Ka dage ka kuɓutar da kanka daga wuta koda da tsagin Dabino ne ko kuɓim Ruwa. !


 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


KHUDUBAR ANNABI (S. A. W. W) KAN FALALAR CIYARWA A WATAN RAMADANA


Al'amarin ciyarwa abu ne mai girman gaske cikin addinin muslimci, ko da kuwa a al'ada ne za muga yana da kyau kuma yakan daukaka matsayin mai aikatawa ballantana cikin muslimci.


Allah (T) yayi umarni da aikata hakan a gurare da dama cikin al-qur'ani kuma ya kwadaitar game da girman darajar da ake samu a duk lokacin da akayi. Musamman ma cikin wannan wata mai alfarma akan nunnunka ladan dukkan wani aiki na alkhairi.


Yazo cikin UYUNUL-AKBAR daga Imamu Ridha (A. S) cewa; 


👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇


الْعُيُونُ، بِإِسْنَادٍ سَيَأْتِي عَنِ الرِّضَا ع قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ ص فِي خُطْبَتِهِ فِي فَضْلِ شَهْرِ رَمَضَانَ أَيُّهَا النَّاسُ مَنْ فَطَّرَ مِنْكُمْ صَائِماً مُؤْمِناً فِي هَذَا الشَّهْرِ كَانَ لَهُ بِذَلِكَ عِنْدَ اللَّهِ عِتْقُ رَقَبَةٍ وَ مَغْفِرَةٌ لِمَا مَضَى مِنْ ذُنُوبِهِ قِيلَ يَا رَسُولَ اللَّهِ ص وَ لَيْسَ كُلُّنَا يَقْدِرُ عَلَى ذَلِكَ فَقَالَ ص اتَّقُوا النَّارَ وَ لَوْ بِشِقِّ تَمْرَةٍ اتَّقُوا النَّارَ وَ لَوْ بِشَرْبَةٍ مِنْ مَاءٍ[9].



عيون الأخبار ج 1 ص 296، أمالي الصدوق 58.


Manzon Allah (S. A. W. W) ya fada cikin Khudubarsa cikin falalar watan Ramadana; 


" YAA KU MUTANE ! DUK WANI DAGA CIKINKU WANDA YA CIYAR DA MUMINI MAI AZUMI CIKIN WANNAN WATA, TARE DASHI GAME DA HAKAN AKWAI LADA WAJEN ALLAH GWARGWADON WANDA YA 'YANTA BAIWA (slave) DA KUMA GAFARAR ABINDA YA SHUDE NA DAGA ZUNUBANSA. "


Aka ce, yaa Ma'aikin Allah (S. A. W. W), ai ba kowannenmu ne ke da ikon haka ba ba. Sai yace; 


" KU TSERATAR DA KAWUKANKU DAGA WUTA KO DA DA TSAGIN DABINO NE. KU TSERATAR DA KAWUKANKU DAGA WUTA KO DA DA KURBI NE NA RUWA ."


To, gaskiyar magana za mu iya cewa babu wanda zai rasa abinda zai ciyar da wani ko shayar dashi cikin wannan wata don neman lada, sai dai kawai idan bai ga dama ba. 


Dalili kuwa shine, zai yi wuya ace cikin tsahon watan nan mutum ya kasa samun wanda zai ba shi Dabino ko ruwa don yayi bude baki. To, cikin wannan abinda za a ba shi ne zai dauka ko ya raba ya bawa wani don shi ma ya sami irin ladan da wadanda suke ba shi suke samu. 


YAA ALLAH KA TAIMAKE MU KA BAMU IKON CIYARWA KO TA HANYAR SHAYAR DA RUWA NE GA MUMINI MAI AZUMI. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.


       (08137925034)


     21ST APRIL, 2021

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post