... Umar Hassan Gololo...
Malam Zakzaky(H) abinda kullum yake cewa shine duk abinda zaka yi kayi shi domin neman yardar Allahu Ta'ala, saboda ranar Lahira kai kadai Allahu Ta'ala zai maka hisabi ba tafinta a tsakani.
Malam Zakzaky(H) yace muna Wannan gwagwarmayar ne domin neman uzuri a wurin Allahu Ta'ala ne, don haka kowa yayi iya iyawarsa, ayi ta tsere ne domin neman yardar Allahu Ta'ala.
Kada ka yarda ka daukarwa kanka cewa akwai wasu abubuwa a harkar nan wadanda idan babu kai ba zasu yiwu ba, da zarar ka yi haka sai ka ga Allahu Ta'ala ya kawo Wanda zai fika iyawa da kuma bada gudummawa.
Kada ka rinka gadara da jiji da kai kana hura hanci da alfaharin ba zaka iya zamewa ba, Jagora ne kadai muke da yakinin ba zai kauce hanya ba, sai kuma shahidanmu da suka yi wafati a wannan tafarkin ba tare da sun sauya ko sun juya baya ba.
Malam Zakzaky(H) yace idan muka ki yin addini sai Allahu Ta'ala ya kawo wadansu wadanda muke wa ganin kaskantattu ne su yi addinin mu kuma mu zama 'yan kallo.
Kai wane guarantee aka baka har kake kokarin korar wasu daga harkar.?
Muna rokon Allahu Ta'ala ya tabbatar da dugaduganmu a tafarkin gwagwarmayar Musulunci karkashin jagorancin Malam Zakzaky(H), Ya bamu sabati da istikama alfarmar Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi wa Alihi wa Sallam....