي قَالَتْ إِنِّي صَائِمَةٌ فَقَالَ كَيْفَ تَكُونِينَ صَائِمَةً وَ قَدْ سَبَبْتِ جَارِيَتَكِ إِنَّ الصَّوْمَ لَيْسَ مِنَ الطَّعَامِ وَ الشَّرَابِ‏.


بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج‏93، ص: 295


Daga Hussaini Bn Ubaidullah, daga Ahmad Bn Muhammad Bn Yahya, daga babansa, daga Ahmad Bn Muhammad Bn Isah, daga Aliyu, daga Aliyu Bn Mahziyaan, daga Hassan Bn Sa'eed, daga Nadhri Bn Suwaid, daga Qasim Bn Sulaiman, daga Jarrahi Al-Mada'iniy, daga Abu Abdullahi (A. S) yace; 


" LALLE AZUMI BA SHINE (barin) ABINCI DA ABIN SHA KADAI BA ."


Sa'an nan yace, Maryam tace; 


" LALLE NI NAYI BAKANCEN AZUMI GA MAI RAHMA (abin nufi shine shiru). "


" SABODA HAKA IDAN KUNA AZUMI KU TSARE HARSUNANKU (daga fadin munanan maganganu na qarya, qazafi, sharri, cin naman mutane d.s), KUMA KU RINTSE IDANUWANKU (daga kallon abubuwan da kallonsu suka zama haram), KUMA KADA KUYI JAYAYYA (na rashin dalili tsakaninku), KUMA KADA KUYI HASSADA (ga 'yan'uwanku cikin abinda Allah ya basu na daga dukiya, ilimi ko lafiya) ."


Yace; Manzon Allah (A. A. W. W) ya ji wata mata tana zagin baiwarta (her slave) alhali tana azumi. Sai yayi umarni aka zo masa da abinci, sai yace mata; 


          " KI CI !" 


Sai tace; " Ai ni ina yin azumi ." Sai yace; 


" TA YAYA ZA KI KASANCE MAI AZUMI ALHALI KIN ZAGI BAIWARKI ? AI SHI AZUMI BA (shine) BARIN (cin) ABINCI DA ABIN SHA BANE ."


Amma abin mamaki shine, maimakon ka ji malamai na karantar da mutane da yi musu hani kan irin wadannnan abubuwa sai ma kaji sune masu aikawa da sunan Tafsiri. Laile masu aikata irin wadannan abubuwa za su wayi gari basu da ladar komai cikin azumin nasu. 


Manzon Allah (S. A. W. W) ya sanar mana da haka cikin wani hadisi nasa.


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


 قَالَ رَسُولُ اللَّهِ ص‏ رُبَّ قَائِمٍ حَظُّهُ مِنْ قِيَامِهِ السَّهَرُ وَ رُبَّ صَائِمٍ حَظُّهُ مِنْ صِيَامِهِ الْعَطَشُ.


Manzon Allah (S. A. W. W) yace; 


" DA YAWA MAI TSAYUWA (sallolinsa cikin watan Ramadan) RABONSA CIKIN TSAYUWAR TASA SHINE GAJIYA. KUMA DA YAWA MAI AZUMI RABONSA CIKIN AZUMIN SHINE YUNWA. "


Dalilin hakan kuwa shine don ba ya kiyaye wadannan abubuwa da aka ambato cikin hadisi na sama. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼Ado Isah Guda. 


      (08137925034)


12th April, 2021/ 30th Sha'aban, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post