Kyakkyawa ce,!!
Ta iya Kalolin Stile na Photo !!!
Tana da kyau, Aji, Sutura da Waye wa !!!
Tirr da Irin Wannan Shigar Da Hotunan da Matasan Sistocin mu keyi Da Sunan Wayewa Kuma Su Dora a Social Media,
A Wuri na, Bakauya ce ke, Doluwa ce ke, Sannan Marar Sanin Darajar kanta da Addinin ta da Tarbiyyar da Mahaifanta Suka Bata !!!
Ba burgeni Zakiyi ba Shima ba Burgeshi zakiyi ba Domin Dukkan mu Munsan Iya Makurar Wayewa Addini Yazo Mana da Ita, Kuma Sayyid (h) ya Zo Mana Da Wayewar da Wasu ke kwaikwaya Daga Wajen mu Amma Ba Irin Wannan ba...
Kiyi Hakuri Sister Dole infada ko kina Karantawa kina Zagina, Hakkine Akan Al'kalamina Domin Abun Tambaya ne a Wuri na !!!
Indai kinason Darajarki to Zamo Cikin Masu Tarbiyyantar da Wasu Domin ke uwace ta Wasu Kuma Matar Wani !!
Hijabi sirri ne daga cikin sirrukan mata da ya zama kamala mai darjanta mace da ba ta kimarta a cikin al'umma. Hijabi yana nuna darajar mace da kimarta a cikin al'umma kuma a sakamakon haka ne zamu ga mata masu daraja tun daga Maryam, Asia, da Hadija, da Fatima (a.s) duk sun zama wani alami na lullubi a cikin al'ummun da suka biyo bayansu. Darajar mace ce ta sanya Allah madaukaki ya girmama ta da lullubi domin a fahimci kimarata a cikin al'ummu ita ma ta fahimci darajarta da kimarta.
A Musulunci, fitar da tsiraici (tabarruji) haramun ne. Tabarruji yana nufin nuna kan mata a gaban mazaje, don janyo hankulansu da kuma yada fitina. Hakan, wani nau'i ne na fitina kuma yana da matsaloli masu yawa. Matsalarsa ba wai kawai shi ne cewa wannan budurwar matashiya ko kuma wannan saurayi matashi zai fada cikin zunubi ne kawai ba - wannan ababe ne na farko-farko; mai yiyuwa ne ma muna iya cewa shi ne mafi karancinsa – amma sakamakon hakan ya kan koma ne ga iyali. Alal hakika irin wadannan alakoki wadanda babu wani kaidi da sharadi cikinsu lamari ne mai halakarwa cikin iyali...
Ki zama Mai Sanin Mai kikeyi, Wayewarki ta Zama Ta Addini Kuma Ta Kasance Irin ta Harka Domin ki Zamo Macce Mai Daraja Abar Alfahari ga Addinin ta.
Barka dayin Sahur !!!!
Mas'udu Dan Masani Shinkafi 08149993999